← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 306

Sashe 59

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallah nayi na kwanta saboda gajiya a dakin da anty Salma ta kaini don bamu ko zauna munyi wani hira da ita ba a lokacin saboda gajiya. Sallah la,asar ya tayar dani na falka kinsan hakan baiwane ga musulmai da zaran lokacin ibada yayi in barci kikeyi sai kin falka saidai shedan yayi kokarin rinjayanki ki koma barcin. Hakama idan idon ki biyu da zaran lokacin nan yayi sallah ce zata fado maki a rai musulmi na kwarai duk abinda yakeyi a rayuwa sallah tana a zuciyarshi hakan aka san musulmin kwarai dashi. Nima irin hakan yake kasancewa dani komai nauyi barci zan falka a daidai lokacin ko lokaci ya dan gwauta kadan in tashi in gaida ubangiji subbahanahu wata,alah. Bayan na idar da sallah ina zaune na jawo wanan karamin ledan da yaya ya miko min a hannuna lokacin da zan fita motan shi daya kawoni. Na fara budewa kudi yan dubu daya sabbi,fill dinsu duk daba nauyi kudi na sani ba a lokacin balle na kiyastasu nasan wanan yafi karfina a lokacin. Sai wasu sarkoki da bangus da yan kunne guda biyu bangus biyu masu kyau ga kudinsu nan a manne jikinsu ga yar takardan da akaiwa rubutu ja. Mamakine fal a fuskana na dalilin sayan kayan nan duk da nasan shi mutum mai alherine dama mutane na fadi ina ji uwarsu kuma ko yaushe tanawa abinta kirari wajen alheri kullum ina ji. Ban kara girgiza ba saidana mike da sauri na fara budan suran ledan gabana nafaduwa nake zaro dogayen riguna masu kyau da daukan hankali guda ukku ko wani da gyalensa a ledansa. Tsorone fal ya dira min a zuciyata mu fulani mukance alherin namiji gareka nuna alaman sone ko kauna sai wanda ka damu dashi kajin lamarinsaa zuciya kakewa alherin bajinta irin haka ? A take wani gefe ya gargadeni da ke wawiya wani so yaya Jafar nefa ina so zai shigo tsakanin ku kuma yadai nuna ke kanwarsace yasa ya saya minsu. Ko kuma don zancen da sukayi na cewa abinda matansa sukai min yake kokarin wanke min zuciya sai gashj nafi amincewa da wanan na karshen wanda kuma haka dinne ko a wajensa. Don yaya Jafar nauyi da kunyana ya dinga ji na abin daya faru yana sane kuma nima abin yayi matukar tabamin zuciya hakan yasa na tsame kaina ga lamarin kowa a gidan. Karshema sai gashi na yanke shawaran in dawo Abuja inzo inyi sallah wanda yaga sakacin dan uwansa Habu daya yarda nazo abuja din idan shine haka ya faru ba zai bari naje ko ina ba zai tsaya ya tura masu haushin abinda suka aikata wanda sai sunyi dasun sanin hakan da sukai min a lokacin. Koda muke tafe hanya yana da takaicin Saiba amma kuma yana sake saken ta yaya zai dan farauta min ba tare dana rikesu ba a zuciyana don cin fuska bai da dadi ga mutum irin haka balle ga yaro karami. Shine yana jin banda waya yaga rashin dacewan hakan gara ina da waya a hannuna aji halinda nake ciki a nan yayi shawaran saya min waya din sai ya ga wa yanan kayan kuma ya hado min dasu. Yarinyar ba laifi gaskiya tana da dadin zama ga tsabta ga ladabi ga hsanin ya kamata bata da hayaniya ko daukan magana duk abinda matansa keyi bai taba jin yaran sun tsaya sun mayar masu da martani ba koda agabansu akai abin. Hakan yasa yake ganin girma da kimar sarakuwar tashi da kanwata duban irin simple rayuwan yaran yakan burgeshi wallahi tundai tsabtansu da wanan yakewa matasa gori wanda sukuma suke kara jin kiyayyan yaran a zuciyarsu. Haka ya kama hanya bayan ya saukeni tare damamakin wani irin halakace tsakanina da mutanen nan haka ? Don da ganin gidan ba gidan karamin mutum bane dole akwai wata halaka mai girma a cikinsa koma meye ya godewa Allah da bai ajeni a wullakace ba. Gara da Allah ya bashi dubara danyi min sayayyan nan da yayi don a ganni a cikin mutuncina da kima ba zaiji dadi su ganni cikin irin suturan da habu ya barni ina sakawa duk dai da baisan daliliba amma dai babu wadatuwa gareni gaskiya. Yasan haka halin dan uwanshi yake tun suna kananunsu habu bai damu da wani rigimar duniya ba kan shima bai fitar da kanshi kunya balle wani. Wayanshi dake karane ya katseshi ya dauko yana duba dan uwan nasa da yake tunanene ya kirashi yana mashi ya hanya ? Alhamdullahi Habu na sauketa tun dazu na saya mata waya don ta rike don nace ta kira idan da matsala tace bata da waya a hannunta. Why habu zaka kasa saiwa yarinyar nan dan waya koda karamace da zata rika meyasa kake hakane wai ? Yaran nan kaika daukosu a karkashinka suke a gidan nan da anga kana darajasu da ba macen da zata nemi tozarta makasu a cikinsu. Bai kamata irin hakan na faruwa ba marayune fa Habu kasan yawan ladan da zaka samu a wanan taimakon da kayi gaskiya banji dadin hakan ba wallahi na dai saya mata da wasu kaya tunda banyi tsamanin ta samu dinkin wa yancan ba da zata saka. Shiru Habu yayi yana saurarenshi na dan lokaci saida ya kare magana yake fadin Nusaiba ta kira wayan kane ? Nusaiba wani abubya farune kuma dazun dai da zan fito tazo tana min rubbish akaina ban tsaya kulata ba don bata da hankali nake gani. Bata dashi kan akan ka dauki Rahama yau tashigo wajen su mama tayi tijara iya son ranta katse dan uwan yayi da fadin What ? For what reason zata samu mama to Salima dai bata kyaleta ba itama bata kyale salima din ba sunyi ba dadi a gaban mama wanan yasa na kasa hakkuri na kiraka . Irin wanan abin yana taba mutuncin mahaifiyar mu sosai don bata magana su kuma sunga ko sunyi ba mataki kake dauka ba yasa suke cigaba da hakan tundai ita Nusaiba din. Saiba saiba takai karshena wallahi amma bari laifin mama din ne dake hanani daukan mataki akansu kome sukayi mama tace inyi hakkuri haka mata suke basu da tunane komai girman su zankiraka habu ina zuwa don Allah ya fada a gagauce ya kashe wayan. Me wanan yarinyar take nufi danine wai yana neman layinta data kirashi danzun yana zancen zuci a fili ta dauka ni dan iskane irinta kome yaji ta dauki wayan cikin basarwa tana fadin hello J. Ke Nusaiba yanzun nan ki tafi gidan ku kada ki bari in dawo zaria yau in sameki idan ba haka ba wallahi saina katse duk igiyan dake tsakanina dake a yau din nan ya kashe wayansa yana huci bai jira cewanta ba. ABUJA Ina saka wayan a caji aka shigo na juyo yar aikin antyce wata yar budurwa mai guntun buje da ganin shigarta nagane ita din yar aikice agidan . Abinda basuyi muna ba ke nan a lokacin sam ba a gane cewa mu yan aikinsune kuma ta gargadi mama dake katobaran fadawa mutane hakan. Ranan da hjy taji tayi fada da mama sosai take fadin mu bamu daukeku a yan aiki ba a yan uwa muka daukeku kowa kuma yasan abinda nake fada ke nan don kun zama yan uwa a wajen mu yanzu. Tun wanab lokacin ummah bata sake wanan katobaran ba tana kafa kafa da abinda ke batawa hjy rai akai zama lafiya sosai a tsakanin mu. Wanan yasa na nasa a raina cewa yarinyar nan ta huta indai har anty Salma ta biyu halin hjy mama da yan aikinta zataji dadi sosai a wajensu. A falo na samu anty salma din tana waya alama tayi min da hannu inzo na karasa ta nuno min fuskan wayanta dake hannunta. Fuskan hjy mama a cikin massalaci zaune ga larabawa suna gittaiya mama kinga Ramaah kin yadda ta girma ta zama big girl yanzu. Mama ina wuni Ramaah ta lafiya lau ya kuke yaya yanda da jikinta yaya yan uwanku na amsa da Alhamdullahi. Ya ibada mama tace Alhamdullahi gamu a cikinta aini mamakin ganin yadda Ramaah ta girma nakeyi mama din ta katseta da fadin anyi sallah ki bari zan kira ku anjima. Ta kashe wayan tana fadin yau mama zataji dama ace tana garin nan ta ganki murmushi nayi ina dukar da kaina kasa. Take tambayana ya jikin Yanda da sauki ko babu dai wani matsala dai ko na amsa da taji sauki sosai lafiya na barta jiya muna asibiti tare a can na wuni dasu. Ta koma tambayana karatu nake fada mata nagama secondry school yanzu gaba zaki ko sai nayi murmushi ban bata amsa ba don banda abinda zan fada mata lokacin. Duk da nasan ana zancen zuwana gaba din amma ita ban fada mata komai ba tunda banda tabbaci akan hakan yanzu saidai abinda shawara ya yanke a kai. Tunda su Salima na karatu ni kuma yanzu rikona ya dawo hannun yaya Habu nasan yana da wuya ban je higher institution da nake son zuwa ba. Zamana gidan anty sallama a ranan ya tuna min abubuwa da dama a rayuwana wanda yasa jikina yayi sanyi don tuno da mahaifinmu da zaman Abuja da nayi. Zaria duk yadda Saiba taso ta kira mijin nata yaki daukan waya don yayi blocking dinta a lokacin karshema kashe wayan nasa yayi don mama ta fara kiranshi tana son taka mashi burki. Wanan karon yasha alwashin sai ya koyawa Saiba hankali sai ta gane ita ba kowa bace in ma rabuwace ai a rabu din ya gaji da wanan irin halin nata na rashin kwabo. Bata kara sanin da gaske bane saida ya Habu ya dawo yana fadin yace ta fita gidan kafin ya dawo har in ya dawo ya sameta gidan wallahi kowa yayi mata tsaye yau sai ya raba igiyar auresu ga baki daya. Iya najin hakan tace maza ki tatara ki nufi gidan ku kada kaddara ya zaunar dake yazo ya aikata abinda ya fada zaman ki gidan nan ya kare maki. Babu yadda ta iya don mama tayi shiru batace komai ba a wanan zancen hakan ya kara tunzurata ta shirya kayanta a cikin yar karamar jakka ta nufi kaduna. Ana magariba tana sauka gidansu cikin tashin hankali ba wanda yace mata komai don ta samu
Chapter 59 · 0% Book details