← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 306

Sashe 107

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ZARIA
Suna zaune gaba dayansu falon iya ga abin karyawa a aje amma sun kasa karyawa sai Salimace data fito ta zauna ta dauki kofi tana tsiyaya ruwan zafi a ciki.
Iya ta nisa tana fadin tsiyaya min ruwan zafin nan yar nan kada hanjina ya nade ga banza banga abin tsayawa tashin hankali wajen nan ba.
Don yarinyar na tafi gidansu kan mijinta ya kara aure za a zauna a daga hankali haka ?
Ita da aka aurota ba hakkuri taga yar uwarta tayi ba wani irin iya shegene basuyi ba a gidan nan da aka kawota saida aka koma ba yan uwan uwargida hakkuri.
Ke dubu lamarinki yana daure min kai wallahi ni banga abin daga hankali ba wajen nan
Yaron nan aure ya kara ba wani mugun abu ya aikata a rayuwansa ba amma kin daga hankalinki haka ba tunane ?
Iya ba haka bane ban damu da aurensa ba don shi yaga yana iyawa ni damuwata shine ya bada dukiyan yan uwasa dake hannusa .
Ba zan zuba ido ina kallo yana facaka da dukiyan yan uwasa a saka mai ido
Iya yaran nan sun san da dukiyan su yana hannun Jafar yau ace kuma Jafar baida aiki sai aure aure yana facali da dukiyan yan uwansa na kallo ?
Haba mama haba yaya jafar ba zaiyi hakan da kike tunane ba wallahi in ma wani ya zugaki wallahi ya dauki alhakin shi don,,,,
Ke kinci gidan ku zan saba maki rai yanzun nan kul kika kara tareni idan ina maganan nan me kika sani ke da shirmen banza ?
Salima ta hada shayinta ta fita daga falon zuwa waje bayan ta mikawa iya nata part din ya Habu ta nufa ta samu ya fita tunda safe sai Maria data samu zaune ga Abba yana wasa a gefe ita kuma tayi tagumi idonta yayi ja jajir alaman taci kuka har ya isheta a lokacin.
Haba dai Madam ba dai kuka kikayi haka akan wanan zance ba kada ki zama wata mara godiyan Allah mana naga hakan farin cikinkine gaki ga yar uwarki a gida daya.
Yau dai kinsan ko waye yaya Jafar kinsan kuma tunda ya zabi hakan ya shiryawa duk wani barazanan da za a tunkareshi dashi gidan nan.
Takai zaune da kofin shayinta a hannu tana fadin ni ina mamaki da kuka kasa gane waye yaya J ?
Ai ki zuba ido kawai kiyi kallo ina fada maki duk abinda sukayi a baya suna ganin sun gama dashi a yanzu zasu girbi abinsu bawan Allah nan ya dade da bakin cikin wa,yan nan matan nashi a zuciyar shi amma an kasa gane hakan.
Mezaisa kike fahintar yau da sune ya habu yaga yan uwansu yace yana so da gudu zasu bashi ya aura don kiyayyan da suke maki suna bakin cikin kasan ,cewarki matar yaya Habu.
Nasani amma nidai a wajena hakan ba daidai bane Salima don ko rantsuwa nayi ban kaffara nice za ace na hada wanan abin.
Ai ashe kinsan da hakan to me zaisa ki damu da abinda zasu fada a kanki damuwa ba naki bane don inkin nuna hakan za a samu sa,an gaya maki maganan banza.
Amma idan anga kin dake ko za a fada ba yadda za a sake a fada maki cikin takaici ba don haka gara tun wuri ki marawa yar uwarki baya Maria.
Sun dauki lokaci suna magana a tsakaninsu kafin ta mike zuwa part dinsu ta samu kawu ya shigo yana fadin abinda yafi dai yanzu ya fito da dukiyan a kasa abawa kowa nasa kaso ai yanzu kowa acikinsu yanaa iya rike nasa.
Kaiyya yaya nifa ban tunanen akwai wanan dukiyan a yanzu illa kawai ya kawo abinda ya saura a hannusa a kiyasta a bawa kowa hakama wanan gidan.
Kaga idan anyi haka zanga inda zai saka yarinyar nan in tunanesa wanan part na yazid to tun yanzu ya canza dabara nayi waya da Baraka ta taso tazo asan abinda za ayi dama mijinta ya matsa ta karbo dansu ya fara juyawa tunda ya gama karatu ba aikin yi.
Hakan yana da kyau kwarai saidai nasan koshi nasa tunanen ke nan a yanzu wanan wajen na dan uwansa zai saka yarinyar tunda ba wani ginan yayi da zai sakata ba can na daban.
Allah sarki idan kin hanashi saka mata a wajen dan uwansa haya kikeso ya fita ya kamawa matan nasa Dubu ?
Duk yadda zaiyi shiya sani mama ai yasan baida matsuguni ya daukowa kanshi zancen aure kina gani iya ko wanan filin daya kara yayi ginan wanan daya dauko kaduna ai cikin filin gidan ya diba ya kara yayi.
Iya sai a kyashi ya mamaye duk kason yan uwansa shi daya nan gaba su koma suna zargina nice na mara masa baya da yayi masu hakan ?
Yanzu dai maganan gaskiya ke iya a bari ya kawo dukiyan a raba abawa kowa nasa idan yaso in zai dauki hanyan wajen shi yazid kafin ya dawo sai ya dauka a dinga ba uwarsa kudin ina ganin haka zaifi sauki tunda abin magadane .
Anya Dauda kuyi tunane kafin ku yanke wanan shawaran yaron nan shine tsaye da gidan nan da yan uwansa yau don abin duniya zaku rufe ido kuyi mashi hakan ?
Iya ai ba tozarci bane nauyine za a sauke mashi kada daga baya abin yazo yafi haka rayuka su baci tsakanin gara tun wuri ayi maganin abin zaifi.
Kit Salima da tayi recording din muryoyinsu ta mike zuwa daki bayan ta kashe wayan bata jira komai ba ta bude ta turawa yayanta komai.
Sun kai wani lokaci a falon suna tatauna zancen kafin suyi sallama da juna ranan mama bata nemi yar uwata ba saboda har ita wanan lamarin ya shafa.
Sai take ganin laifin duk natane da badon ita ba babu inda Jafar zai ganni ai zancen kawune da yace da ita mudin fulani abin tsorone.
Zamu mallake mata yaya ta koma bata gane komai ba har gara wa yan nan matan na J ai damu bata ganin habu komai da yake ciki ba a taba sani saboda boyon kurwa da yakewa mutune.
Wanan zance mama ta haushi ta zauna sosai donshi ta kara hawa zancen cewa a raba gado a warewa kowa nasa kaso a yanzu don ta kula Jafar ya salwantar da dukiyan nasu.
Bai tashi ganin sakon salima ba sai da dare bayan ya gama abinda yakeyi ya bude data yaga sakon mutane lokacin ya kula da sakon kanwar tashi.
Ya bude yaga sakon muryane kusan guda hudu daya bayan daya yake bin sakon yana saurare a ranan kasa barci yayi don zullumi da tunane.
Habu ya fara nema akan zancen ya nuna mashi yasan da zancen shima an fara a gabanshi amma ya nuna rashin dacewan hakan sai aka baryi dashi.
Haba dai Habu shine ka kasa fada min komai a cikin lokaci tun tuni idan nasani da ban fitar da kudin nan an raba a bawa kowa nasa ba ?
Yake tambayansa waya turo mashi wanan murmushi yayi shi habun yace salimace don ra,ayin mu daya da ita tun a waje ta fada masu gaskiya abar nata a wajeka kome zakayi dasu kayi.
Sun dan jima suna zancen tun bayan kashe wayansa ya kira nura da yunusa abokansa da suke kasuwance a asirce ya bukaci da su hada mashi kan kudin a waje daya.
Ya kuma kara umartan Nura da ya mayar da hankali wajen ginan daya saka suna gama waya ya kira wani ya bashi cigiyan gida.
Allah sarki da ace mama tasan abinda ta haifa da bata yarda har kawu yayi amfani da damanta ya bata wanan shawaran ba duk da bai kyautata zaton shawaran kawune shi kadai dole akwai wasu yan uwa dake kwadayin dukiyansu a hannunsu.
A lokacin kuma ya kara yarda da maganan hardo kalai kawu ya dade yana bin duduniyarsu ba tare da sanin hakan garesu ba duk da alama Habu yasan wani abu shikan dip yake banda kasuwanci baisa komai a gabanshi ba.
Bayan kwana biyu ya bar kasan zuwa South Africa da niyar sati daya amma saida ya share sati ukku a can wanan yasa mama dake ta neman layinsa dare da rana ta kasa samun shi .
Ta kira Habu shike fada masu baya kasan nan Saaratu ke fadin kin gani ko mama da kudin yake ta facaka ya dauki yarinyar nan sun fita ke nan yawon amarci ya barmu nan ko Lagos bamu taba zuwa ba.
Shi kuma kawu cewa yayi dubu na fada maki yaron nan yana dawowa a kwace komai na hannusa a rabawa yan uwa ko gida in bai tsira da komai ba dole ya sayarwa yan uwa da part dinshi a basu hakkin su.
Mama da bata data cewa sai kara hasala da zancen ke sakata a kan danta takeyi haka yasa ido rufe ranan data zo gidan ta shiga part din habu .
Yanda na kwance sai ganinta tayi ta mike tana gaida ita cikin rashin walwala take fadin yar uwarki tana inane Maria ?
Ta dan sasauta murya tana fadin tana Abuja mama tace kira min ita yanzun nan a waya hakan yasa yanda daga wayan takira layina na dauka na fara mata yarenmu na fullanci tace bani ita nan ta mika mata wayan.
Naji muryanta a lokacin yasa tana karban wayan tace hello Rahama ina jafar yake ne ?
Na maimaita sunan a cikin mamaki ina fadin mama bansan inda yake ba don rabona dashi tun dana barshi gida nazo abuja ban kara ganinsa ba sai naji ta kashe wayan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Chapter 107 · 0% Book details