Sashe 252
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
nayi mashi kafin naje gida dana koma gidana kuma maman tudu ce ke taimaka mashi. Zance hakan kamar shagwabane wanda ba hakana bane saukin daine kawai ke shiga a hankali lokacin don yanzu yakai yana dan lalabawa yaje da kansa. Saidai ina ganin hakan na mike zama ya fara yi ina gaidashi da mashi sannu da jiki ya amsa yana fadin koya makarane nace ba a tayar da sallah ba ai a lokacin. Yana kokarin mikewa tsaye ganin yanayinsa yasa na tuna da zancen likitoci da suke fadin idan mutum ya tashi da dare koda safe daga barci ba a son ya mike farat daya sai ya dan zauna jininsa ya sauka don gujewa faruwan sturk a gareshi balle wanan dake halin ciwo a yanzu. Daka zauna tukun na bashi amsa yake fadin wallahi naso tashi kuma na kasa kinga yanzu abin dake damuna shine duk ilahirin jikina sai na dinga jin yana min majirya wani lokacin. Wani lokaci kuma sam banjin hakan a tare dani amma hakan yafi faruwa gareni da safe haka ko da yamma idan na dade a inda nake fitowa insha iska. Kinsan yanzu sun daina tayar min da injin don kawai Asmau tayi magana ranan kan an jima ba a tayar da injin din ba wanan yan iskan yaran suka fadawa mama shine tace samun wajene ai ? Ko gidan ubanta ana tayar da injine haka balle ta kawowa mutane iskanci to injin din ma an daina tayar dashi idan akwai wutan nepa aga haske din. Idan babu kuma kowa ya zauna hakana kinga ni basu damu dani ba koda mutuwa zanyi ke nan Rahama kansu kawai suka sani sai naga yayi murmushi yana hada hannayesa a waje daya. Kafin ya dago kai yace amma kinsan me kuma duk sati sai ansaka kudin mai a cikin buget din da za a fitar nidai kawai kallonsu nakeyi fatana a yanzu shine. Idan ina da rabon tashi a ciwon nan Allah yaban lafiya mai amfani gareni da iyalina idan kuma hanyar tafiyanane hakan Allah ubangiji yasa na cika da imani Rahama. Tausayi sosai ya ban a zuciyana wanda nagane maza da yawa ashe in sun kwanta ciwo suna ganin takaicin duniya a kan iyalinsu ban ji tsoro ba saida naji yana fadin kinsan me kuma ? Nace a,a yace duk basu zata Allah zai ban lafiya da zan mike kamar haka bama a yanzu ba karamin illa sukaiwa dukiyana ba Rahama zancen dai kawai ayi shiru tun Habu yana hanawa yazo ya fada min har yakai yanzu shima ya soma nasa hada hada a ciki saidai nayi kamar ban fahinci hakan ba garesu. Yau dan uwakane yayi ma hakan da mahaifiyarka to don wani yayima me zakace mamafa wai har cewa tayi a ware wasu kudi don auren yaran nan kada nazo na mutu kudin su shiga cikin magadana ? Ki duba wanan zancen don Allah Rahama wai mahaifiyace takewa danta hakan me zan fada a yanzu suyi min hakam waye ba zai min ba nasan wanan shirin kawune sarai shike turata duk wanan abubuwan . Bansam lokacin da bakina ya furta to wai ku baku iya maganin kawu din nan ne mutum yana cutan ku kun sani amma kuna taushewa don Allah ? Bai ban amsa ba sai murmushin da yayi yana fadin kamani inje inyi alwala kada mu makara ga sallah lokaci naja hakan yasa na kamashi ya mike tsaye zuwa bandaki. Bamu fito ba saida yayi komai ya fito na gyara mashi inda zai zauna yayi sallah na koma na dauro alwala na fito nazo na don har an tayar da sallah a lokacin. Na idan na dan zauna nayi addua kafin na mike zuwa kitchen tea mai kauri na hado mashi nazo dashi dakin yana zaune a wajen har lokacin. Na mika mashi bayan na fifita ya karba ya shanye yana min godiya ruwan dana tofe da addua na mika mai ya dora a sama bayan yasha na shafe mai jiki dasu tsaba na kamashi zuwa gado ya kwanta. Na gyara mai kwanciya yadda zaiji dadin samun barci zan mike yake fadin ki kwanta mana ki huta nace ina zuwa kawai na fice daga dakin zuwa dakin biba na tayar da ita don tayi sallah. Duk aikin da nakeyi zancen mu dashine na dazun ya tsaya min a rai na na fahinci wanan abin sai an koyawa mutanen nan wayau a rayuwansu. Wani abin ko baka da niyar yi mutane suke sakaka yinsa don fansan kai matsala guda kishiyoyina haka take garesu duk inda aka juya mu can suke. Haka kuma ba zamu taba rabuwa da wanan matsalan bafa matukar talikin nan yana raye sai mun rabu da mutanen nan kamar yadda yaya habu ya tsame kansa cikinsu a yanzu. Dan zama da igiyar auren Jafar yasa na fahinci abubuwa da dama game da zaman gidan wanda a baya ban kai fahintar hakan ba a lokacin don abune dabai shafeni ba lokacin. Don haka ya zama dole na fito da halin fulatanci na mugunta da nuna wayau wawaye yanzu garesu don tsirar da mutuncin mu ga baki daya. Mama ko a gaban mu da yar uwata idan abinta ya tashi zatace ita makircin fulani ai duk ta sanshi ita da tayi zama da inna amarya ana gwada mata fulatanci ? A yanzu zata fahinci fulantanci ba komai bane sai zalla wayau da kissa da iya duniyanci akauyance muke shammatan mutum. Abinci lafiyayye na shirya mashi wanda nasan zai kara gina masa jiki ya samu lafiya don ramansa tayi yawa a yanzu ba son nakai zuciya nesa ba saima na zargi zama a kusa dashi din. Kamar yadda saudi ta ban shawara na zage in kula dashi idan yana wajena ta yadda ba zai iya boye komawansa wancan gida ba a fili ta hanyar bashi kula ta musanman. Don ita saudi irin mantan nan ne da suka kare rayuwan kurciya a bariki har lokaci ya kare masu basu sani ba sai a koma yan kame kame saboda girma. Wanan ya kaita ga aiki gidansu ummah ita din ance wata yar uwar su daddyne ta haifeta gashi tana bala,in jin tsoron daddy wanan yasa a yanzu ma don ta natsu ya zaunar da ita a gidansa yana kuma yi mata albashi. Alhamdullahi din ta natsu kamar yadda yan uwa suke mata fatan hakan wanan yasa bata da shamaki a gidan din nasu yazo daya da ummah sosai saboda bata takura mata ko kadan. Itace kuma a irin hiran mu ta kara min haske akan zama da irin su mama da iyalanta wanda wanan huduban hakan yai min tasiri sosai a cikin zuciyana a lokacin. Na lekashi a dakin na samu ya samu barcinsa sosai har baisan inda yake ba a raina nace har yunwa a cikin lamarinsa na fito falo na tsaya muka gyara da biba don gudun girshi a gareni azo a samu gida ba shiri wanan kesa macen kwarai ke gyara gida tunda safe kazama kuma malakaciya itace ke zama har wani lokaci gida ba gyara ko jikinta nakoma dakina nayi wanka. Bayan na fito na zauna na shafe jikina da mai sosai na zauna nayi kwaliya kafin na fito daga gidan har jikin mu duk ya dauki kamshi yadda nake so . Ina cikin irin mutanen dake son kamshi a rayuwansu don hakane ban wasa da kamshi a lamarina ko don tashi a wajen mummy Abujace na kasance a hakan oho ?