Sashe 133
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru tayi ta juya zuwa dakinta cikin hasala ashe baki ciki yar iska ba daki dawo ki maimaita abinda kika fada a gaban yan uwana. Yau in baki mamaki don da kinbar gidan nan na har abada su yaya zaki kawowa rashin kunyar ki sun wuce hakan a wajena balleke. Duk iya shegenki da iskanci ya tsaya akaina amma banda yan uwana don kamar iyayye suke wajena bazan daukar maki wanan iya shegen daki dauko yi a gidan nan ba. In zaki zauna kiyi hakkuri yadda kowa yayi ki zauna idan baki hakkuri kuma kofa a bude yake gareki tun yanzun nan kaji min sakarai mara lissafi ba a hakkuri ke akai hakkuri dake aka zauna koba wata kika shigo kika sama a gidan nan ba. Akwai yar cin aman data fiki keda kika yaudari kawarki kika hana mu zaman lafiya don son kai irin naki ? Yi hakkuri Jafar mu ai mun tashi ke nan muma tunda munyi abinda ya kawo mu. Mu yanzu idan bata so dai ruwanta Allah ya gani ka fita hakkinta ai ba kowani namiji ke wanan ba yanzu don ya kara aure. Yanzu a zamanin nan in bashi ba wani namiji zai kashe maki wanan galarin haka kuma baki shafa masa lafiya ba gidansa ? Shi ya daukesu don ya mayar dasu gida a hanya yayi fada sosai yake fada masu irim damuwan da saiban har asmau suke sakashi ciki. Sai hakkuri suke basu a nan family house suka sauka tare da nasu abin arzikin har yan uwan zaman mama dubu alherin ya shafa. Dama haka yakeshi muddin ya samu kudi sai kowa na tare dashi ya sani don zaibi yan uwa daga daga ya dinga masu dan alheri daidai gwargwado. Wanan yas arzikin yake bukansa kamar an bude masa kofofin arzikinsa ga baki daya shi mutum ne mai yawan alheri. To wanan alherin daya shigo maine yabi yan uwa ya raba masu abin arziki har mazan da yan unguwa abokan arziki ya samu abinda ya basu a lokacin. Kwana shidda ke nan yayi a gidana kuma zai koma washegari don aiki daya taso mai na bussiness dinsu lokacin sun samu kaya irin wanda suke fita dashi waje din zai tafi ya gani. Ance sabo turken wawa a yan kwanakin na saba da yaya Jafar sosai yadda yake jana a jiki hakan yasa na fara sakewa dashi inda ko fita yayi kafin ya dawo na shiga damuwa. Shiko sai shirye shiryen tafiyansa kawai yakeyi daga gidan iya har nan da nike ni kadai abubuwa kawai yake shigowa dasu yadda ba zamu nemi komai ba ke nan a bayanshi. Gwargwado yaya Jafar yana kamanta adalci a dan fahintar danayi mashi yadda yake a tsakanin iyalinshi din haka kuma ina ganin yadda yake mu,amulansa a baya kafin na aureshi. Missalin hudu ya shigo gidan nasu kai tsaye part din iya ya nufa wanan dabiansane yanzu sai ya fara shiga yaga kwanansu ya wuce zuwa wajen matanshi. Saidai ga mamakinshi a nan part din ya samu matan da kowa na gidan zaune inka debe yar uwara da yanzu ke zaman kadaici ita kadai don kamar an hada mata kaine a gidan gabadaya sai salimane ke kula lamarinta. Suna ganinshi sukai tsuru tsuru bakin dayansu kallo daya yayi masu ya fahinci akwai matsala haka ya daure ya gaida mama da iya ya samu waje inda saratu ta daga ya zauna yana fadin. Lafiya dai ko ? Ina fa lafiya Jafaru fitina su wa yan nan ai bata kwana a wajensu ko yaushe tsaye take suna figanta. Wai kayan nan daka shigo dasu suke fada a kai yakai harda bugaiya suna nema su illanta kansu sujawa mutane aiki. Fada kuma akan me iya to gasu nan dai kaji a bakinsu ance waka abakin mai ita yafi dadi dama. Duban inda suke zaune yayi yana fadin ke Asmau ya akayine tace ina daki Nusaiba ta sameni wai na rage kayan nan dakai muna su yaya suka shigo dashi. Wai da suka tafi na hurhura kayan cikin na kwashi masu kyau nabar mata marasa kyau don haka in fito da nawa ta dauki abinta niko bansan wasu kaya dana dauka a cikin nata ba. Innalillahi ya ambata a fili ya katse mata zancen da fadin iya kayan nan komai iri daya aka saka don gudun haka yanzu haka kayan haihuwan ita asmau suna nan aje don kada tazo ta haihu ban kusa a girsheni don hakane ban kawosu gidan nan ba na aje. Amma kuma wai kinji abinda wanan mara hankalin take fada yanzu komai fa kala dayane a cikin akwatin saidai a banbanta kala kawai . Samu sukayi aida Allah bai kashe ya basu kai ba daka zama bawan matam da basu godewa irin hakan ba zai faru ba to sun samu sai suyi iya shege ai mama ta fada cikin kunan rai. Mama laifine yau na samu banwa iyalina ba au duniya saita zageni kan hakan to ya zama laifi kan a wajen matanka yanzu . Yanzu idan nayiwa Rahama kayan lefe ban masu komai ba ni kaina nasan sai Allah ya tambayeni akan hakan tunda ina da halin yin hakan garesu duk da nasan karshe wullakantawa zasuyi tunda basu iya tattali ba a rayuwansu. Nusaiba baki da tsoron Allah a lamarin ki kayan nan bake kika rokeni ba ganin daman kainane na hado makushi yan uwana da suka kawo kayan nan ranan saida kika nemi yi masu rashin kunya. Don baki da kunya yanzu kece kika dawo kina fadan kayan kuma ke bafa dole bane zama dake Nusaiba koda duniya muka haifa dake kin sani ? Kawune ya shigo yasa yayi shiru bai cigaba da fadan da yakeyi ba lokacin gaidashi yayi ya mike yana fadin mama ni gobe zan koma daga can ina ganin har kasan waje zan fita don mun samu kaya zan bi jirgi in samesu can. To wani kasa aiki kuma kuka samu na fita kasan waje yanzu Jafar kawu ke tambaya yace eh ba wai kasan wajen turawa make nufi ba ai nan ghanane kawai na fadi hakan don ta gane. Ghana ba kawai bane ai Jafar ya fada yana dan dariyan yake a fuskansa zuciyarsa kuma tana mashi tafasa da wanan zancen da yaji don yasan a baya kome jafar din ya samu zai fada mai. Yana fita part dinsa ya nufa Nusaiba ce ta fara mara masa baya ta bishi ganin ya nufi part dinsu yasa ta biyoshi ba tare datayi magana ba . Dakinsa ya nufa ta bishi a baya ta sameshi duke yana daukan wani takarda a drower ya dan juyo jin anshigo dakin ya ganta tsaye a kansa. Yanzu tafiya zakayi baka dawo gidan nan ba kome komu bamu da hakkin ka dawo wajen mune inka gama kwanakin ka a can din. Kwanakina ai bangama ba zan tafi tunda saura kwana daya in mata a gidan ta kinga kuwa ko ita ban karasa mata kwanta ba ke nan ai ? Cabdi wanan ai zaluncine wallahi mu meka maishemune wai yanzu ? Abinda kika maida kanki shina mayar dake Nusaiba ke inkina da kunya har zakiyi wanan maganan a gabana to inama kikaga kunyan balle babu sam baki da kunya don ban taba zaton haka kike ba ai sai a cikin yan watanin nan nasanki tsab. Kome zakace zakace ai tunda anke an baka kasha ka lashe baki yanzu mun zama banza da bamu da amfani mu a wajenka. Au ba wankewa tayi ta ban ba, kaina kafa nasha na lashe ,ai ban tsaya saita wanke bama nina kafa kai na lashe komai da kaina. Lalai akwai kazan uban nan kuwa don gabadaya an sauyaka yanzu har da abinda baka yi ka fara yinsa gidan nan to mu zuba da ita wallahi. Ki dai zuba yadda zaki iya kwasa aurene dai nayi baku da kudin wani na kara aure ba yadda na auroki aka tara shedu haka itama na aurota gidana. Yazo ya wuceta da takardan a hannunshi zuwa falo nan ya samu Asmau ya zauna yana duban takardun nasa saiban ta fito ta sameshi tana fadin. Wallahi duk abinda mutum keyi Allah na ganinsa ka dauko yarinyar nan don ka bakanta muna rai kan abinda bamuyi ba akace munyi. Zancen da abakin yan uwanka mukaji suna fadin ga ciwon dake jikinka shine laifin ka dauka ka dora muna a kai yanzu ? Na fada maki ai zaki girbi abinki koban fada ba yan uwana da suka fada din banji a bakinsu ba sai naki. Badai dadi haka yakai yamma dasu a gidan yabasu kudin cefane dana sauran bukata yayi masu sallama ya tafi ya barsu nan. Ranan da ta sauka gida tayi mamakin ganin gidan a share tsab komai an gyara ba yadda ta saba tafiya ta dawo ta samu gidan kaca kaca ba wanan karon har da abinci aka aje mata shimkafa da miya da salad . Tabarma suka baza a tsakar gida tare da yaranta dake jiran ta bude jakkar tsaraban data dawo dashi ta bude jakka ta mikawa yaro guda kudi tana fadin amso min coca colan kwalba bata gora ba mai sanyi zakace a baka yaron ya karbi dari biyar din ya fita sai gashi ya dawo da kwalban cock din dake nason sanyi a hannunshi. Ya mika mata ta karba tasa baki ta balle murfin ta kafa kai tana zuka gyatsan da yazo matane yasa ta sauke kwalban a bakinta. Ta saki wani uban gyatsa tana hamdallah ta ture abincin gefe daya Aliyu dake gefe zaune ya zubawa uwar ido tun bayan shigowanta gidan yake nazarin abubuwa da dama game da mahaifiyar nasu. Daki ya shiga yasa mata kira take amsawa tare da juyowa ta hangoshi zaune saman kujera yana dakon shigowanta dakin. Saidai bata da niyar tashi daga inda take zaune din don sai hiranta take zubawa tana bada labarin abinda ta gano da wanda akayi saidai ba zancen rabon gadonsu da sukayi da yan uwanta a cikin hiran nata. Daga daki yaron ya kara fadin mama fa sai kanwarsa ke fadin mama yayana magana dake a dakifa tundazun kallon yar tayi tana fadin ina jinsa me zanshigo daki in mashi ? Muna nan zai shige daki yace inzo idan bai iya fadan abinda zai fadi a nan ya bari har lokacin