Sashe 69
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Basu iso zaria ba sai goma na dare nayi barci a lokacin don mun dan samu sabani da anty Saare inda Iya da anty Nafisa suka shigan min da cewa. Idan banyiwa yar uwata abinci nakai mata ba wa zai kula min da ita tunda mijinta lalura ya kamashi yanzu bai cikin hankalinsa akan dan uwansa. Hakan kuma sai ya zama laifi saratu ba dole bane duk abinda ta dafa ace saita zubo muna tunda abincin asibiti takeyi abinda mara lafiya ke ra,ayine ai ta dafa mata ni inama ganin kokarin yarinyar nan wallahi nafisa ke fadan hakan . Saare ta kallota tana fadin kada tayi kokari mana wa tayiwa ba kanta ba nifa dole in fada yarinyar nan tunda taje Abujan nan ta dawo ta canza gaba daya a gidan don taje Abuja zatayiwa mutane daukan kai kamar wace taje london. Abinki dai hassadane Saare inbashi ba wani daukan kai yarinyar nan takeyi gidan nan yarinyar da bata ko saka kanta cikin sha,anin kowa ? Dama ai hassadane hakan kada ki dada ki kara indai anty Saarece yanzu haka acan lungun yaya J akai haka tazo ita ta ara ta yafa abinda bai shafeta ba. Ramaah tun wancan case din da akayi na kayan sallah da kuka hana a bata ta kama kanta a cikin gidan nan sai tacewa yar uwar nata salima dake magana. Wa zata kamawa kai mufa nan gidan mune ba cin rani mukazo ba wanan yasa na fito daga dakin iya dana idar da sallah magariba nake fadin. Anty Saare nima gidan mijin yar uwata nazo idan ba haka ba aiba zaku ganin gidanku ba nasan baki kaunar zaman mu gidan nan kuma Allah yayi mu zauna daku din tunda Habu ya dauko yar uwata dole ki ganni a gidan in baki son ganina yau kisa Habu ya saki Yanda gobe idan kin ganni ki fadi abinda kikeso a kaina. Ke nikike fadawa magana haka Rahama ke yar gidan uban waye nace yar gidan ubana malam Aliyu bafillace rugga da kika fada. Shi kenan kun dauka mu fulani dabbobine bamu da wayau ko hankali kowa sai yaso ya raina muna hankali girmanki nake baki don abubuwa amma tunda baki so muje a hakan ai kowa ya iya rashin mutunci. Yanzu kin samu abinda kike so ai tunda kikaiga fada yarinyar nan ta fada girma kuma ya fadi ba salima ta karbe iya data soma maganan a lokacin. Bata daiji dadin kowa ba a cikin zancen donshine tunda na shiga daki ban fito ba tunda naji kawu na fadawa iya ba zasu kwana ba donshine banje part din su Yanda ba. Sun gaji da zaman jira suka kwanta sai anty Salima dake zaune tana kallon film wayanta itace taji dawowansu maigadi yana bude masu get. Ta tayar da iya tana sheda masu sun dawo taji maigadi na budan get din yana gaidasu da dawowa a lokacin hakan yasa suka bude kofan ni dai ban fito ba don idona biyu ina hadiyan bakin cikin Saare a zuciyana a lokacin kinsan bafulace da bakar zuciya dama. Sai washegari dana fito na gaida mama dake zaune falo tanawa iya bayani abinda mai magani ya fada ta juyo tana amsawa kafin na mike nakoma daki tabini da kallo. Kodai yar nan malamin nan yake nufi dai don wanan kunun tsamiyan da take damawa shi kadaine abinda Jafar yake sha ya zauna a cikinsa. Kai ba ita bace dai nafi sa ran Nafisace dai bata kai karshen zuci ba da takeyi taji iya na fadin jiya Saratu bata kyautawa yar nan ba. Akan abinci ta zauna taci mata mutunci a gidan nan wai tayi girki bata zubo masu ba ta zuba min ta kwashe takai asibiti zokiga yadda tayiwa yar nan falle falle a gidan nan jiya. Garin yaya haka ya faru kuma me saratu ke nema da yarinyar nan don Allah ai jiya takai ga bata amsa ta fada mata ba,a daji aka daukosu ba suma suna da uba ai dalili yasa ta ganta nan din tasa habu ya saki yar uwarta idan ta sake ganin fuskanta a gidan nan. Ai gaskiya ta fada idan ba dalilin yar uwarta ba ta yaya zamu ganta gidan nan da tana zaune ta mike kafa habu ya kawo masu yar aiki ko ? Bafulace zaka rainawa wayau ka zauna lafiya don ma yaran nan nada wayewan kai suna amfani da iliminsu aida ta dajinne datace data gane bata da wayau gobe ba zata kara raina masu wayau ba. Murya tasa tana kirana daga falon na fito take fadin Rahama daga yau nayi maki iyaka da sa,insa a gidan nan kinji nasan an bata maki rai amma kiyi hakkuri itama zan fada mata wanan halin banzan nan data koyo ba alheri bane ga mace tagani ta gaza shiru komai kace sai kayi magana akansa kana tare da wahala bance kuma inkiyiwa yar uwarki abu sai kin dibawa kowa ba tunda suna da hannayesu kiyi hakkuri kinji Rahama. To fadane dai gashi nan irin ta uwa mai son yayanta bata goyi bayana ba bata kuma nuna nayi laifi ba wanan shi ake fadin wanka da jurwaye ke nan. Na daiji amma nace nagode mama tace ba komai kinji gaba zai maki amfani yar nan hakkuri baya baci gabawa. Allah yaba yar uwanki da Jafar tare da sauran al,umman musulmi lafiya na amsa da amin nashige daki ashe ta samu Saare a can tayi mata ba dadi a gaban kowa. Saiba ke fafin amma mama kada kuba wanan yarinyar garati da yawa ta dauka daya take da mutane a gidan nan ko banza ai duk sun girme mata don me zataki masu girki. Ya J dake kwance sama dogon kujera mai ci mutum uku ya dago yana fadin wanan wani irin maganan banza kikewa mutane ? Kinfi nama sanin abinda ya dace tayine akan mu ko kinfi yarinyar wani darajane a wajenta ? Koko an fada maki boya aka kawo masu ina da niyar wanan maganan mama ta rigani don aikin da yarinyar nan keyi a gidan nan babu wace cikin ku dake yinsa tafiku wawiya kawai ko ta zauna tayi girki aci hankali kwance wanan ba daraja bane banda cin mutunci me kika koya ke ? Zancen nan dai ba naka bane jafar ka barta aina san abinda nakeyi ba zan zuba ido su saka yarinyar mutane a gaba ba ina kallo aiki ya wuce nawa da iya kona yar uwarta ba zata kara kauda kara a gidan nan ba. Wanan ma da iya ta dauko kwanan ta uku batazo ba son bata iya kallon ga mata zube amma basu iya komai wa zai zauna yana wanan wahalan haka ? Suna cikin wanan zancen muka shigo da Iya a cikin jam,i na gaidasu kafin nace yaya ina kwana ya karfin jiki ya amsa da Alhamdullahi . Yadda naga fuskokinsu yasa na fahinci akwai abinda ya faru don haka ban zauna ba na mike don barin falon don kusan ni dayace bare a cikinsu. Kin hada abincin asibitin ne Rahama mamace take tambayana na juyo ina fadin na rana zanyi masu yau sunce abar na safe zasusha shayi. Ai shike nan sun hutar dake aiki naso naje na dubasu saidai abinda hali yayi zuwa anjima tunda jikin jafar din da sauki sosai yau insha Allahu. Ya dace aje a dubasu kada suga rashin hankalimu iya ta fada mama din ta sake fadan insha Allahu zan kekasu yau ina ganin can Habu ya nufa tunda safe. Ban tsaya ba na fita naje aikin gabana sun dan jima zaune kafin ya mike zuwa daki yana fadin zai kewaya. Sumama suma suka bar falon don gaskiya maganin da alaman ya karbeshi sosai ba bugun kai da yakeyi a lokacin nafisa ta rigasu barin falon ta koma part dinsu. Salima na zaune tana dakilan wayanta suka fara magana Saiba tace dole tayi hakan don ta danje Abuja tayo clean baki ganin daga kan data fara yiwa mutane tunda sun iya asiri . Babu asiri sai iskanci a ina wanan zata samu asirin balle tayi Asmau take fadan hakan haka kike gani da asirinsu ake haihuwansu. Yar kauyece fa kibar yan kauyen nan inda kike ganinsu sis haka suke kiran junan su tun farko yanzu in ana dadin rai hakan ake furtawa juna sunan na sis idan fada yazo kuma za a kira mutun da sunansa na yanka. Boni ya tabbata ga mai zunde yanzu me yarinyar nan tayi maku da zaku sakata a gaba da zaki harda wanan irin zargin inma asiri tayi ai baku tayiwa ba dai ko ? Salima inma tana asiri tasan wanda zatayiwa nikan nafi karfinta har kowa nata kuwa haka dai kikace idan baka damu da mutum ba ai baka zaman kushesa haka ? Ke Saare bar part din nan kafin ranki ya baci yayan nasu ya fada yana nuna mata hanya don ransa ya gama baci da wanan halin nasu. Ke kuma Nusaiba abinda yarinyar ta tsare maki saiki kokarta ki koreta a gidan ki samu sanyin a ran ki tunda zamanta ya tare maki wani abu. Salima ce ke ban labari daga baya zamuce Alhamdullahi don gaskiya jikin nasa yayi sauki sosai sati daya ya iya yi a gida ya soma harkokinsa na yau da kullum. Haka salima da Saare sun koma wajen karatunsu ya rage gidan dagani sai Nafisa da zance zamanta ya dawo nan dai ke nan don tafi ganewa zama a nan din donko da mama zata koma gida bata bita sun tafi ba tace sai mama ta dawo ita tana nan ba yawan hayaniyan nan na gidansu. Shakuwa sosai na tsakani da Allah ne a tsakanina da Nafisa don tankar yar uwa ta daukeni inda har dan fi min salimama zance dadin zama don bata da son kanta tare muke komai da ita. Ba irin rayuwansu bane ita ba sai ta jira kayi mata abuba ita zata tashi tayi da kanta dama aikin dai iya girkine kawai inyi na safe tayi muna na dare wani lokacin idan tana gida tare zamuyi aikin da ita. Watan haihuwan yar uwata ya kama kowa hannunsa a gaba duk da likitoci sunce babu matsala ga hakan saidai komai a hannun Allah yake ai ba a wajensu ba. Allah cikin yardansa ta haifi danta