Sashe 280
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tace kada a fada ? Laifine mama don mama tace kada muyi surutu mu tayata da addu,a sai hakan yazama laifi ni naga ai abinda yakamata muyi ke nan mama ta fada. Lalai Barakha dole kishiya ta dinga cin galabanki indai wanan halin naki na saurin yarda da mutanen yanzu kikeyi a can ? Yayace zatace kada ku fada min abu ke har ki yarda kiki fada min don kina bi can sun san halinki ke sokuwace da sauri ta dubi uwar tana fadin ni mama me kuma nayi na sokonci a nan don na fadi gaskiya ? Damu fada maki abinda zai tayar maki da hankali a banza ita saratu na can zaune dakinta ai gara muja bakin mu muyi shiru tunda nan Allah ya nufeta da aure. Wani malolon bakin ciki ya tokare mata makoshi ta kasa ba yar nata amsa don bakin ciki ta mike zuwa dakinta barakha ta dubi mama hafsatu tace wallahi mama kada ki yarda kice komai kada tashiga wani hali su jafar su sakaki gaba a gidan nan. Jin hakan yaba hafsatun tsoro tace ni kingama bari bazo nabar gidan nan yanzu da nace sai yamma zan karasa gida amma yanzu zan wuce. Dubu na shiga daki waya ta jawo ta dannawa saratu kira gidan cike yake don a ranan suke wunin buki tunda amarya ba a gari take ba. Hayaniyane dakin nata sai cewa take bata jin abinda mama din take fada don idon mutane dake kanta a lokacin dakin tap yake da yan uwa da abokan arzikin gidan yan zuwa gani amarya. Gashi duk sun isheta amma ba daman magana yarasu sai hawa saman kujera sukeyi suna takawa iyayyeb da diyan anci shimkafa an wawatsar mata a dakin nata. Dole ta koma kuryan dakinta ta kwanta tana kukan zuci Allah ya gani tana son habibinta don irin mazan nan ne da mata basu dauke ido akansu don kyau. Wanan yasa duk inda yaje ya taya mace yake samu da sauri gashi iri mutanen nan ne manema mata ko yaushe tsab yake komai nashi neat tun daga kanshi har takalma zaki gashi neat dashi clean . Saidai shi dan karyane na gaake kuma manemin mata dama idan kaga na mijin kauye ya faye wayewa hakane dabiansa neman mata. Ko ita saratun da karya yaje mata saita lake mai har abin ya zama masu aure bai boye mata ba da abin yayi nisa ya fada mata shifa dan kauyen sokoto ne haka kuma bawai wani mai kudi bane shi. Ta dauka yana zolayantane kawai don ya barta sai gashi tace zata daiyi din ko yaya yake don ita a zatonta kawai yana fadane don ya gwadata ashe haka abin yake. Allah ya dora mata son habibi a zuciyarta don haka ko yanzu da tan uwa suka watse suka barta bataga laifisa ba tunda ya fa mata din abu dayane har lokaci bata tantance ba cewa da akayi itace ta hudu a gidansa. Bata gaskanta ba saida yan uwan mijin suka hadusu waje daya ana tsawata masu kan zamantakewa nan tasha mamaki ganin su hudune dai matanshi kamar yadda mama hafsatu ta fada data koma daga jere. Wanan yasa hankalinta tashi sosai har saida ta kasa daure ta kira mama da kuka tana fada mata itama uwar kasa daurewa tayi nan ta nemo kan iya tana labarta mata a zatontama Jafar bai gidan saboda rudewa ranan bata tsaya yin lissafin kwanan mu ba don ga yarta cikin bala,i. Ke dubu ki natsu dob Allah zama da kishiyoyi haka kan saratu ne farau din haka keda kika zauna a cikin kishiyoyi meya sameki nace ? Iya ba daya bsne da nawa don ni a cikin gari nake kuna jin duriyana kuma ina ganin na gida wanan kuma wani uwar duniya fa take bako kusa da yar uwarta hannatu ba can fa kauye ya ajeta. Sai akace kauyen ba a zama ko aure inane bai kai mace wai don Allah ana ce baki ga zuma kina ina badaci yarinyar nan dai tana son mijinta ko batace dake bata iya ba dubu ? Suna zancen jafar da habu suka shigo part din suna gaidasu nan iya ke fadin to kuyiwa uwarku magana tun bata jawo maku abin kunya ta kashe auren saratu ba ? Kashewa kuma akan me mama jafar ya fada yana kallon uwar iya ni baki fahinceni bane abinda nake nufi don me yayi muna karyan mata daya gareshi ? Haba mama ai hakane daidai da saratu gidan mata da yawa inda zata ji dadin yin gulman ta da makirci ba ta iya tsegumi ba tun nan tana shiga matan yan uwa tana hada fada yau gata Allah ya kaita inda zatayi nata. Habu nagane saboda matarka ka tsani yar uwarka to koma meya samu saratu yar uwarkace dai mama ta katse ya Habu daya soma magana. A,a mama ba wai zancen tsana bace kece kika damu akan wanan abin yarinyar nan itafa ta gabatar da mutumin nan tana son sa banga abinda zaisa ki damu kanki ba yanzu don Allah ? Habu yana nufin cewa zata iya zama a duk inda ta tsunci kanta tunda ta koya a gun matan mu da suke rayuwa tare a gidan nan shi kuma sai bai fada ba kai tsaye. Iya sai murmushi takeyi tace banda abin dubu saratu mace ce fa yau ko sha biyar aka wanketa a zamanin nan a kai cikin mata ukku ai tsab zata zauna dasu balle mace kamar saratu. Ai maganan habu gaskiyane zata zauna tunda ita ta saka kanta auren nan idan kika sa damuwa har ta fahinci hakan ta kaso aure tazo ta zauna maki gida shike nan. Addu,a yakamata kiyi mata mama yadda ko wata uwa kewa yarta in yaso sai a saurara aji ko zatayi korafi aka zaman nata kinga sai a san matakin dauka a lokacin. Wanan magana ta jafar ya kwantar mata da hankali suna cikin zancen saiga Saiba ta fado masu tana huci take fadin mama naje can ban sameki ba ? Ashe kina nan dama karan su na kawo maki kowa yasan dai nice zan karbi girki a jiya amma sai J yasan ban gari ya dawo yaba Asmau girkina. Wooo,hwahoo ni jikan mutum biyu yar nan kina data ido kuwa Iya ta katseta sa fadin hakan wani kallo tayiwa iyan kafin tace da hankalina wajen mama nazo. To meye a cikin hakan kuma Nusaiba akwai mana mama tunda ban karawa Rahama kwanan ba na dawo nan bata samu yadda take so ta bata min suna da yar mutane ba. Na dawo na kwana da Asmau ko kike nufi idan na tsaya can kuma ki dorani a ture ki yawata kina fadin na saci kwanan ki ? To na kwana din kiyi abinda zakiyi marata ido kawai bansan baki da mutunci ba ai da bandawo na samu kinwa Asmau duka ba yau. Tsuki habu yaja ya mike yana fadin ni zan tafi iya yaya karfin jikin naki dama nazo na dubakine zan tafi ya mike yana fito da kudi cikin aljihunshi ya mika mata. Da sauri ta mika hannu ta karba tana godiya hakan yabasu dariya aka wasance J ya mike suka fita da habun sun jima a wajen motar suna magana kafin ya bar gidan.