← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 306

Sashe 114

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kanshi ya kadu iya kaduwa da ganin irin riban daya samu a wanan harkan ta ma,adanai daya soma tare da Maibei . Da farko yaki shawaran nata kamar dole tayi mai kan wanan halakan bayan dogon bayanin yadda abin zai kasace a tsakaninsu. Maibei tasoshi da arziki a rayuwansu ta kawo mai boyayyen sana,a damu yan arewa bamu faye daukanshi da muhinmanci ba a nan. Sai gashi shiga farko da kayansu yayi yaga ya samu abinda lissafin kan mutum ba zai iya kwatantawa ba wai duk a sunan riba. Ranan daya kira Meirbe yana sanar da ita irin yadda kayan suka samu karbuwa cewa tayi dashi ai dama na fada ma saidai ka zama boss ba zaka kara zama a karkashin wani ba idan har ka gane wanan sana,an. Ta fita da ma,adaine akwai wuya akwai hadari a ciki saidai amfaninsa yafi ga mutum yayi mata godiya suka kashe waya. Bayan satine ya kirata kuma again bayan sun gaisa yake fada mata ya gama komai yana son ya dan dawo Nageria saboda family dinshi. Take fadin haba dai family ai donsu ake neman kudin nan sunsan kana wajen neman kudi me zaisa ka damu ? Kinsan ina da mama kuma ina da yan uwa meaibe haka kuma matana a ysnzu ukku nayi sabon aure ina gab da tafiyan nan yanzu haka amaryan nawa ta tare a gidana ban gari. What kai at your age kamarka ke da mata ukku gentle man haba haba ina zaka kai mata ukku a rayuwan ka me kake so ga mata hakane ? Dariya ya kwashe dashi tace wait woo are you kidding me in wasa kakeyi ka bari please ina aure dai mutum ya samu mace daya is ok for him sai su haihu tare su dubi yaransu ? You know iam muslim my religion accept this for me our prophet comand us to marry four wives if posible for a man and there is special reward for doing that in islam . If you can feed them give them a shelter and cloth them and all there needs katseshi tayi da fadin is that all you can give a woman my friend stop telling me this ? Wai har kana fadin kayi sabon aure for where my friend wace mace zata yarda ka aureta kana wani duniyan ka barta a gida ? Iam telling you wallahi ni angone nayi aure kafin na bar Nageria kalman wallahin da taji ya ambata da suka san musulmin kwarai bai wasa dashi yasata fadin . Eeee way are you serious my friend ya kara furta wallahi i marry a young fulani girl but she is schooling now in A B U zaria ,,,,,, Ta sake katseshi da fadin so you are serious friend who is dis lucky girl that charm you heart ? Tayi sa,a data sameka a matsayin miji a rayuwanta duk da ka bata mata tsari don nasan ba zataso ta zauna a cikin mata haka da yawa ba tana educated ? Dariya yayi yana fadin mu a wajen mu musulmai wanan ba matsala bane don haka muka taso muka gani ga iyayyen mu. Sun dan jima suna hira kafin suyi sallama da juna akan zai kara kiranta idan tafiyan nasa zai yuyu a lokacin kamar yadda yake so. Bayan sun gama waya ya zauna yana tunanen zantutukan da sukayi da ita din haka dinne gaskiya akwai tauyewa a cikin lamarin wani lokaci amma zai iya kokarinsa wajen ganin bai tauyewa kowa hakkinsa ba. Yau da ace baida zarahin hakan ya kumayi hakan yasan akwai tauyewa sosai a cikin lamarin yadda zai daukota ya jefa cikin matansa da kansu har yanzu basu bari ba balle a dauko wata a hadusu zama a waje daya. Matan dakowa nasa baida mutunci a idonsu kowa suna masa kallon bai isa ba har dai Saiba daya dauko wace bai gama sanin halinta ba ta yaudareshi ta hanyar abokinsa. Wai kuma yanzu itace mama take nunawa goyon baya don saboda Saratu kome shiya rasa abinda ya rufewa mama ido har take masa wanan mumunan fahintar ayanzu. A iya saninsa ya taso cikin yiwa mahaifansa biyayya tun mahaifinsu yana raye har zuwa kawu da suka dauka mutum na uku mafi daraja a idanusu. Amma yau sai gashi an wayi gari duk hakan na kokarin ya tafi a banza wajen mama tunda har take iya zarginsa akan kudin da bai taka kara ya karye ba. Ya dan murmusa ya gyara zama don tuno ko dai saboda Rahamane har kiyayyanta da mama ya shafeshi haka amma a iya saninsa ai mama bata taba nuna bata kaunar yarinyar nan ba a gabansa. Don ko dan zaman jinyasa da sukayi ya fahinci kamar akwai kyakyawan halaka sosai tsakanin yarinyar da mama don yadda take yabonta a gabanshi yana daya daga cikin abinda ya kwadaita mashi yarinyar ta kasance daya daga cikin iyalinsa don ita mama din data nuna hakan . Sai gashi kuma abinda bai taba zato bane ko tsamani yake fitowa daga mama din yasan sun taso mahaifiyarsu na matukar sonsu a rayuwansu. Mama irin mahaifan nan ne da keda rayuwan da ran yaronsu ya baci gara nasu ya baci sau dubu a wuni. Haka kuma akan danta zata iya yin komai yasan da wanan don haka dole akwai wani abinda ya faru da baisan dashi ba game da mama din. Koma meye tunda har ba laifi yayi ba kawai don ya auri Rahama zaisa mama ta nemi tozartashi haka a idon duniya ? Zaije gidan zai yi kokarin ganin ba a kai ga samun matsala ba tsakanin shi da mama din ko yan uwan nasa in sha Allahu yasan wajen matsala gudane sai yayi da gaske akan matanshi don ko bai samu matsala da Asmau ba dolene zai samu da Nusaiba. Sau daya ya daga wayanta kafin ya baro Nageria irin ashar din data dinga mai tace zatayi a gabanshi yasan ba zai lamunci hakan ba gaskiya. Koma meye yana rokon Allah ubangiji ya kawo mai sauki akan komai ko wani bangare magana dayace a yanzu itace dole ya jajirce ya kara zama namijin gaske ako wani fanni. Yajima zaune yana zancen zuci har tsawon wani lokaci kafin ya mike zuwa ciki don ya watsa ruwa a jikinshi yana son fita da yamman zuwa wani waje. ZARIA Tun bayan tafiyan su anty salma gidan yai shiru duk da Nafisa da Salma suna gidan amma suna daki suna barci kasa kwanciya nayi na fito na gyara ko ina na gidan sai kusan azahar suka tashi banga laifinsu ba tunda akwai gajiya a lokacin koni ban samun sukuni idan ba naga waje da tsabta ba haka yasa na kasa kwanciya na gyaro ko ina . Wanka nayi tare da sallah na saka wani atamfa saiki rantse abayane rede made dinkin ya hadu sosai gashi kayan sun matukar karban jikina. Kalansu yayi min kyau sosai dama tasan hakan yasa komai ta zabo min abinda nafiso don sai incema na zabo a cikin rashin sanin cewa nice mai kayan a lokacin. Ban fito daga daki ba duk da ina jin muryoyinsu a falon sun kuna tv kuma suna hira saida nayi sallah la,asar Nafisace ta lekoni taga ina sallah take fadin har la,asar yayi ashe muna nan zaune. Bayan mun fitone na gabatar masu da dan dabaran da nayi muna don kada mu zauna da yunwa duk da ban tsamanin hakan akwai abubuwan da zamu iya ci a lokacin. Tunda ns fito naji salima tana fadin wai kan uban nan wai Ramaah ko dama course aka kaiki yine Abuja ? Nifa gaba daya wallahi kin sauya min sai nake kallonki kamar bake ba Allah tun jiya duk kin sauya min ga sanin da nayi maki ga baki daya kin juye kin zamo min wata ta daban. Dan murmushi nayi ina fadin kai anty salima wani irin sauyawa kuma don Allah ni din daice Rahaman da kika sani a idonki. Gaskiya akwai drama wallahi na yarda da ake fasin akwai wani rahama a cikin aure da sai wanda yayi yake fahintar hakan. Na duka na bude abincin dana aje a gabansu suka dago suna fadin meye wanan abincine na basu amsa. Salima dake kishingide ta kalleni tana fadin yaushe kikai wanan aikin Ramaah nace kuna barci tace wai yadda na gajin nan nima nasan nayi barci sosai wallahi. Tun shekaran jiya da ya Habu ya kiramu wallahi bamu huta ba muna tsaye ai dole mutum ya gaji don ma gidan anty Ai muke akwai yan mata a gidan da suka tayamu aikin . Wallahi naji dadin kai aikin nan da akayi gidan anty Ai ai kinga yadda take farin ciki kuwa sai kiran abokan arzikinta takeyi tana sheda masu abin arziki ya sameta. Da kikace ta bar komai daya rage a wajenta idonta kamar zatayi kuka a lokacin tama rasa me zatace a lokacin don mamaki Nafisa ke fadan hakan. Nafisa anty Ai mutum ce fa tafi mun su anty yar malam sau dubu wallahi baki taba jin zance ya tashi ace da anty Ai a cikin zance. Nima ai hakan yasa naji dadi da kika fada a cikin gida cewa yaya yace gidan anty Ai za ai komai har baki su wuce. Wai baki ji sakaran nan Saiba ba da nake fadawa iya tana tsaye sai cewa tayi wai dama ita ya dace aje can tunda taronna yan kauyene ai. Kuci abincin mana na fada ganin sun bar abincin a bude yana sanyi a lokacin saidai hakan bai hannusu hiran ba sukaci gaba da hiran yadda Saiba tayi ta iya shege tana cika baki. Salima ta kare da fadin saiga shegiya tayi lakwas dataga karyan bariki baki ya mutu ance bayan zuwan mu nan ai bala,i tasa don wallahi yaya yayiwa kowa bazata ga auren nan. Gaba daya ya nunke kowa a baibai don bai bari kowa ya fahinci komai ba su matar kawu ba a samu kafan iya shege ba wanan karon da bukin maria yaya habu matar nan tayi iskanci sosai wallahi. Ta hana komai karshe ta kwashe takai gidanta sukai ta amfani dashi muguwa kawai ni wallahi nasan itace ke kara yiwa mama fanfo akan komai. Itama mama ni har mamakin yadda ta sauya nakeyi ni yanzu har tsoro nake ji idan mun
Chapter 114 · 0% Book details