← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 243 OF 306

Sashe 243

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da ita komai ba a lokacin saidai a zuciyana na fada nakeyi ina fadin wanan shiya shafa a yanzu don sun fini sonshi ai idan ya halaka sun huta don kowa saiya kama gabansa. Haba dau uwata aida kinyi hakkuri kin koma Saudatu ke fadan hakan gareni da sauri na juyo ina fadin in koma ina saudatu gara dai kowa ya taba yaji a yanzu ai. Ba komai ya kawo hakan ba don itama maman tudu ta koma gida sati biyu ke nan yanzu kingako inba iya ba a yanzu ba mai tsayawa ya bashi kulawan daya dace ? Iyan kuma ba karfine gareta ba sai naji ummah tace mahaifiyarsu saida na juya idon nake fadin in kawu ya bari ta zauna har ta kulashi ba ? Ni dai sai ince auren ki da bawan Allah nan uwata auren kaddarane kawai amma ba wani jin dadi ga hakan sai bakar wahala kana amaryan ka ko haihuwan farko bakayi ba zaka tsaya jinya irin haka don Allah ? Haba saudi ai hakan ma bautan aurene tasan irin ladan da zata samu a wajen Allah jinya takeyi fa kuma na mijin aurenta. Duk abinda kagani ya faru da bawa da sanin ubangiji Allah kadai ya san dalilin haka ga bawansa Allah yasa hakan alherine gareta damu baki daya ummah ta katse maganan da hakan duk muka amsa da amin lokaci guda. Take fadin ni kingani nan saudi bawan Allah nan tausayi yake ban abu daine na dan yau wallahi da yarinyar nan da daddy sunbi ta tawa datayi hakkuri ta koma dakinta hakana . Duk abinda zasuyi ko suce mata ta sharesu kawai ladanta yana ga Allah haka kuma wata rana duk sai labari insha Allah don gaskiya mutumin nan yana sonta banga abinda zata tsaya duban iskancin wasu ba dama su ba son ganin ki sukeyi tare dashi ba ai. Hakan da kikayi kuma ya basu daman samun kafan da zasuci gaba da musguna maki ai mutum in makiyinkane kada ka yarda ya samu kafan galaba a gareka ? Ina kurum ban tanka mata ba don nasan indon tasuce ita da yar uwata basuki in shirya kwatsam ince na koma ba a yanzu din ba tare da anyi min gatan da daddy keson ai min ba. Ummah kodana koma wanan matar bawai zata canza halinta bane a garemu na sani amma hakan zaisa na samu dan dama a wajensu ai. Ita Yanda mijinta yana tsaye garesu shiko wanan fa ummah bai iya katabus ga iyalinsa sai abinda tace dashi zaiyi haka kanninsa mata. Saidai hakan amma dai gaskiya ya ban tausayi sosai wallahi zan samu lokaci ai in kirashi mu gaisa inji yaya karfin jikin nasa. To hjy idan kinyi hakan ba laifi bane amma ya kamata kowa ya sharesu nan yadda suma suka share kamar basu damu da itaba yanzu idan kin kira zasuga kamar kina bikonsune suzo nan. Shiru nayi don gaskiya saudi ta fada ba karya a zancen ta don ko kowa bai fada ba mama zata iya fadin hakan kuma naga zancen yayi tasiri ga ummah . Don tace hakan ne kuma tunda matar ba mutuncine da ita ba ta fahinci hakan tun haduwanta da Hjy Sa,a data hada ummah din da mijinta na yanzu da take aure. Don yadda mama taso kushe abin sai Allah ya kawo ciwon Jafar na farko a lokacin hankalinta ya dauke da jinyarsa har aka samu akai auren don hankalinta daya dauku wai a cewanta ga kawu nan ya nuna yana son ummah din a lokacin. Ganin yadda ya rame a kwanakin yasa mama din mayar da hankalinta gareshi saidai tafi saka rai da fadan cewa saboda nabar gidan yake son ya halaka kanshi ga banza ? Har yakai ranan ya bata amsa da fadin mama koda tunanenta nakeyi ai hakan ba laifi bane ki duba yadda aka barni haka ba gyara ba komai kamar mara gata mama ? Ace Asmau bata da lokacina saidai kwanciya idan anyi magana tace aiki yayi mata yawa a hakan kuma take son in barta ita kadai ba tare da wata ba ? To ai tasan hakan ba zai yiyu ba ita dai waccan mara hankalun idan ta gama shashancinta ai dole ta dawo a zauna tare ai yanzu tayi hankali hakan ? Wa kike nufi yarinyar nan Rahama kowa iya ke tambayan mama din tace Rahama kuma uwar yarsa dai ta dawo ta samawa yarta abokan shawara hakana. Bako a gidan nan ba mama don na gaji da fitinan Saiba hankali a kwance yake banson abinda zai raba min hankali biyu yanzu kuma. Rahama dai nake Habu nake son ya dawo daga legos zuwa jibi inbi bayanta in dawo da ita bakai kadai zaka tafi ba dole uwarku taje har yaran nan suyo maka bikon matarka kamar yadda mijin uwarta ya fada. Iya kikanso kamawa karya yanzu don ance sai naje shine zakice har dani zasu tafi in yabi ta tawace ai ko zuwanma ba zaiyi ba shi balle aje zancen wai nima in shirya inje din. Anya biyu kina kaunar dan nan kuwa duk cikin yayanki na kula Jafarune baki damu da damuwansa ba dubu ? Yau da kina da tunane da yarinyar nan batakai wanan lokacin ba a gidansu zaune da akace kece matsalan dake da yayanki da tuni kin tasa keyan yaran nan kun dawo mashi da matarshi. Amma da yake haka rayuwanki take kamar mara kwakwalwa Dubu baki san mutanen nan tarko suka dana maki ba don su gaskanta abinda yarsu taje ta fada. Ki barshi ya taka a hakan har kaduna tunda sakariya kike baki da lissafi kiga abinda zai biyo bayan hakan a karshe. Don ke da kanki zakiyi dana sanin rashin zuwa din duk ranan da tunane ya kara turmuze yaron nan har ya kwanta a gidan nan don saura kiris a kai ga hakan yadda yaron nan ya koma don tunane. Matukar kika bari har ya taka yaje bikon matarshi aka hana masa ki saurari naki bakin cikin da zaki tara akan hakan tunda yaran nan suna son junansu. Har yanzu kina wani zancen wanan mara hankalin ta dawo ta dawo a yanzu tayi mashi me yarinyar da bata san Annabi ya faku ba har yanzu. Matukar Rahama taki daaowa gidan nan dubu bake ba harmu ga baki dayan mu sai abinda zai biyo baya gidan nan ya shafemu kaf a gidan nan . In kuma kince a,a kada kije tunda kece sauniya mara hankali kawai ina mamaki matuka sauyawan yanayin ki dubu ? A yanzu kowa ya zuba maki idone yana kallon wautanki dubu kinsan farin cikin yaron nan kin kuma san komai game da hakan ? Ke yanzu ba abin kunya bane a gareki dubu yadda kowa yasan zancen da irin dawainiyar yarinyar nan a gidan nan kan yaron nan amma ace wai har kin yarda haka ya kasance da ita akan yayanki.
Chapter 243 · 0% Book details