← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 306

Sashe 47

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

idan ta banye kanta. Port,harcourt rivers state ya J ne ya gama shirinsa na tafiya ma,aikatar da zaiyi singnig don kayansu su samu shigowa arewa a cikin wanan watan. Don sun gama duk wani proces din da akeyi dashi da maigidansa yana shiga wajen yana kiyasta irin dukiyan dake kasan nan ta Nageria da Allah ya bamu. Amma dan arewa yana zaune a cikin kunci yake rayuwansa zai iya rantsewa a wajan nan ba wani bahaushe saishi kadai duk da suna bat da kama da irin shigar mutanen wajen a yanzu. Don shine ba zai rantse da hakan ba a lokacin a madakatar da zai sadaka da wajen da za a sakama hannu din ya samu mutane birjit dake jiran su gana da babban mutumin . Wanda kowa da laluran daya kawoshi wajen bai dade da zama ba wani ya fito daga office din yana kiran sunan company nasu hakan yasa ya mike don ba wanan ne zuwansa na farko ba. Mutumin dake zaune a barin hangunsane ya bishi da kallon mamaki don a iya saninsa baisan mr Okah da wanan mutumin daya canjesa ba a baya. Wanda a yanzu shima yazo ganawa da wanan mutumin ne ta yadda zai samu ya dan jona ya fara business din don abubuwa da suke kokarin tsaya masa a yanzu din tun bayan barinsa wajen mr Okah da abayansa yake yana ci yanasha yana duk wani biyan bukatansa cikin mutunci har duniya ta sanda shi a lokacin. Saidaga baya da ya yaudareshi ta hanyar cuta mr Okah din ya watsar dashi na har abada da a yanzu bai aikin komai kuma sai dan buga buga don ya kare mutuncin kansa. Lalai babu tamtama wanan yaron mr Okah ya aza a matsayinsa na baya amma wanan yarone sosai anya kuwa tunanensa ya zo a gaskiya yasan halin mr Okah da kyau kamar yunwar cikinsa fa ? Mr Okah mutum ne da zai sakar maka dukiya kayi komai a kai kamar bai damu dasu ba sai ranan daya bukaci sanin kan dukiyan zai waiwayeka akansu. Wanan karon ma haka yaiwa Jafar din da kanwarsa tillo daya ta gabatar mai dashi kuma ya yaba sosai da hankalin yaron da baiwansa bai taba tsamanin zai samu yaro karami haka da zai rike wanan amanan da zuciya daya ba don yaron akwai basira da hazaka ga zafin nema. Haka hasken taurarinsu yazo daya kusan ma yace na yaron yana gab da taushe nasa yadda masana suka fada mai akan yaron. A bangaren jafar din kuma dashi da kaninsa Abubakar suke tsaye sai yan uwasa biyu daya yaba da halaiyansu sune suke gudanar da wanan sana,an dayanzu darajan gidansu ya soma farfafowa. Irin jajircewan Jafar din da taka tsantsan akan dukiyan mutane yasa idonsa yana kan komai yasan shige da ficen da yan uwan nasa sukeyi da dukiyan bai yarda ya shagala a kan dukiyam mutane ba yana hasaso masu jin dadinsu gaba. Har kawu dauda ya dora a wanan harkallan a yanzu a wasu jahohin dake kusa da kaduna din shima sai tubarkallah a yanzu. Nace ashe da zamu samu irin jafar goma a arewa ba za a barmu a baya ba indai dan uwa zai samu ya tunane saura azo aci tare a tsira tare da mun rage raddin talauci a nahiyar nan ta arewa. Saidai mutane a yanzu kansu suka sani sai iyalinsu mutum bai tunane zai iya mutuwa ako yaushe yabar baya da Kura ga magadansa. Har jafar din ya fito wanan kafirin yana zaune yana jijiga kansa a wajen ya fice abinsa ba zaka taba daukan wani abu maimuhinmanci yayi ba a lokacin. Jafar mutum ne daya bude ido da neman kudi tun yana karami suna bin mahaifinsu kasuwa suna ganin yadda ake harkan kasuwanci da har yazp kuma kawu dauda ya kara dorashi kan wata sana,an . Hakan baisa yayi sake da karatunshi ba don har masters yayi saboda daman da yake dashi na magani a ganan yaron don ga tushen ilimin a cikin garinsu. Hankalinsa yana kan tukin da yakeyi duk da a yan kwanakin hankalinsa gaba daya ya koma gida saboda azumi dake karatowa yaso a satin nan yashiga arewa saidai hakan ba zai samu a wajensa ba don kayan su dabasu daga daga kudun ba har lokacin. Wanan yasa bai samu shiga gida ba sai dole an fara azumi badashi ba ke nan hakan yasa ya jawo wayanshi ya soma kiran layin mahaifiyarsu dan yaji ya za ayi ke nan ? Tana dauka yaji muryanta da alaman ba lafiya ko barci kuma ta tashi a lokacin hakan yasa hankali tashe yake fadin lafiya dai mama ? Dan murmushin dole mama din ta kakaro a fuskanta kamar yana gabanta take fadin ba komai jafar yau dai na kwana da dan ciwon kaine kawai amma da sauki. Kina asibitin ne tace a,a gamu gida iya da matar kawunkune can da ita yau mun dawo gida mu dan huta muryoyin mu yaji a lokacin yace taba saratu waya take fadin bata kusa tana can wajenka. Salimace da Rahaam suke magana yace ta bashi salima din nan ta karbi wayan tana gaidashi ya amsa yake tambayanta idan ciwon mama din sosai ne don yasan ba zata fada mashi gaskiya ba ita. Gaskiya tun jiya take kwance da muka sameta asibiti amma dai kuma yau da sauki tunda tasha magani fada ya fara yana fadin shine baku kirani kun fada min ba salima ? Me saratu takeyi can bayan mama na nan kwance bata masan halin da take ciki ba yanzu zan turo Lawal yazo ya gani idan zai kaita asibitine ? Hakan yasa ya fasa fadan zancen da yake sonyi da mama din a lokacin ba a dauki lokaci ba mukaji sallaman lawal din yazo duba mama din da jiki . Abokinsa ne nasanshi sosai yana yawan zuwa gidan idan yana gari wajensa haka kuma sukanyi tafiya tare indai yana arewa. Shiya shigo ya dubata har sukai dan hira da mama din duk da ina kitchen ina hada girkin sara lokacin amma ina jiyo hiransu daga kitchen din. Ya fita bai jima ba ya dawo tare da wani ma,aikacin jinya ya dubata ya bata maganunuwan da zata sha a raina nace gata ke nan mai karami shike da babba akace. Anty yanda muke sa rai a cikin mu yanzu ta nunawa mama damu wanan gatan sai dai karfin mijinta bai kai ba amma duk da hakan Alhamdullahi gaskiya. Abinda yasa nace hakan dole indai da nagarine kai kaga yadda iyalan mama suke gudanar da rayuwansu dole abin ya baka sha,awa. Don ko ya Habu saida ya kira yana fadin zai taso ta hanashi tace ya zauna yayi abinda ke gabanshi ita lafiyanta kalau Jafar daine ya tayar da hankalinsa. Shima ya Salis ya kira cikin damuwa donshi yanzu yana ghana yana karatune daga can kuma ya kira yana gaida ita da jiki me zai hana bakaji sha,awan hakan ba yadda diya keba uwarsu kula. Bansan ya akayi ba saiga matan yaya din har saare sun shigo suna fadin mama ashe bakiji dadi ba yau yanzu sweet j yakira yake fada muna. Aina fada mai ni zaune nabar mama tana banyewa maman su Raamah kai da za aiwa kitso fadan hakan yasa na kalleta don nasan mahaifiyar mu zataji nauyin hakan data fada. Sun dai dan jima kafin su fice daga part din lokacin har na hada komai da za akai asibitin na shiga wanka don nice zanje nakai masu abincin .
Chapter 47 · 0% Book details