Sashe 13
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
idan kayi tunane tunda kana da contact dina zaka iya kirana naji shawaran daka yanke akai . Takai hannu ta kamo nasa hannun tana fadin kada ka damu Allah ne ya hadani dakai abar zancen so yanzu a tsakanin ka daukeni yar uwa a wajen ka. Zanso ace kaima ka shigo cikin system duniya tanayi dakai kamar kowa amma ta hanya mai kyau bata banza ba. Hannun nasu data rike ya kalla tayi saurin saki tana fadin sorry na manta dakai malam ne ai addinin ku bai yarda da hakan bako iam sorry for this. Ta sake ta gyara tsayuwa tana fadin ni zan tafi saina jiki nasan ba zakace a,a by god gra grace don abune maikyau da zai tamakawa rayuwanka. Nagode yace da ita zanyi tunane akai idan babu matsala zakiji itama godiya tayi mai suka rabu ta nufi tsadadden motanta dake fake a gefe fara sol mai shegen tsada da sai wa yanda suka kafu suke shiga irinsa. Juyawa yayi zuwa cikin gidanjen nasu da ake kira da one milleum quaters anan ne kuma suka hadu da Meabe din wace ta taba fada mai zamanta a nan na dan lokacine ta kusa kammala ginanta da zata koma cikinsa very son. Dutse biyu a lokaci daya zancen wanan kafiran zai tsaya nazari ko zancen da Saiba ta kirashi dashi zai tsaya duba fadawa yayi kan kujera tare da tallabo kanshi yana lumshe ido. Dolene yaje gida ba zai kira kowa ba don ba zai fahinci gaskiyan meya faru ba gara yaje da kansa ya ganowa idonsa haka kuma duk wace ya kama da laifi akan mahaifiyarsa zaiyi mumunan sabawa maishi don ya fada masu wanan duk sun sani kuma. Ba mama Dubu ba har iya da kawu dauda suna da kwakwaran kashedi ga duk iyayyen nasa daya kafa masu don bai yuyu a garesa su wullakanta mashi iyayyensa shi bai wullakanta nasu ba. Haka yake murzan goshinsa da hannuwanshi yana jin wani iri kasan zuciyarshi zancensu da Meambe na dawo mai akai sam ba zai taba yarda ya jefa kansa cikin halaka ba. Mafi yawan masu kudinnan na kabilu kudinsu kudin tsafine don haka shikan ba zaiso abinda zai tabfba martaban gidansu ba. Gara ya dogara da dan juya kudinsu da yakeyi tunda ko wanan akwai daukaka a cikinsa yana tsoro matuka da wanan shawaran da Meambe ta kawomashi. Da haka washegari ya dauki hanyar gida tunda safe yabar lagos din don baijin zai iya daukan lokaci baije gida yasan abindake faruwa ba. Karon farko ke nan daya tsani halaiyar matan nasa da irin fitinansu da suka kasa kwantar da hankalisu su zauna lafiya a tsakaninsu. Tsuki yaja yana mai ganin laifinsu duk kansu amma na Asmau yafi don me zata canza halinta daya santa dashi akanshi. Yasan Nusaiba zata iya jan fitinan da sai Asmau din takai ga tankawa amma meye a ciki idan ta shareta tayi haukanta tagama yarasa Saiba wace irin yarinyace mara jin magana haka wai ? Hanya ya tsaya ya sai doya manja jan garin kwaki domin iya dake sonshi sosai saura a can gida yake saya idan yaje wanan ne kawai yake saya a hanya don yafi sauki da kyau a nan yake tsayawa ya saya. Baiga Zaria ba duk uban sammakon daya buga sai wajajen karfe tara na dare ya shigo garin zaria kai tsaye gida ya dosa don dare yayi baijin kuma mama tana tudun wanda a lokacin yafi kyautata zaton dai tana gidansu yanzu haka . Haka shima Abubakar sunyi waya da mama take shadai mashi cewa tana unguwarsu wajen iya don haka shima kai tsaye a can motarshi ya saukeshi da kayanshi ga baki daya daya sayo Sahabi yana ta mashi sheri akan kayan bai kulashi ba. Saibace ya sama wajen part dinsu tana waya kala batace dashi ba shima kuma bai kula da ita ba haka yayi ta jidan kayashi yana kaiwa kofan iya da sukr ciki part din da yarta mama basu sanda isowarshi ba har yagama jido kayan daga waje cikin wahala ya shigo dasu lokacin ya koma ya kwankwasa kofan iya din . Mama Dubu ce ta bude kofan tana ganin danta ta dan murmusa tana fadin ikon Allah kun karaso ke nan sannuku da hanya. Daga ciki iya ke tambayan waye tace habu be Allah ya dawo dashi lafiya tasowa iya tayi tana fadin da daren nan kuke tafe haka Bukar sannunku da hanya . Karasa fitowa mama dubu tayi tana fadin a,a kaya haka ka zo dasu haka Habu kuma duk bamuji shigowanka ba sannu da zuwa ta duka ta fara tayashi kwasan kayan zuwa cikin falonsu iya din. Saida aka gama kwasan kayan kaf mama ta nufi wajen dan karamin fridge tana daukowa dan nata ruwan leda karba yayi yana fadin bari naje nayi wanka mama indawo. Ya fada tare da juyawa bai tsaya sauraren iya dake fadin ka zauna kaci abinci kafin kaje wanka mutum sai kace agwagwa da son wanka dai juyowa yayi ya dubeta ba tare daya tsaya magana ba ya fice. Yana jin yadda Saiba ta kure kida a gefen part dinta zakice wani sha,anin buki ake a wajanta alkawari yayiwa kansa zai kawar da ido daga duk wani abinda matan yayan nasa zasuyi a gidan. Don haka bai tsaya kulata ba ya bude part dinsu dashi da kaninsu dake boarding school anan suke da dakunoninsu don sunbar can cikin gidan nasu yanzu tun bayan da yayan nasu yai aure. Yafito dogon rigan jallabiyansa ya zura a jikinsa ya shimfida sallayan sa ya tada sallah saida ya idarne ya kula da gyaran dakin da akayi wanda yasan ba aikin kowa bane sai mama Allah sarki mama ya fada yana lumshe ido. Can yaji sautin buga kofa hakan yasa ya saurara da kyau ba karya kunnuwansa ke masa ba don ko nan din ake duka hakan yasa ya mike yana duban wayansa dake hannunsa. Karfe goma saura na dare a lokacin don haka ya nufi get din kai tsaye daga ciki yake tambayan waye . Aka bashi amsa da Jafar bude min get hakan yasa ya leka yana mamakin yadda akayi yayan nasa yayi tafiyan dare haka tun daga lagos. Saida ya tabbatar daya shiga da motan ya mayar da kofan ya rufo ya saka kwado dan basu da maigadi a lokacin karasawa yayi wajen motan yayan nasa yana mashi sannu da zuwa. Motar ya bude ya fito yana amsawa kafin ya daga kai ya kalli part din nasa da kida ke faman tashi yana fadin wanan kuma me suka samu haka yau ?