← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 306

Sashe 152

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

muje wajen yandan ki Anty Salima ta fada na dan kalleta ta mike tsaye tana fadin muje ai yanzu tabar wajan nan itama duk muna nan zaune. Bata dakin da alama tashiga bandakine dataji shigowan mu muka fito bamu tsaya jiranta part din muka fice zuwana yar uwata dana matsu muyi arba da ita a lokacin don a yanzu nasan tasan munshigo gidan tunda munyi waya kafin na fito gida. Wanda a yanzu zaune take kawai gidan bata wani dogon hurda da kowa sai salima da iya dama dai kusan hakan ake zaune saidai na yanzu din yafi worse ne kawai saidai haihuwan nan na Asmau tace dani ta danga canji ga Asmau don data shiga barka Asmau ta mata bazata don ta mika mata yaron wai ta shafa mai man zaitun donta samu an mashi wanka lokacin. Iyace dai mai wankan yaran idan sun haihu dama ba wata ake daukowa ba tunda da dan karfin ta har yanxzu shine tana shiga iyan ta gamawa yaro wanka tace a ba Yanda din tayiwa yaron shiri ita kuma tashiga nata wankan. Wanda bata zaci hakan ba tunda da farko duk sun dauki zafi a kanta kan zancen aure masu miji dani yar uwarta nayi a cewansu asirine mukai mashi muka sameshi haka a bagas din. Koda muka shiga ashe Saiban na tsaye ta windon dakinta don shike facing din part din yanda din tana kallon mu zaune takai saman gado ta jawo waya ta dannawa yar uwarta ikilima kira. Tana dagawa tace Saiba ya akayi yazo din anyi magana tace anty ikilima inafa ya dai zo da wanan yar iskan yarinyar tayi barka. Anty Iklima kinga yadda yarinyar nan ta koma kuwa cikin dan kwana biyun nan wallahi koke kika ganta sai kince ba ita bace Ramaah da kika sani a baya. Takoma sak irin manyan matan nan da yake korafin son yaga mun koma da kullum yake fada yana son ganin hakan a kan mu. Mena fada maki Saiba ai dama nace kibar biyewa Asmau kuna wanan rayuwan kidadancin kamar wasu jakuna kinki ji ? Yanzu gashi dan hakin da kuka raina na nema ta tsone maku ido keda bakinki kin fada ko wanan baisa ya fita batunku ya baku baya tunda abinda yake so ke nan dama ? Tundai ke kice baki da aiki sai cusa mai bakin ciki ance ga yadda zakiyi ki tsaya kina takama da kin gama dashi bai iya komai sai abinda kikace dashi ? To yanzu kin gani masu iya magana sunce ko kana da kyau ka kara da wanka kin dai san Jafar yayi kokarin zama daku haka Nusaiba ku zauna yayi takashe maku kudi amma a banza baki amfani dashi saidai ki sayar ko ki kimshesu cikin akwati tun farko abinda inna take maki gudu ke nan amma baki ji Nusaiba ai yanzu kin gani. Anty Ikilima nagaji da zuwa gidan malam nan wallahi bani ganin biyan bukata gaba daya yanzu abubuwan sun juye min yadda ban tsamani ba sam inayi kamar banayi wallahi don banko gabanshi balle na samu aiwatar da abubuwan dana karbo din. Ki bari ai zan shigo ana gobe suna kuma naji inna tace zasu zo barka kinga nasan zata zauna dashi ai donshine ma bazan biyosu ba don ina son inzo in kwana din idan nazo sai musan yadda zamu bullowa zancen nasa. Sun dauki lokaci suna waya kafin dai ta taushi yar uwar nata ta bata shawaran da ita saiban take ganin yana da wuya ta iya hakan ga jafar din da take gani idan ta sameshi yanzu saita hukuntashi fiye da tsamaninta. Zai gane shayi ruwane idan ya shiga hannunta saita bashi mamaki sosai ta rama duk wani takaicinshi dake zuciyarta abugeka a hanaka kuka shine abinda jafar yai mata a yanzu kan Rahama. Muna shiga maria na zaune tana ba Abba abinci tun daga kofa nace da yaron baby na ya juyo da sauri yana kallona sai yai kamar zai dago zuwa gareni sai kuma ya noke zuwa jikin mamanshi yaki zuwa wajena din. Wai Ramaah kece haka abinda Maria din ta fada ke nan tana min kallon mamaki na dan bata rai ina fadin kinga duk na lalace ko ? Ta watsa min harara tana fadin wani lalacewa kuma gaba daya kin sauya kamar bake ba ummah nacan tana damuwa akanki kullum sai tayi min magana a kanki wai naki zuwa in duba matake . Ni kuma ya Habu ya hanani zuwa gidan duk sun sakani a gaba kan maganan ki na karasa ina fadin to ai gani nazo yau muka fara gaisawa da ita lokacin Nafisa ta shigo part din tana dariya tace. Wai ashe bakuga saiba ba da kuka shiga yanzu ta fito tana fada dake Salima wai zakuyi tsiya idan kina shiga huruminta dolene saita gaisa da yarinyar nan da zaki kwasheta zuwa dakinta ? Allah sarki shi gaisuwan ma wani fitinane ashe banzata haka bane da bance muje a gaisa ba ai ? Mun bar zancenta aka dauko hiran anty baraka data dagawa mutane hankali tunda safe wai tun cikin dare ta kira waya ashe zata dawo gida ita mama dubu ta hanata dawowa dagani har yar uwata bamu ce kala ba don ba abinda ya shafemu bane . Muna zaune kanwar Asmau matar yaya J tashigo tana fadin amarya angonki yana neman kifa ? Wai ashe suna zaune falon gaba dayansu ya fito yake fadin ina Rahama ? Sukai shiru ya bisu da kallo kafin yace ke Rashida kira min ita part din habu don Allah ya juya ya koma dakin nasa shine ta taso tazo kirana din . Jiki a sabule na mike cike da mamakin don me zai aiko nemana a wanan lokacin gidan matanshi irin hakan zai iya kawo wani matsala kuma tunda dai gidansune na shigo ai ba nan din nake ba. Namiji oho donshi ko a jikinshi a dole zai saka mata kunci a zuciya ya nuna hakan ba komai bane ai tunda nima hakinsace na karasa falon na shiga gabana sai faduwa yakeyi suna zaune ana surutu sai sukai tsit lokaci guda. Yana ciki Rashida din ta kara fada na nufi hanyan dakin nashi da sallamata yana kwance yana waya na sameshi ya dago yana fadin. Kije wajen Iya ki dubo min abincin da kikazo masu dashi din nan yunwa nake ji zuwan kawu dazun ya hana in tsaya in karya da kyau a gida. Na juya zan fito muka hade da saiba da zata shiga fuskanta kawai na kalla nasan akwai magana a tare da ita lokacin. Ni dai kala bance da ita ba na dan rabe ta shiga ni kuma na fito daga dakin yan falon ko na samesu sunyi tsit sun kashe kunnuwa suna sauraren abinda zai faru a lokacin. Part din iyan naje na samu har lokacin dai ba dadi a yanayin dana samu mama din don itama waya takeyi lokacin don haka da iya na samu yin magana ina fada mata sakonshi din. Iya ke fadin shi kuma jafaru baici a gidan bane da zai kwashe muna wanda aka kawo muna nace kadan zan dibar mai ai iya. Na bude na kyafata mai komai na rufe ina jin Saratu na fadin bari dai in diba kafin ya kare naga an fara kwashewa haka kowa baici ba. Kai wanan matar bata san harara ba ban taba kawowa a raina zata ko kalli abinda na daho din ba balle tayi fadan taci har nakai kofa naji mama na fadin idan kinje ki kira min shi daga nan ana magana ya mike ya fita ni zasu bari da tashin hankalin da baraka ke son ta dauko muna akan mijinta ? Tunda na doshi kofan nake jin muryansu daga dakin hakan yasa naja na tsaya naji yana fadin har ke kin isa ki kafa min doka a gida Nusaiba ? Na fada na kara Rahama matatace kamar yadda na auri kowa a cikinku tana da ikon shiga duk inda taga dama a cikin gidan nan ko da kudinki na hada na gina gidan nan ne ? Nace ki koma gidan ku kince ba zaki koma ba to ki zauna tunda zaman mama kikeyi bazan koreki ba don kin zauna zamanta amma kada kice zaki takurawa kowa a gidan nan cikin iyalina kinji na fada maki . Kikace zaki tayar min da fita a yanzun nan ba sai anjima zan shayar dake mamaki cikin gidan nan oho ashe ba dadi lokacin da kika zarga min ciwon fitana a kaina ita kuma sakaran nan ta mara maki baya kuke gudana. Don yanzu na samu wace bata gudana tana iya zama dani ko wani hali nake ciki zaki kuma ce baki yarda da hakan ba kije nace ki samu mai lafiya irin ki don Allah ki barni in huta hakana a rayuwata. Dakin na fada dauke da abincin ta zaburo kamar zatayo kaina na gwauce Allah ya gyara abincin bai zube ba har na falon duk suka mike tsaye saboda muryan yaya dake fadin kika taba ta wajen nan yau sai kin kwana asibiti Nusaiba na fada maki inkon zata karyane ki gwada taba Rahama ki gani a gidan nan. Ni basai ka rama min na ina da hannuna nice zan ramawa kaina ai amma wanan abin baikawo kallo ba a tsakanin ku a cikin jama,a don Allah . Kaje mama tana magana da kai idan ka gama na fada na aje abincin na fito daga dakin na barsu a ciki yan falon tsuru tsuru ban tsaya ba na fita daga part din.
Chapter 152 · 0% Book details