Sashe 257
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasa a raina ranan zai koma wancan gidan donshi ma banyi motsin girkin dare ba don nasan a ka,ida dai kwana bibiyu mukeyi ga girki tun muna mu ukku. Balle yanzu da mu biyune tare dashi muna falo zaune tun bayan fitansu yaya Ai da sukazo min sannu da dawowa a cewarsu. Muna zaune maigadi yayi sallama ya tsaya daga kofa yana gaidamu bayan ya amsa yake fadin akwai wani yaro a waje tace daga zamfara yake a fadama sunansa Aminu ? Kallon sa nayi naga ya daure fuska yana fadin to me yazo yi nan da baije can gida ba wajen su mama zaizo nan kallonsa nayi nace ko dan yaya Barakhane ? Yace shine mana don me zai biyuni nan kuma yaushema yazo garin na dubi maigadi dake tsaye nace dashi ce ya shigo malam don malam nake kiran maigadin dashi. Ya juya da sauri ya fice fada yaya keyi yana fadin don me zaizo nan barshi yazo najima meya kawoshi ni ban daukan wanan iskancin a yanzu gaskiya. Haba dai ba girmaka bane yaya yaron nan ai ya gansu ya nufo nan inda kake don Allah dai kayi hakkuri kaji abinda yazo yi din. Yaron ya shigo tun a kofa ya zube yana fadin kawu ina wuni ya amsa mashi fuska daure yaron cikin in,inniya yasoma fadin dama naje can gidane na samu baka nan su mama ma sun fita akace sai mama salima ita kuma tana barci. To sai akace me ita Asmau bata nan ne ya tambayeshi naga yayi kasa da kai ganin na mike tsaye yasashi fadin mummy ina wuni na amsa da Aminu anzo lafiya yaya su anty ? Suna lafiya kalau ya fada kafin mu gama gaisawa ya sake jefo mashi tambaya da mekazo yi zaria ko baka fara school din bane har yanzu. Nayi jam kawu basu fara dauka bane ya fada na katsesu da fadin kaci abinci kuwa Aminu yace yanzu na iso mummy naje can ban samesu ba nazo nan. To shigo mana kaja ka tsaya can a kofa kamar wani bako bari na kawo ma abinci kaci ka huta sai ku tatauna ko na nufi kitchen din mu abinci na hado mashi mai lafiya yaji ganye a sama da kayan hadi. Inda yake zaunse nakai mashi ya karba yana godiya na juya na kawo mai ruwan sha ya soma jan plate din zuwa gabanshi na juya zuwa cikin dakina . Na dan jima a dakin na fito na samu yaya na fadin to yanzu yaya kake son ayi ke nan shi ubanka ya koreka gidansa shine ka nufomu nan ? Bayan haka kai baka da hankaline ko kasheta yayi ina ruwanka da saka masu hannu a cikon fadan da sukeyi dashi ? Mahaifinkane fa Aminu baka da hankaline koka fara shaye shayene yaya yi hakkuri don Allah kasan uwa ba yadda za ayi yana tsaye yana kallon zai kashe masu mahaifiya ya kyalesu ? Nice na tsoma masu baki a zancensu bayan na gama sauraren maganganunsu da dansa din abindana fada yasa ya dan kalloni yana fadin. Haba Rahama baida hankaline da zai ture ubansa ubansane fa don kawai yaga suna rigima zai saka baki a cikin zancensu hakan ya nemi albarkansa ke nan ? Zaune nakai cikin sanyin jiki ina fadin yaya ceton mahaifiyarsa kuma yana iya saka yayi komai a lokacin rabu da irin gidan nan da ake irin haka a gabab yaya abin yakan saka yayan shiga cikin zancen wani lokaci. Don babu mahalunkin da zai zauna ana dukan uwarshi bai dauki mataki akai ba kai ya girgiza yana fadin Rahama na gane da sauraki kema kina da kuruciya a tare dake . Har yayi shiru ya dago yana fadin meyasa su yan uwansa mata basu sa hannu a rikicin ba sai shi zaisa hannu don gashi mai karfi ko zai iya fada da ubansa. Ba hakana bane yaya yayi kuskure don Allah da gani a jigijce yake a barshi yaje ya huta bari nasa maigadi ya bude mashi dakin baya guda ya zauna kafin asan abinyi. Da sauri naji yaya din yace No don me zai zauna muna nan baga can gidan ba ya zauna mana da iya nace don Allah yaya tunda yazo nan din ka barshi ? Kayi hakkiri ya zauna nan din bai min magana ba na dade a zaune wajen ina sauraren amsan shi baice komai ba har lokacin. Haka yasa na mike ina fadin inka gama taso muje kaga inda zaka sauka din na fice ba tare da nace komai ba. Shima kuma baice komai ba sai wayanshi da yake duba ya fita batun mu daga bayan mu akwai dakuna hudu kamar boys quaters a gidan da suke rufe sai maigadi dake dan amfani da guda don adana abubuwansa. Tambayasa nayi ina kayanka ko suna can gidan ka bari yace haka nazo mummy don bai bari na shiga gidan ba balle in dauki wani abu . Ok shiga kayi wanka ka huta zuwa anjima kazo ka fita nan titi ka samu kananan kaya ka saya na juya na bar wajen ina jin yana fadin nagode mummy nagode. Na koma ciki na samu yaya a zaune zama nayi ina fadin an bude mashi dakin tsakiya zai zauna a cikinsa shiru yayi ba amsa hakan yasa naja bakina nayi shiru a cikin tsarguwa da hakan da yayi min din. Kamar daga sama naji muryanshi yana fadin ke har yanzu baki fahinci mutanen nan ba naga kina kokarin jawo muna yaron nan a gidan nan banson wani abinda zai kawo muna fitina ko tsegumi ki barshi can ai kakansa tana nan yaje can wurinta ya zauna mana don me zai nufo nan gidan haka kai tsaye. Shiru nayi ina nazarin zancensa a kaina tabbas gaskiya ya fada don ba mutanen arziki bane alheri sai ya zama tsiya a wajensu. Zama na gyara ina fadin ni naga ba zaizo nan mu koreshi ba ai yaya tunda yazo din sai ayi hakkuri don kai ba za aga laifinka ba sai nawa tunda yariga da yazo kayi hakkurin hakan don Allah. Bai kira yace dasu yaron na gidansa ba hakan yasa hankalinsu ya tashi lokacin da uwar ta bugo waya tana tambayan ko yaron yazo nan ? Duk hankalinsu ya tashi haka ba wanda yai dabaran kiransa ni dai ganin har magariba banga yana shirin komawa gidan can ba sai mamakin hakan da zaiyi nakeyi a zuciyana. A bangaren yaya barakha an nemi Aminu a nan gusau ba a sameshi ba har washegari hakan ya daga mata hankali ta bugo waya nan zaria tana tambaya ? Mama Dubu hankalinta ya tashi har dare suna buga waya gusau din suna tambaya ko an ganshi sai ace har yanzu dai ana nemansa ba,a sameshi ba. Ga jafar da suke sa ran shigowan gidan har goma na dare ba labarin shi hakan yasa mama sa a duba mata ko yazid ya dawo aka dubo yana gida. Da kanta taje part din yazid din ta sameshi tana tambayan malam fa don sunan malam Jafar marigayi da sukai jahadin da,awa a cikin kasa yasa duk wani Jafar yawanci ake saya sunan nasa a cikin girmamawa ga malam Jafar din dake tashe alokacin. Yagane dan uwansa take tambaya donshi ake kira da wanan sunan na malam din take fadin malam fa yace yana lafiya ta amsa da aina sani tunda naji shiru ? Tambayanka nayi har yanzu bai shigo ba kai gaka ka dawo gida ko da kansa zai dawo yau ya kamata ace yana nan ga zancen yaron nan da har yanzu ba a gansa ba ko za ayi wani abu a nan ? Mama J aiba zai dawo gidan nan ba yau ban ma tsamanin nan kusa gaskiya kin ga a yan kwanakin nan yadda ya koma kuwa ? Dakata don Allah nasan duk bakin ku daya shi zai fara yace bai dawowa gidan nan a yau da kuwa na sameshi a can naci masa mutunci. Acan kikace mama kwarai ko kana tsamani ba zan iya bane kagani ya dan dubeta ya kawar da kai ya soma tafiya yace zaki iya masa hakan nasani to kira min shi yanzun nan . Ko kaje kazo min dashi yanzu gidan nan yanzu fa mama gomafa ta shude da nan da can ai dayane nagani meye ruwanki da zamanshi can din ke ? Yazid kai abin da nace kada ranka ya baci dani a wajen nan Ok yayi bari na kirashi naji in zai dawo sai naje na daukoshi din. Ya kira wayansa bai shiga ba haka yasa ya fada mata gaskiya itama kuma taji matar computer tana sanar da hakan a wayan . To kinji wayansa a kashe yake yanzu yaya ke nan kaini gidan idan ku ta shanye ku aini bata shanyeni ba har ita karamar yarinyar ta isa ita da masu taimaka mata din kar nake kallonsu. Bai haifawa jikokin fulani diya ba balle suzo su mallake min yaya da raina da lafiyana ina kallo shi kuma J far din zaizo ya sameni ai zai jini. To bari in shirya in fito ya fada ya koma ciki itama ta juya zuwa dauko hijabinta don tafiya ya shige ciki yana dariya. Har ta fito yazid din bai fito ba nan kofa ya tsaya yana kallonta yana gyara rigansa hakan yasata daga murya tana kirasa a hasale tana fadin zata saba mashi fa idan bai fito sun tafi ba. Iya dake cikin tana jin sautin muryan mama ta fito tana fadin lafiya anga yaron ko don tana cikin damuwan rashin ganin yaron a lokacin. Karan budan kofan da iyan tayi yasa salima dake kwance tana charting ta biyota tana fadin iya lafiya ? Iya sai fadi take anganshi ko cikin rawan jiki a lokacin Yazid ya karaso yana fadin mama shiryawa fa nakeyi don nayi shirin kwanciyane kika zo . Nace kunga yaron ne iya ta sake fada karo na uku ba a ganshi ba iya gidan Jafar zamu mama ta dauko shi ya dawo nan. Jafar kuma ta daukoshi kamar yaya iyan ta tambaya to ni dai tace in kaita ta daukoshi can din wai nan ya kamata ya kwana a yau ? Dubu iya ta fada cikin mamaki tana kallon yar nata da wani irin kallon dake baiyana mamakinta