Sashe 129
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ba so sorry kiyi hakkuri da hakan don Allah ? Na boye kaina a cikin jikinshi yacigaba da fadin Allah yayi maki albarka naji dadi sosai jiyan kamar nayi kuwa ban sani ba koma nayi din ai ? Dariya yaso subbuce min na kara noke kaina saman jikinshi yace wallahi Rahama komai naki yai min a rayuwata ina sonki sosai mu sanman kamshin nan naki don Allah ki bani hadin kai mu zauna lafiya. Kaina gyada kana na furta a hankali da in sha Allahu yace ba zan manta da rayuwan daren jiya ba da komai na cikinsa har wanan cizon da aka gyatsira min a wuya . Ina son wanan daren har kullum ina son abinda ya faru a daren abinda ya faru a cikinsa wani irin nauyi da kunyane suka rufeni nasa. Yace Allah kuwa gaskiya nake fada Rahama na rasa inda zan saka kaina a jiyan kamar in bude cikina ki shiga naji lokacin don tsaban sonki dan Allah kici gaba da inganta min sauran dararen da zamuyi tare dake a rayuwan mu. Ya dagoni yana kokarin mu hada ido dashi yake fadan hakan na kasa yadda yake so din na daiyi kokarin daga mashi kai alaman in sha Allahu. Naji yakai min kiss a goshi yana fadin bari naje na rage kayan nan a jikina in dan watsa ruwa in dawo in baki abinci ya fada tare da sakeni ya juya ya fita daga dakin. Zaune nakai a hankali bakin gado ina sakin ajiyan zuciya wai yau ni Rahama mutum kamar yaya Jafar yake fadawa irin wanan maganan a kaina. Dama ace ni kadaine fa in more miji har miji a nan saidai kash kadara ta riga fata nidin a haka ragowa na samu ragowan wasu ma bako mutum daya ba. Take naji wani irin kishin matan nasa ya tokare min zuciya a karo na farko tun faruwan alakan hada aurena dashi sai wanan karon naji zafin matan nasa. Zafi na daban ba irin wanda nake ji nasu ba a baya akan matsin da suke min kan yar uwata wanan wani na dabanne ya ziyarci zuciyana. Kwance nake rigingine a yadda ya sameni da farko na soma tunanen ko yaya zamana dasu yanzu a matsayin kishiyarsu zai kaya oho ? Na sandai wata rana dole a hadu an kuma ce mai hali baya fasa halinsa sai yayi koda kadan ne ashe zan iya kyalewa in shanye duk wani cin fuskan da zasu iya min kuwa ? Kai ina dole in rama a yanzu ga duk wace taso barazana a kaina basu ba koma wacece indai akan yaya jafar ne ba zan taba kyale mashi ba kuwa. Haka ya dawo ya sameni Tsarki da aminci su tabata ga Allah na furta a raina lokacin dana kyala ido nagashi tsaye a kofana cikin kananun kaya wando da riga iri daya saidai wandon iya gwiwa ya tsaya mashi haka kuma rigan ya dan sauka ya dan rufe zuwa cinyarsa masu ruwan kalan dorawa da akaiwa rubutu a gaban rigan da gefen wando cikin manyan haruffa da FREE MAN. Na nanata kalman a bakina har lokacin yana tsaye yana waya yana fadin gaba daya za a kwarai massallacin na fada masu sai a kara mashi girman tako goma ako wani bangare tunda akwai sauran fili wadattace da za ai hakan. Duk wani kayan da za a kawata massalacin dashi na riga da naba garba kwangilansa shi zai sayo ya kawo banson aikin nan ya wuce nan da wata biyu insha Allahu tunda akwai komai a kasa. Aina fada mai Habu zai kawo mai kudin komai da mukai killisafi dana zirga zirgansa duka gaba daya ya dan jima yana saurareb bayanin abokin maganan nasa kafin yace hakan ba matsala bane ai ayi komai yadda ya dace kawai. Ya kashe wayan yana kallona ban farga daya gama wayan nasa ba saida ya ware hannayesa alaman inzo garesa niko na shagala da kallonsa ban farga ba lokacin na sauke wani irin ajiyan zuciya ina mikewa. Na tako zuwa wajenshi hannuna ya rike a cikin nasa yana rada min tafiyan nan naki ba daidai bane har yanzu Allah ya taimakeni ba kowa a gidan nan danaji kunyar hakan a idon mashi. Ledan daya shigo dashi din ya dauka nidai har mamaki yake ban yadda shi bai kunyata ko nauyina zakice mun dade da shakuwa dashine lokacin. Falo mukayiwa tsinke saida yaga na zauna ya nufi gaban tv ya kunna ya dawo ya zauna lokacin nake fadin a dauko abincine nan ? Abinci kuma ya dago da sauri yana tambayana nace na girka abinci dazun danaji sauki Ohho no no a hakan kika wahalal da kanki Rahama ? Baki da lafiya fa kin sani da badon karna shafa maki bakin jini ba daga zuwan ki Allah ba inda zan fita yau ina gidan nan ina jinyar abina nida nayi barnana da kaina. To amma rashin fitana din zai iya shafa maki laifi ga mutane da yawa musan man mutanen gidan mu sai a dauka kece kika hanani fita. Da ina nan ba zakiyi wanan wahalan ba haka na dan kalleshi cikin marairaicewa nake fadin don nayiwa yayana girki kuma shine wahala ? Haba dai ai naji saukina kuma ban iya badin ka da yunwa tunda nasan kai kafi son cin abincin gida ko yaushe meye a cikin dan girkin iya bakinka kadai ? Na mike zuwa dinning na dauko abincin zuwa inda yake zaune na aje a gabanshi ya kalli kayan yana fadin kinsha fama wallahi. Allah yai maki albarka Rahama sunan ki yaci ke din mai tausayice da imani da har kika iya fahintana wallahi kamar kin shiga raina kin gani ina tunanen abinda zanci mai dan nauyi da daren nan kafin in kwanta. Kinsan ni din rainon iyace ai ban wanka in bushe a gidan mu ina dakin iya duk da mahaifin mu bai yarda na zauna a wajenta dindindinba saidai in tafi in dawo gidan mu in kwana. Ya bude abincin daidai ina aje mashi ruwan sha dana wanke hannuwa ido ya lumshe ganin yadda semon yabada ma,ana a cikin ledan dana daresu a ciki kulli biyune na saka mai ya bude miyan yana furta masha Allah. Zaman dirsha yayi a kasa da alaman haka zaici abincin a lokacin ina kokarin kaiwa zaune kujeran dake kusa dashi naji yana fadin zo nan ki zauna yana nuna min wajen zama a gefensa kasa haka yasa na sauka na zauna kusa dashi din kamar yadda ya bukata. Naji yace waima in tambayeki don Allah Rahama kudin da gaskiyane kun taba zaman daji kuwa ni sam banga alamun hakan ba gareku amma ance a rugga habu ya gano muna ku ? Murmushi nayi ina fadin a can ya ganmu mana zama na shekara biyar mukayi a rugga tare da baffab mu na fada ina zuba mashi abincin a plate yana bin zanen hannuna da kallo cikin mamakin abindana fada.