← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 236 OF 306

Sashe 236

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani shewa ta sake wanda yasa hankalin mutanen gidan ya dawo gareta inda take zaune tana waya bayan kiran da Saare tayi mata din. Don tana ganin itace tasan da magana hakan yasa ta mike tabar wajen ta koma gefe daya don taji meta samu ta kirata kuma yau ? Nan ta fara sheda mata albishirinki Anty Saiba tace goro cikin zakuwa tace yar iskan nan Rahama tabar gidan nan tun jiya . Ke ki bari don Allah saiba ta fada tace wallahi yau su ya habu sunje kaduna wai su dawo da ita tace dasu bata dawowa gidan nan wai ? Haka suka juyo suka dawo su kaidai taki ta biyosu shine dslilin shewan nata da har ta dawo da hankalin mutane gareta. Saida sukaji tana fadin aina fada maki saaratu bashi taci wallahi indai nice yadda tasa nabar gidanku itama saita barshi wai abin haushima yayanki ai yafi ban mamaki saaratu. Wai ace yaki zuwa yaki ya turo tunda nabar gidan nan kamar dama yana jiran haka ya faru tsakanin mu to shegeb cikin jikintafa yana nan kota zubar ? A kema kinsan yana nan ai tunda tana son ace ta haihu da yaya ba dole tabar cikin ba saiban ta amsa da fasin shegiya ai bataga komai ba. Gara dani ba goyo ba ciki nabar gidan itako yar banzan ko zaman ciki ai ya isheta yar iska tana wasa dani saina mayar da yar iska ko abin sayen goro. Waima meya farune tabar gidan take tambaya ? Wani irin dariyan shakiyanci Saare din ta kwashe dashi tana fadin kin manta dani ke nan ai dana saka yar iska gaba saida naga bayan shegiya . Wallahi yarinyar nan baki san irin haushinta da nakeji bane ai hana shegiya shakar iska nayi ko walwalan kwarai ban bari tayi ba. Nusaiba tace dakyau nawa ina sonki irin wajen nan wallahi a aina fada maki ki barni da ita ita a dole tazo cin arziki to taci din mugani yar iska kawai. Saura wanan shashan matar habu din itama haka zan ta zuga mama akanta sai naga bayan shegiya su tattara subar muna gidan yan iska muggan iri kawai. Aini ba barin gidan wanan yarinyar ba Saratu naso har munafukin cikin nata ya zube banson ma tabar wani alaka a tare dashi wallahi ai in ta haihu dashi taji dadi kota abinda zata haifa ba a rabuba ke nan dai ? Barta aiko haka an nunawa yar iska iyakarta don daga kan yarinyar nan yayi yawa tana daukan kanta ita wata tsiyane kiga tanayi kamar tana jin warin mutane ita gata maidigiri. Sun jima suna zagin kansu waini a wajen kafin suyi sallama su kashe wayan uwar ta kallo Saiba tana fadin wa aka saka tace wai amaryan Jafar ce tabar gidan subbahanallahi uwar tace. Nusaiba wanan zaman gidan baisa kinyi sanyi kin koyi darasi ba ashe ? Na dauka wanan halin da kike a gida zaisa kiyi nadaman abubuwan da kika aikata a baya ai ? Yanzu akan abokiyar zamanki kikewa wanan mugun fatan haka har kina fatan Allah ya barar da cikin jikinta don Allah keda kika haifa wani yayi maki bakin ciki da hakan ? Sai yaushe zaki hankaline ke Nusaiba irama wace ke turu maki tsegumin tafiki rashin sanin ciwon kanta ai da zata zauna duk tsegumi da sirin gudansu tana aikawa waje. To ki guji naki a wajen ta ranan da zata kwaye maki baya tayi maki tonon sililin abinda kuke shukawa a tsakanin don tayiwa dan uwanta ciki daya balleke ? Dama sam rayuwan yarinyar ni baimun ba wallahi don na fahinci itace ta shiga tsakanin ki da Asmau tun farko ta hanaku zaman lafiya duk amintakan dake tsakanin ku. Duniyace ai ita ke koyawa wawa wayau koda baida fahinta wata rana duniya zata fahintar dashi keda ya kamata ki natsu a yanzu ki komawa Allah inda rabon komawamki gidan ki komawa uban yarki kin zauna kina wanan hauka haka ? Katse uwar Nusaiba tayi da fadin mama ke saiki dinga ganin laifinaita da tayi min fa ta hanani zama dakina ta rabani da mijina ? Oho ba zakiji ba kenan ko ta ina ta hanaki halinki dai ya hanaki zama a gidanki Nusaiba waye baisan halinki ba yanzu ? Duk hakkurin yaron nan da kawar da idonsa jan abinda kuke mai saida kika kaishi bango ya koma komu yanzu bai ganin darajan mu a idanunsa kuma ? Ai duk wanan sherin yaeinyar nan ce da baku son a fadi kaifinta har yaushe za a tsaya goyon bayan wace aka san itace matsalata amma baku son a fadi laifinta sai saratu dake kaunata ni gabadaya naso subar gidan ba ita kadai ba don ko Asmau munafukace ta gaske dole sai ta fita tabarni dashi. Tsuki uwar taja ta juyo tana fadin na yarda abin nan ya tabaki Nusaiba ki matsa harki samu tabin hankali Asmau dince zaki fitar a gidam jafar ? Shiko Yazid tun bayan dawowanshi yana part dinshi tare da iyalinshi dan baison yayi nusa dasu sosai hakan yasa tunda ya shiga bai sake fitowa ba. Sai washegari daya fito yaje gaida j din suka dan zauna dashi ganin yadda J din yake kwance yasashi fahintar yana jin jikin nasa ranan. Muryan J ce ta katseshi da yake fadin yarinyar nan taki dawowa ashe nayi mamakin hakan ban kuma san abinda taje ta fadawa iyayyen nata ba har suka riketa. Me zata fada J abinda kuke mata kai da mama da yan uwanka da matanka shine zata fada mana ai basuce ta fada masu komai ba . Illa dai tace ba zata dawo bane ita tagaji da abinda ake mata kai baka daukan mataki koda kana zaune kaga bata da laifi anan . Don kaika daukota J yakamata ace ka nema mata daraja a idon kowa gidan nan duk da suna ganin sun girmewa shekarunta amma dai shi zama tare baice hakan ba ai. Bsice don mutum yana kasa dakai yana auren danka ka dinga muzantashi kana nuna shiba komai baine haka kuma kowan ku yana kallon yaran nan da matanka sinaciwa yar mutane mutunci nasan da gidan nan ne ba zamu taba yarda aiwa kannin mu hakan ba a gidajen auren su. Shi habu wai yayi fushi don yarinya ta dage akan bata dawowa har saida yakai sunyi musayan baki dashi don gaskiya inda shine bai yarda aiwa matarshi hakan ai. Shiru jafar din yayi yana saurarenshi kamar yana tunane kafin ya jefowa dan uwan tambaya yana fadin atakaice dai yanzu nida mamane masu laifi a wajensu. Kwarai kuwa bros lafinka anan shine baka tsawatawa lamarin koda kana kusa akayi mata baka daukan matakin daya dace koda gobe ba za a maimaita irin hakan ba sai yayi murmushi ga dan uwan nasa dake magana. Yazid din yace kwarai kuwa bafa wai kai ka nuna mata concern a bangarenka alhalin tana samun musgunawa a wajen mutanen gida shine kawai abinda zakayi ba . Yama dole kabata kulawa a ko wani bangare kamar yadda kakeba kowa tunda kaika daukota cikin gidanka. Haka kuma ita mama kamar da saninta ake komai ga yarinyar nab banda wanan itama kanta tana yawan aibantasu a gaban kowa don ko gaida mama sukayi ance bata amsa masu wani lokaci kaga ba wanda haka zai faru dashi yaji dadi har ya zauna itace uwar mijinsu fa ni nasan halin mama idan ta tsargi mutum bros ka sani kaima ? Baiyi magana ba saici gaba da kurawa dan uwan nasa ido yayi kawai a inda yake zaune yayi shiru ya kafawa kasa ido yana tunane. Mikewa Yazid din yayi yana fadin yakama a gyara zancen nan abinda na guda kenan da matana kaga ban yarda ta shiga kwamacalan gidan nan ba don ina da labarin komai a wajen iya. Yanzu ya rage naka idan kana son matarka saika gyara ka shirya da abinka idan kuma ba yadda zakayi don Allah bros kabar yarinyar nan ta tafi taje gaba ta samu wani mijin . Sai a lokacin ya dago kai da sauri ya dubi kanin nasa dake magana Yazid din yace hakane mana ka sallameta ka zauna da wa yan nan mayayen naka lafiya tunda itace matsalanku. Ko dai makaho yasan irin hakkuri da sanin ya kamatan yarinyar nan kai kanka kasan ka tauye mata rayuwa a gidan nan don ba kalan macen da za a dauko a takura haka bace ita. Yazid idan da bansonta zaunan aureta gashi ka fadi kaima ko makaho yasan halinta na alheri balleni da kusan a yanzu yarinyar nan itace rayuwanta. Me nake tsunta a wajen wa yan nan marasa hankalin tunda na auresu sunan nayi aurene amma ba wani jin dadin rayuwa na ma,aurata a tsakanin mu. Na tabbatar da Rahama bata tare dani haka ya sameni gaskiya ko kwanana bai kare ba dana wullakanta ita kanta mama tasan hakan don tun bata aureni ba take dawainiya dani a kwance kan lalurana. Na zata dana yanke shawaran aureb yarinyar nan mama zatafi kowa jin dadin hakan a ranta ashe ba hakana bane a wajen mama don sai gashi ta juya zancen da cewa sihiri sukai min don suci arzikina kawai. To ashe kasan hakan ka bari ana mata hakan a gaban kowa bama kamar yar iskan nan Saratu da kawu da sune suka canza muna mama daga nan gidan kawu na nufa zanje amsan gadona dake hannunsa ko ba zanyi amfani dashi ba ina bukatan abina a hannuna yadda kowa ya karbi nasa . Da sauri yace da dan uwan nasa No Yazid kokaje kudin nan a yanzu ba samuwa zasuyi ba Yazid don haka ka barshi kawai don Allah. Duk abin nan da kawu yake muna sam mama bata ganin hakan a idonta saima idan mun matsa taga laifin mu zancen iyace datace ba banza suka barta ba. Kaga na dauka akan zancen nan nawa da kawu keda hannu a cikinsa zaisa mama ta gane waye kawu sai gashi naga yanzuma suke wani shiri na daban a tsakanin su don haka karkaje ku samu matsala da mama don Allah. Dolene inje bros so nake in kawo karshen mutumin nan ai masa iyaka damu yadda zai fahinci yanzu mun girma ya fita daga tsabgan mu gaba daya. Mamace yar uwarsa bamu ba ka bari na
Chapter 236 · 0% Book details