Sashe 272
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zance ya tabbata kuwa don Nusaiba dai Aminu ya fara fada min yana ganin kamar wanan dayan matar uncle fa ta dawo. Don yaga motoci da mata sun shigo sunata guda zuwa part dinsu a hakan kuma salima ta kiran ita da Asmau da yanzu tun bayan kiran da Asmau din tayi min muke dan gaisawa da ita sama sama don data kira cewa tayi dani. A Amarya Rahama dai kin sharemu gaba daya ko kizo gidan nan ki duba yaranki inmu ba dubamu ? Nace ban shareku ba anty gani nayi dai ya kamata naje gida na dawo kece yakamata ace kinzo kin duba jikina ai sai naga ba haka ba. Lalai kuwa anyi haka to amma ai kinsan halin gidan mu Rahama yanzu da anji nazo gidanki sai a fassara min abin da wani manufa ta daban shiya ban zo ba. Anty in baki zo ba saiki turo min yaran ba tayi dariya kafin tace to kinji dai mutumiyar mu zata dawo ko mama ta matsa wai ta dawo tunda dukkan mu bamu da amfani kanmu kawai muka sani mu sai yan uwan mu. Ikon Allah mudin to da wa zamu sani banyan kanmu da yan uwan mu dake kulamu wanda bai kaunanka ai kaima kayi nisa dashi ni ban damu wani yasoni ba bayan Allah. Son Allah kadai da Annabinsa nake nema sai mijina ban damu da son wani ko wata ba can don basu a gabana don Allah anty ki sa masu ido ki daina kula kowa da shirmensu neman bakinki sukeyi dama aji dadin bata labarin idan ta dawo. Ta dawo mana ba daina halinta zatayi ba ai saima abinda zai karu a yanzu don hakani dawowanta bai taba damuna ba anty ni kawai abinda nake so dake anty shine kiyi hakkuri don Allah. Ban dai daukeki makiyana ba don zama tare ya hadamu a yayata nake kallon ki har yanzu naji tana fadin wallahi nasani Rahama. To kiyi hakkuri abinda kika san baiso ki daina don Allah kema ki zage yadda kowa keyi a zama daidai ki fita batunsu kada ki biye mata yaran nan sunyi wayau a yanzu sun fara fahintar komai fa. Mun jima da ita muna magana har ina mamakin ko nawa ta saka a wayanta lokacin data dade haka tana magana dani din. Tun bayan haka muke gaisawa shine a ranan ta kirani take fada min zancen dawowan Saiba din ita ma na fahinci nufinta so take ta hada kai dani a yanzu ni kuma ba zan yarda da hakan ba hadin kai da kishiya cutane adaiyi zaman lafiya kawai kowa ya mutunta juna shike nan a zauna lafiya. Munyi hakan na kashe wayan tare da dimbin tunane a zuciyana a ranan yaya bai gari yayi tafiya amma ya kirani tunda safe yana sheda min cewa zai dawo a ranan . Don yanzu tafiyanshi ba irin na dadewan nan bane da yakeyi a baya iyankashi yayi kwana biyu ko ukku ya dawo gida. Duk da nasan tunda Nusaiba ta dawo bai garin don haka idan ya dawo a can zai sauka donshine ban matsawa kaina da mashi girki ba duk da nice da girki idan ya dawo din. Ashe wai hakan plan din Saratu ce na saiban ta tare a lokacin don su bata muna plan su hadani fada da yaya don dole sun san in anyi hakan zamu samu matsala a tsakanin mu dani dashi. Tun yana can ya samu labarin dawowanta din don suna waya yake jin hayaniya yake tambayan tana ina tace zaria dakinta don ta dawo tun jiya daga haka baice komai ba. Koda ya dawo din kuma gidana yayo direct ana ruwan sama a lokacin muna daki nida Biba dake zaune tana assignment ya shigo ita naji tana fadin uncle ya dawo. Jin hakan yasa nace ina take fadin taji muryanshi a falo kafin nayi wani magana sai gashi a dakin nawa yana fadin nakan fada maku idan kun shiga ku dinga kula da rufe gida. Kasan nan yanzu ba wani sequrity kwarai a yanzu Aminu muke jira ya shigo ya dauki abincinsa na bashi amsa. Idan yazo ya kwankwasa mana ko a aje mashi daga waje ana ruwan nan sai mugu yayi amfani da daman yazo ya cuta maku a raina nace cuta yafi naku kuma ? Na dan dago nayi mai sannu da zuwa ya amsa yana fadin ya kuke Alhamdullahi na fada a cikin basarwa ya juya ya fita mai karatu har zuwa lokacin ba wani sakewa a tsakanina dashi irin baya qda muka dan shaki yanzu duk na daina hakan duk da shawaran da mutane ke ban wai yana sona don haka kada in nuna abin ya dameni a bamgarena. Dole in nuna don yiwa dan cikina gata baka sanin halin mutum ka zauna ya shanmaceka nasan waye Saiba da Saratu hakama mama da danta. Don haka ban sanyaya a wanan zance ba gaba daya na kara dagula mashi lissafi idan ya dauka ni ruwan sanyice zan nuna mashi kalan tafasana a yanzu. Bafulatana fa nake ta asali ba muna fulani ba zuciya gadan shi mukayi a jinin mu yake ba ara min akayi ba idan kayi min sai nayima don bamu yafiya kona kara balle na fili. Ki tashi idan ya fita saiki rufe kofan nacewa Biba daga inda nake kwance jin hakan yasa ya dan juyo yana fadin idan na fita ina ? Nina rufe kofan aidana shigo ko Aminu din bai dauki abincinsa bane baya gidanne har wanan lokacin biba data mike don barin dakin take fadin ina ganin yana nan don da aka fara yayyafi yana falo yana cin abincinsa. Tana fita shima ya fita hakan yasa na mike zuwa kitchen na shirya mai abinci na kawo falo na dauko ruwa na samu ya fito yana waya naji yana fadin na dawo mana tun dazun ina nan gidan wajen Rahama. Yadda ya tsaya sauraren wayar yasa nasan maishi na koro mashi zancene a ciki na juya naji yana fadin mama wanan kuma ra,ayinane fa bansan da dawowanta a jiya bani ? Kai kai kai su mama dubu dai anga lagwai da tsohuwar nan nada ikon kasheni na tabbatar data halakani ta gama a duniyan nan. Yanzu uwace ke fada da danta haka akan matarsa a fahintana sunyi mai bazata shima ya mayar masu da hakan idan Saiba ta dawo a ranan girkina don su nuna min isa to Allah ya hau dani kansu ga baki daya yanzu. Da wayan yayi yawa bayan ya kashe aka kara kira naga ya dauka yana fadin na dawo ina gidan Rahama. Karshema yaja tsuki ya kashe wayan tashi baki daya ya aje gefe daya yacigaba da cin abincinsa ba dai wani hiran da mukeyi na zauna ya gama in kwashe kayan a wajen. Ina zaune kamar ban fahinci meke faruwa ba a lokacin har ya gama na kwashe kayan bance dashi uffan ba shima haka baiyi magana ba. Na fito kitchen yake fadin maganina fa da ruwan addu,an da kike ban ban hada ba na bashi amsa na shige daki na barshi a falon zaune . Kayan kwanciya na sauya a jikina na kwanta can dare wajajen sha biyu da rabi barci ya soma daukana sai gashi a dakin yana tayar dani. A cikin idon barci na bude ido na sauke a kanshi yana tsaye kaina saye da farar jallabiyansa mai dan hannu yake fadin wai meye haka Rahama kinfa san ina jiran ki kinzo nan kin kwanta kuma ? Ido na mayar na lumshe kamar ban san yana tsaye a wajen ba sai jinsa nayi ya fita daga dakin na soma barci ya dawo ya kwanta a bayana don jaraban maza daya motsa mai ya kasa rike fushinsa da yakeyi dani ko dai wani abu. Washegari da safe har muka zauna karyawa bai kunna wayansa ba saida ya fito ya zauna naga yana kunna wayan kamar ana jiransa a lokacin kira ya shigo. Tarr naji me take fada lokacin don kusa dashi nake zaune lokacin saibace take fadin ba sai ka nuna min kafi jin dadin abu kazan yar fulani ba zakai min haka. Yace ashe kin sani to tunda kin sani kisan matsayinki yanzu kada ki hada kanki da ita don ita din ba tsaran yinki bace look Saiba mena fada maki game da yarinyar nan kafin in yarda ki dawo ? To udan bakiji ba kada kiyi mamaki yau din nan ki kwana gidanku na har abada ba dai kinga na kyaleku ba kada ki dauka bokan da kike bine aikinsa yaci a kaina karr nake kallon ku wallahi. To in kwana mana sai me dama ban saba kwana bane a gidan namu wallahi akan wanan yar dajin matar taka ba zakai min wullakanci in kyaleka ba Jafar. Tunda banga abinda tafini dashi ba da zan dawo ka dauki kwanana kakai mata don ita tafi ko wace mace a idonka yanzu kome ?. Kwanafa kikace gashi kin ba kanki amsa tafiki komai ke nan ashe kin gane hakan keda kukace zaki dawo ki zauna zaman yarki ina ruwanki da kwanan da nakeyi da matana yanzu kuma ? Zaka dawo gidan ai ta fada a hasale kamar wace idan ya koma zata dukeshi a ranan ta kashe waya yaja tsuki ya dauki plate din abincin dake gabanshi yana fadin mahaukaciya kawai wanan ba zata taba canzawa ba tayi hankali ba wallahi. Wacece na samu kaina da tambayar karya tankar banji me sukeyi a wayan ba da ita ya dan kawar da kai kafin ya ban amsa da Nusaibace mana mahaukaciyar banza da wofi. Naja bakina nayi shiru don ba abinda ya shafeni bane zancen har ya gama kamar kurame haka muka zaune a wajen ba wanda ya kara magana a cikon mu. Saida ya dan jima ya mike yana fadin bari na leka gidan in dawo ina yaron ki yakene nace ya fita school tunda safe ok yana da lectures ke nan ko ? Ban tsaya bashi amsa ba don zuciyana dake famam sake sake a lokacin ko don wanan mahaukaciyar zan daure in biye masa mu kara haukatata kafin nasan abinyi. Lokacin kuma na fahinci dole akwai wata a kasa cikin zancen dawowanta gidan dole a kaina ta dawo ko wani abu amma yadda naji magananta haka a