Sashe 85
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zan iya cewa a yanzu har da wasu aiyuka na daina shiga taya mama a part dinsu sai dai lokacin shan magani bayan maganin na rage yawansa nace kuma ya kare a karshe don haka na daina wanan sintirin na kama kaina. Idan na fita tun safe ban dawowa gidan sai ana gab da magariba zan shigo inyi sallah in kwanta sai kuma da safe idan zan fita zan lekasu inmasu ya maijiki wata ranama don sammakon dana tsiri yi nakan samu yana wanka a lokacin bai fito ba na gaida mama in juya abina infita. Itama Nafisa ta tafi bukin dangin mamanta a kauyen nan zaria din wani gari da ake kira da fanbeguwa mahaifiyarsu yar can garin ne sun kuma kwasa sunje buki. Sai ya koma daga mama sai yan mantata suke faman dawainiya dashi don sune dama doleshi ai mu karan taimako mukayi masu amma Saare bata gane hakan ba. Duk da ya danji dama yana iya wasu abin da kansa don bawan Allah nan Allah ya bashi karfin halin ciwo da dauriya a kwancen dayaji dama a haka yake gudanar da bussiness dinsa abinka da rai da guri. Amma sai hakan ya zama gajiyarwa ga kannen nasa dukkansu kowa na korafi a gefe da basu samun hutu ko kadan daga ayi wanan sai gyaro wancan mama ke sakasu. Anty salimace tashigo part din yar uwata a gajiye tana zama take fadin wayoni maria bayana zai tsage ? Anty maria take fadin garin ya ke kuma ta dan kai kwance tana fadin ke matar yaya kinsan irin wahalan da mukeyi kuwa mama bata bari mu huta sam wallahi dakin dan zauna yanzune zakiji tace tashi kiyi wanan ko dauko abu kaza ki gyara. Duk wanan mai bakar aniyarce Saare taja muna haka wallahi ni nasan Ramaah da Nafisa fushi sukayi din abinda saare din ke masu. Ai wani abu tayi masune maria ta tambaya tace bata fada maki ba ko dadina da Ramaah ke nan ai bata faye irin surutun nan ba ita. Maria ta sake fadan wani abin ya farune tsakaninsu tace ai kinsan halinta da sakin magana Nafisa kuma ta nuna mata ko ita waye. Nasan hakan da Ramaah ta gani yasa dauki zancen ta daina shiga itama tana aikin ladanta gabadaya ko dazun nan wallahi saida yaya yayi min zancen sun daina shigowa kome ya faru ? Sam bata fada min komai ba wallahi kinsan halinta da zurfin ciki ai haka kuke fulani sai dai in kun tashi fada baku duban bakin gatari kuke sarawa. Au sheri zaki min ke nan kuma yanzu ai naga kema da baki iya hakan ba da yanzu kin bar gidan nan akan sherin matan gidan nan. Nice na fado falon da sallamana ina ganin ta nayi murmushi na karasa shigowa ina gaidasu da gida suka amsa min take fadin. Cigiyar ki nazo yi Ramaah yaya yace kun dauke kafan da part dinsa bai san dalilin hakan ba a yadda na kula kuwa hakan ya dan dameshi. Ni kuma aiko dazun da zan fita nashiga mana da safe yanzun nan kuma dawowana ke nan ai ban zama yanzu zamu soma exam yasa hankalina ya dauko. Kyaleshi kinji kinsan halin yaya J ai da damuwa da wanda ya damu dashi yanzu dan kulashon da kukeyine yaga kun daina shine yake wanan magana shi haka yake da damuwa da mutane shiyasa ake saurin kamashi. Dan kallonta nayi na kau da kaina gefe ina wasa da Abbati daya zo ya fada jikina ban jima ba na mike da yaron zuwa ciki. Nasan dai ta fita tunda naga anty Maria ta shigo dakin gab da magariba take tambayana meya hadani da Saare na dago ina fadin Saare kuma ? Yaushe ba abinda ya hadani da ita take fadin in daiyi sannu ita ba don mama da ya habu ba ba zata yarda ina sintiri a part din yaya J ba. Tunda tasan halin matanshi ba mutuncine dasu ba hakama Saare din na dai share zancen zuwa don ban bata amsa ba. Saidai a kasan zuciyana ina tunanen me akace ya hadani da itane wai tunda bakina da nata dai bai hadu ba duk bare baren da takeyi a kaina din. Tunda bata nuna dani takeyi ba akan me zan tsaya nuna mata nasani balle yanzu dana kama kaina da shiga part din da sunan jinya. Shima kuma addua muke mashi Allah ya bashi lafiya ya mike don ba mai fatan ya tabbata a hakan da yake din. Na share hakan kwana biyu kuma ranan weekend na gama wanki nayi wanka sai gata again wai yaya J yana kirana. Saida na shirya naje suna falo zaune na shigo nake gaidasu da kwana suka amsa min yake fadin Rahama lafiya kwana biyu na daina ganin ki ? Ita Nafisa ance tayi tafiya amma ta dawo jiya sai a lokacin ma nake jin cewa su Nafisa din sun dawo daga tafiyan. Nake fadin ba komai yaya exam zamu soma yasa ban zama yanzu exam zai hanaki shigowa ki duba yayan ki Rahama ? Sai nayi kasa da kaina bance komai ba don mama data kura muna ido tana sauraren mu itace ta kawar da zancen tana fadin yace kiyi mai irin ferfesun da kikayi ranan ya tsaya kuma tareki da tambaya. Wayyo Allah da mama ta sani ko shi yaya din da basu sakani wanan aikin Allah bai hada jinina da kifi ba duk bafulatanin asali haka yake inba mu fulanin zamani ba . Sam bafulatani bai cin kifi ace zaki dauki spoon ki motsa miyar kifi ki kuma dauka ki motsa miyar naman dashi ko one spoon kikai a bakinki a ranan idan kin soma amai kamar zaki amaye duk hanjin cikiki. Amma don kawaici da alkunya haka na mike zuwa kitchen din nasu na soma aikin hada ferfesu din ina gamawa na bude fridge an kawo kifi mai yawa da gani sabon zubawa ne ballo na wanke na hada. Ban fito ba saida na kammala komai na zuba na nufo falon dashi na samu mama bata nan ta fita saishi da wani abokinshi a falon suna hira. Sallama nayi na aje tare da gaida abokin nasa ruwa naje dauko mashi naji bakon na fadin kai mutumina wai dama kayi sabon aurene ban sani ba ? No wander naga alots of changes a tare dakai da kuma yanayi yaushe ka auri wanan african queen din banda labari ? Yanzu daka sani ai bai baci ba gashi kun gaisa amma gaskiya ba ganin fuska ba wanan karo kan ka tsaya ka zabo abinda ya dace dakai. Allah ko ya fada hangoni dayayi tafe ruwa na dauko masu da drinks na aje gaban bakon daketa faman sabarin baki ga abokin nasa. Godiyana ga Allah banyi kwaron hannu na dafa kadan ba tunda nasan mama da yaranta na wajen sai kuma Allah ya turo wanan bakon nasa yazo. Furcina yasa bakon dan kallon mu da nake fadin nagama yaya shike nan ko akwai wani abin naji yace jeki Rahama zan nemeki idan mun gama. Zo amarya mana kada ki tafi ban sayi baki ba bayan abincin da kika karrama ni dashi haka tun ban ciba kamshi ya danne hancina kudi ya dibo daga aljihunshi ya miko min na dan dubi yaya din yai min alaman dana karba. Naji bakon na fadin kai akwai irin matan nan har yanzu ashe gaskiya J ka dace kwarai wallahi kudin ma sai ta tambayi izzinin ka zata karba ? Gaskiya kayi dace Allah yasa abin yacigaba a haka ni abokinsane sosai tare muka taso dashi saidai bani zama a nan yanzu shine ya rabamu har baki sanni ba na mika hannu kawai ina fadin wawa sai zuba yake haka na tsani namiji irin haka wallahi. Na fito na hango Saare tsaye kofansu tana waya ban sake kallonta ba na shige part din mu da kusan a jere suke a barin dama dana yaya J din sai dai akwai dan tazara sosai a tsakanin su. Inda part din su mama ke barin hagu yana kallon nasu yaya din da wanan dayan part din da ake cewa part din yaya yazid ne shi ko yaushe yana rufe saidai da yarsu tazo daga zamfara kwanaki aka bude mata ta sauka ciki da yaranta. Sai tsakiya dake da fili tsakanin gidajen duk girman wanan filin da haka nake tashi in shareshi tas amma yanzu na ba kaina lafiya ko ita wace akace yar aikin bata iya sharan wajen yanzu sai almajiraine ke zuwa kwana bibiyu suna sharan wajen. A basu abinci da kudi garama namu part din muna sharansa har wajen gidan mu zaki gashi tsab dashi saidai a tsarin ginan yanzu na ya J yafi sauran girma don filin dake bayanshi an hade dashi anyi gina da aka karawa wajenshi girma sosai donshine nasa part din ya fita daban dana sauran. Ina zama saare na fadowa part din saida gabana ya fadi dana ganta na dauka wata tsiyar tazo yi min sai naji tana fadin . Ai bansan kina part din nan ba Ramaah dana shiga me kika bar su yaya sunayi da zaki fito nace kila abinci zasuci na dai dafa mashi taliya fara da ferfesun kifi yace ayi mashi. Wai kinsan wanan yaya mansur din abokin yaya saurayinane kuwa ya tambayeki ni ko ince kinji suna magana a kaina don Allah ? Wallahi banji ba ni ina kitchen na gama na aje masu na barsu suna hira a wajen na fito sai naji tace barin koma na gani ko sin gama ? Har ta gama surutunta ta fita maria bata daga kai ta kalleta ba sai bayan ta fita taja muna kofa maria din tayi tsuki tana fadin wahalalla kawai. A haka zata kare ance ko saurayin arziki bata dashi ina ganin shine na Abujan data lekewa tana so din nan yazo ? Itama ke sonshi mama bashi ke sonta ba aiko akwai aiki wallahi gara kaso wanda ke son ka ba wanda kake so ba anyi ma kina so yana so yaya aka kare balle wanda kake cusa kanka wajensa. Kudin daya ban na aje ina fadawa yar uwata din abinda yace nace shifa ya dauka aure yaya yayi sai zuba yakeyi harda miko min yana fadin gashi na sayen bakine tunda