Sashe 234
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
niyar barin wanan halin banzan da dan uwata ke dorata a kai na fahinci gaskiyan tsohuwar nan dauda ke zuga dubu ga duk abinda tayi mara kyau don ya zama dattijon banza. Wanan maganan na mama yasa na kara kafewa kyam ban yarda na bisu ba ina jin suna sallama da su ummah suka tafe . Ummah harda fushi dani don bayan tafiyansu yinin ranan daure min fuska tayi ko nayi mata magana a dake take amsa min yasa nima nayi shiru na kyaleta. Saida safe taga ina shiri take tambaya nace gidan mu zanje can garin mu nan kuma ta hauni da fada wai na rainata in tafi gidan indai kawune ai nasan abinda zanje in sama a gidansa . Ina kuka nake fadin koma meye ummah yafi min tunda gidan mune ko yayi min kansa yayiwa da in zauna mama tanaci min fuska don kawai danta ya aureni shike nan ta dauku kiyayyan duniya tasa min. Ni abinda saratu ke min bai damuna kamar na mama dake fadin zamu mallake mata diya su koma sai abinda mukace kamar yadda kika maida daddy nan haka mun asirce su daddy Abuja sai abinda mukace sukeyi akanmu shine itama za a kawo mata ga iyalinta. Nan ummah din ke fadin matan nan fa na dade da fahintar ta tun zaman mu asibiti da mukayi da yar uwarki ? Agabana in kun kawo abinci zata kama fada tana fadin ana barnan abinci ana saki abin miya haka da yawa don ba asan wahalan nema ba. Bayan wanan kashin kudin da aka dauko masu a yanzu kuma a koma ana barnan abinci haka ita ba zata yarda da hakan ba a diga kirga nama kafin a saka a miyan. Wanan ma kadan ke nan ai na fada na dinga bata labari ta hau tana fadin ita wallahi ba zata yarda da wanan cin fuskan ba ai muma yayane kamar diyanta bawai bata son mu bane ai koda sukaga tana nuna hakan kawaicine kawai nasu na fulani take muna. Wanan yasa ta dauki zafi akan zancena din take fadin ki zauna sai tazo gidan nan da kafanta ta sameni na fada mata abindake raina nima kafin ki koma din. Tun bayan barunsu gidan habu ya fisgi mota yana gudu Iya ta lekoshi daga bayan mota inda take zaune tana fadin kai hanu kajamu a sannu don Allah ? Kana zuciya kamar an maka wani abu yarinyar nan tana da gaskiyanta inma laifine ita dai akaiwa shi ba karya ta fada ba ai. Tunda yarinyar nan ta kafe haka abin ne ya isheta don Allah nasha fadawa uwarku ta guji irin wanan ranan kada haka ya faru amma bataji ba. To wai ni iya ban gane ba me akewa yarinyar nan haka wai naga gidanta daban mana yazid yake tambayan hakan ? Kadai fadi duk yadda akeyi Yazid J yayiwa yarinyar nan amma wai shine don jin dadi zatawa mutane rainin wayau haka din taga yana yinta haka sosai a cikin matanshi. Allah sarki dama hakane ai idan namiji ya nuna kai yakeyi sai ace komai yi maka akeyi ita fa baku fahinceta bane har yanzu nake gani habu ? Yarinyar nan takafe akan ba zata dawo gidan nan bane kan irin cin fuskan da uwarku take mata a gaban kowa Dubu take nunawa yarannan hattara da kyamansu tana sakin maganganu akansu. Kasani kowa kuma yasani idan matsafane ko mayu aida yanzu sun baiyana daba hakaba da sauri iya ta dafata tace madallah Amina kin gane matsalan kenan ke ashe ? Shi wanan bai san komai ba sai zuciya a gaban yaran nan take nuna bata kaunarsu batayin lamarinsu su din ba kowa bane sun shigo rayuwanku zasu juya mata kanku . Wani tsuki yayi yana fadin nasan wanan mama aiga maria nan wani irin cin fuskan mamane bata gani ba a gidan nan kan matan J da bako kyautata mata sukeyi ba kamar ita kuma tayi hakkuri ta zauna . Ba zaka hada ba habu don idan anyiwa matarka kana tsayawa tsatin daka ka nuna bacin ranka kan abin shiko jafar fa bai iya komai saidai ya juya ya wuce kawai har can gidansu fa take binta itada dauda suyi mata kaca kaca su dawo zakace kadata nuna itama mutunce don Allah ? Inda laifi daga Jafaru har dubu da yan banzan yaran nan duk suna da laifi saidai kawai ace ayi hakkuri kawai shine yanzu amma abinda yaran nan sukeyi banga sarakuwar gidanmu dakeyin hakan ba gaskiya. Yarane da suka san mutunci da kimar babba da darajan dan adam mutum indai daga bangareku ya fito yaran nan zasu darajashi yaya ake son mace tagari ta kasance wai ? To mama ai na dauka don kawai wanan abin daya hadata da Saaratu ne take wanan zuciyar ashe bashi kadai bane tarawa tayi ta amaye muna komai lokaci guda haka ? Inda zata amaye din ne aida ta amaye muna idan watace ba tas zata fada a gaban kowa ba cewa ga abinda ke nan amma ita kaga tayi hikima takafe akan bata komawa kawai ? Dole aiwa abin tufka gaskiya bansan yaushe mama ta juya ta koma hakaba bayan tafiyana koda yake ance kawune matsalan komai a yanzu shike hura mata kunne yake zugata. Tundana dawo nake son a zauna naji zancen kudin mu dake wajenshi matsalan nan na j yasa na kyale amma yanzu ai dole mu hadu tunda ina son kudina na fara dan bussiness dasu . Habu na fada maka kabar zancen kudin nan don babu su rayukane kawai zasu baci a karshe don ko mama ta sani babu kudin nan a yanzu. Babu fa kace bros haba dai wanan wasane kawai kubar zancen agama wanan don Allah kada ku tayar da wani zance a yanzu muna fama da wanan ? Shiru sukayi don habu ya fahinci iya saboda mamace dake cikin motan abin daya shafi iya sune zancen kudin nan bai kamata ace wani na wajen dakinsu yaji zancen nan ba. Shiko yazid bai gano hakan ba sai fada yakeyi yana fadin kawu zaisan koshi waye bai sanshi bane wallahi jin kowa a motan yayi shiru yasa shi fara fahintar akwai matsala. Sai mama din ke fadin kai yazid ai kaji iya tace ka bari agama zancen nan toka bari mana hakan ya isa ba sai ka bata ranka a yanzu ba ai. Koda suka isa zaria la,asar tayi don haka su basu shiga part din ba saukesu Habu yayi yace zaikai matarshi gida ya dawo. Shi kuma Yazid part dinsa ya nufa saisu Iya da mamane suka shiga ake masu sannu da zuwa don nan suka samu kawu da mama dubu a zaune tare dashi. Tayi masu sannu da zuwa tana fadin ina yarinyar ko an sauketa gidan can ne don bata ganni ba iya tace wani gida yarinya kan na hannun iyayyenta sun rike abinsu kamar kowa . A,a duk da kunje basu baku itaba ke nan kuma yau ga mutanen banza marasa mutunci har anbi bayan yar ku kuma ku hanata dawowa akan wani dalili wai kuma ? Shi nake son ji kawu ya fada a cikin bacin rai iya ta juyo tana fadin akan dalilinku na cin fuskan da kuke mata ta hakkura tabar maki gidan da danki a zauna lafiya. Sallah ya sallame daga inda ya zauna ya juyo yana fadin wai bata dawo bane iya da gaske ko tana can gidan kun sauketane ? Bata dawo ba Jafaru ta nuna bata dawowa gidan nan a yanzu ban sanarwa gaba ba inda rabin dawowanta ?