Sashe 122
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tauyeni kamar ya shake min wuya don yaga inata kokarin sasautawa da hannuna hakan yasa ya dan kara rankwafowa saitin fuskana yana kokarin cire min daga jikina. Ina jin yadda ya sauke ajiyan zuciya lokacin da yayi arba da suran jikina daya dan baiya afili daga yanayin dinkin rigan jikina. Dagawa yayi daga rankwafin da yake naga yana shafo suman kanshi da hannunsu wani irin soyayyata yana fisganshi lokaci guda duk ya dan daburce yana fadin kinci abinci dai ko ? Bana jin yunwa na bashi amsa a takaice ina mikewa daga yadda ya barni a kwance don irin kallon da naga yana kare min sai lumshe ido yakeyi a cikin wani yanayi na gajiya. Da alama baki son cin abinci Rahama kosai na zauna kwana biyu ina baki da kaina zakicine ina kula ko dazun bakici komai ba koso kike antyn Abuja tace ina maki sakacin kiyon ki ? Ni ba sai ka zauna ba dama haka nake ba ko yaushe nake cin abinci ba sosai nafi son abu mai ruwa ruwa dashi na saba rayuwata da nake zuwa kiyo a rugga. Hannu yakai ya ja min hanci yana fadin bazan taba yarda da hakan bani donki na aje komai a gidan nan Rahama. Kici sai kince min kin gaji da nau,insu na cabza maki wasu don kanki saina turo baki cikon shagwaba ina dan kauda kaina gefe daya. Yayi murmushi yana fadin watarana basai nace kici ba Rahama kece dai zaki dameni da inci din ranan da kika haifa min kyawawan yaya masu kama dake ba zakiso ko kudi ya sauka a kaina ba lokacin. Saidai zanso ki haifa min ya mace mai kama dake sak mai irin tsayinki da hancin nan naki da gashin nan yakai hannu yana kokarin taba gashin kan nawa nayi saurin gwaucewa ina murmushi. Falo muka fito tare zuwa dining ya zauna na fara bude abincin ina kallon sanda ya lumshe idanunsa naci gaba da hada mai na aje komai na zagayo na duka a gabanshi yabini da kallo. Takalman dake kafanshi mai belt don na kula yana son saka irinsu shi din dan gayune na karshe idan yai shiga saikin tsaya kina satar kallonsa wani lokaci. Komai nasa a nutse yakeshi nasan kuma shida kansa ke tsayawa yiwa kansa lalura wani lokacin koda wanda ya kamata ace mace tayi masane ya rigada ya saba da hakan. Kafafuwan nasa ya kara miko min na karsa zare dayan ina kokarin mikewa naji ya dafa kaina yana fadin sharp kinga na manta da takalma a kafana na zauna. Allah ubangiji yayi maki albarka Rahama sunan ki yayi daidai da halinki na kirki da sanin ya kamata daidai da addini yadda ake son mace ta kasance harta bawa yara tarbiya ke nan. Nidai dai murmushin iya baki na sauke na juya da takalman zuwa dakinshi naji yana fadin wai ina Nafisane ? Ta tafi gida dazun nan ta wuce wai zataje ta duba su inna sai yayi dan murmushi ya kada hannu a ruwan dake gefenshi yana dauraye hannunsa . Na juya nakai takakman dakin na dauko mai wasu sifas masu kamar gashi a jikinsu wanan duk hikiman anty Salmace saida ta jaddada min kan wanan akidar na kula da bashi takalman tafiya a cikin gida ta kuma nuna minsu din hakan yasa na fara amfani da nasihar nata a lokacin. Na zo na aje masa a gefe inda inya daga zai saka na zauna a kujeran dake gefenshi abincin naga ya debo ya nufo bakina dashi na noke kaina ina fadin zanci ai idan ka gama. Bai tsaya saurarena ba ya mika min dole na bude baki na karba a haka mukaci abincin waya ya mikar dashi daga wajen wanda na fahinci daga matansace dake mashi cin mutunci a cikin wayan a kaina. Kayan na shiga tattarawa na nufi kitchen dasu ban fito ba saidana dauraye na kife na dawo nagoge dining din na nufi dakina don ya shiga dakinshi tun lokacin. Kayan jikina na sauya na kara muke jikina da dan kamshi mai saukin shaka na dauko riga cotton bubu mai gyale na daura a kaina lokacin wayata tadauki kara ina dubawa anty Salmace a layin. Na dauka da sauri muka fara gaisawa ina tambayanta yara da gajiyan hanya take fadin suna lafiya suna wajen lesson . Kafin naji ta dora da fadin to yaya ashe ango ya dawo sai ta kwashe da dariya nima a bangarena murmushi nayi kawai a lokacin. Take fadin komai daidai ko murmushi mai sauti na sake kawai tace ato na dai fada maki yanzune zaki koyi narkar mashi da zuciyanshi akanki kada ki tsaya wanan sanya da kauyanci. Kiyi kokari ki kafa taki gwaunatin a zuciyarsa ta yarda zai mata da irin ukuban daya saba dashi wajen wa yan can garorin matan nasa. Duk abinda kika sai zai farauta masa Rahama ki daure kiyishi don Allah kicire duk wani kunya da nauyi ki nuna masa kulawa fiye da zatonsa tunda abinda yajashi gareki kenan dama samun natsuwa a wajenki din. Muryanshine ya katse muna hiran da yashigo yana fadin kin kwantane Rahama ina son na leka gidancan in dubusu ban samu tsayawa dazun ba dana shiga abubuwa sunyi min yawa a lokacin. Saika dawo yaya agaidasu dasu dasu hajjaju da iya ya amsa da zasuji har yakai kofa ya juyo yana fadin kada kice zaki sake wani girki ki huta hakana sai gobe don Allah zan riko muna abinda zamuci da daren. Saida yakai kofa nake fadin da anty Nafisa zaka dawo ko ? Sai naji yace kina son ta dawone shiru nayi na kasa cewa ehh don irin kallon da yake jifana dashi lokacin ya juya yana fadin banjin hakan su dan huta a gida kwana biyu. Yana fita muka cigaba da hiran mu da anty salma din dake min sherin a,a komai zam kan ga alama nan naji da kunnuwana . Kin gane yanzu fa abin kamar compertion ne a tsakanin ku kowa ya biya allonsa ya wanke suma zasuyi kokarin ganin kin zama banzace a wurinsa don haka shiga gidan mata biyu akwai hatsari babba ga mace sai ka iya takonka sosai dasu. Mun dai dauki lokaci zancen ke nan guda akan zamantakewan aure ta yadda zan zauna da kowa kafin mu dauko hiran su hjy yabi muna dariya wanan ya shagal dani na manta da komai saida aka kira sallah na mike zuwa alwala. A gidan su kuma yana isa yaran ya sama a kofan ya Habu suna wasa da Abba ya fito mota ya nufi wajensu. Zaune yayi ya dorasu saman jikinshi yana dan jansu da hira irinta yara jin shiru yasa maria bude falon don taga ko Abba yana kusa. Sai tayi arba da ya J din ta dan daburce don tunda abin ya faru basu hadu ba sai wanan karon suka hadu dashi din. Shine ya fara gaida ita wanan karon taji abin wani banbarakwai tana fadin sannu da dawowa yaya ya hanya lafiya yaya gida dasu Abba koda yake gashi nan yana fada min wai yana son karatu . Tayi murmushi ta juya zuwa ciki ta barsu a wajen yake fadin gashi ai zamu shiga ciki take fadin dama wanka zan mashi nake nemanshi. Ya iza yaron zuwa gareta ya rike hannun yaransa zuwa part dinsa inda ya samu matan basa a zaune falo duk da suna a waje daya kowa da abinda takeyi a lokacin. Sallamanshi ma da yayi sai Asmauce ta amsa mashi da kyar itama dai a cikin basarwa tayishi bai kula da hakan ba ya zauna a tsakiyansu Yana fadin ya Asmau ya karfin jiki kuma sai saiba taja tsuki ta mike kafin ma asmaun tayi magana tabar falon a cikin hasala binta yayi da kallo ya dawo da dubasa ga Asmau sake fadin lafiya gamu dai muna ja ai. Ai watan haihuwan ki ke nan zai kama ko tace haka akace saidai idan Allah ya raba kawai yanzu Allah ya rabamu lafiya ta amsa da amin. Badai wani matsala ko tace da sauki gaskiya kinje asibitin da kikace tace naje naga likitan shima yake fada min edd dina ok ya fada. Yarshi data hau saman cinyarsa tashishi ya biye mata suna hira kafin ya mike ya shiga wajen saiban dake kwance ta kafawa siling din dakin ido tana tunane. Nusaiba ya wai meye matsalankine haka ta dago daga yadda take ta watso mashi harara tana fadin matsala matsalan me kagani a wajena ? Naga kin gani kina basarwa mana kamar baki ganni ba tace oh so kake in daukeka in goyaka tunda ka tuna damu kazo garemu yanzu ? Yayi murmushi yana zama a bakin gadon daidai kafafunta ta wani jaye kafanta da sauri gefe daya ya sake fadin wai meye hakane wai ? Cikin kyarmar murya ta soma magana tana fadin me kuwa ko kagawani abune a wajena kaje wajen wace kake tunanen ta fimu wani abin daka zabi tozarta mu a idon mutane . Tozarci kuma ya fada tace koma meye dai kaika sani da abin kunyanka tunda baka daukeshi komai ba ya mike yana fadin Allah sarki auren da nayine abin kunya kuma yau Nusaiba ? Ashe aure yana zama abin kunya a wajen ki don na auri wace kika sani na hadaku a waje daya a matsayin matana ? Wanan kuma kaiya shafa don ni wanan figagan yarinyar karamar yar iskan da kake kallo a mata bata isheni ko kallo ba balle . Allah ko niko kinga ko gajiya baniyi da kallonta da tayi min dari bisa dari ko kifta ido idan tana kusa ban iya yi yanzu . A hakan kai har kaga mata ke nan ita dai Ramaah din dana sani ko ancanza mata kamane kuma ? Ya gyada kai yana fadin itafa yanzu ai in ba itaba banganin kowa a mace yarinyat data san zafinka tasan ciwon ka ako wani hali ka shiga ina zanga daidai da ita. Don haka inma kushe min mata kike kokarin yi gara ki daina don ita din tauraruwanace a yanzu tunda ba zata taba guduna ba duk halin da nake ciki kuwa yasa kai ya fita ya barta tana ta zunduma ashar. Ya jima a falon kafin ya shiga wajen iya daga can ya wuce masallaci bayan an fito sallah ya dan