Sashe 289
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yar uwa saidai ince Alhamdullahi masha Allah don abubuwa sun kankama cikin dan kankanin lokaci abinda ake fatan samu a rayuwa an sameshi don kuwa tafiyan nan da yaya ya samu yayi ba karamin alheri ya jawowa rayuwan mu ba sosai mussanman mashi dani. Don abinda yasa nace ni anyi sunan moh,d a cikin walwala da dadin rai anci ansha anyi alheri kuma baby ya samu alheri wanda zance a sanadinsa na samu hakan . Ubangiji Allah ya tsallakeni daga kaidin mama hassada ko bakin cikine ko kiyayya da ake min kasancewa da yaya ya zamo min taki a rayuwa lokacin haihuwan dan nan. Don ba karamin alheri na samu ba ga haihuwan dan da mama da kishiya suka sare min gwiwa tun a cikinsa ba abinda na samune farin cikina ba sai irin yadda kowa ya dauki dan zai furta masha Allah wanan photocopy ne kawai na Jafar da mutane ke furta a bakinsu don dan tun yana karami ubansane sak ya kwaso a kamanninsa. Ga kyauta ta inda ban zata ba da yake shigo mun in kuma an kawo din uban yace a ban nice na wahala ai na rike ba kamar yadda muka soma zaman asibiti ba a takure yana karba din a lokacin. Ni dai banda tacewa ina zaune mama ke fada min na dauki duk wani abinda zan dauka don ba a nan za ayi taron suna ba can gida zamu tafi ayi taron don mama tace mu dawo nan ayi taro a gabanta. Don haka tun daren suna muka dawo nan gidasu inda matanshi dasu iya da mama suke zama a gaban mama a part din iya muka zauna. Na samu salima ta gyara wajen tsab tsohon dakina a nan akai min masauki dani dasu mama da Biba tun kan muzo saida mama ta gargadeni akam koma meye manufar mama in daure inyi hakkuri kada in nuna hakan ya bata min rai don Allah. Nidai kawai murmushi nayi bance komai ba tunda gidan ba bako na bane ai duk wani abu da nasan cewa zan bukata a lokacin na dauki ba saj na tsaya nema ba a nan din. Don haka koda ya iso a nan ya samemu don tun yana can ta kirashi ta gaya mashi umurninta haka yasa daya iso ya nufo nan din ashe saida ya biya can ya aje duk wani abu da baison ya kawo masa fitina kafin ya iso nan din ya samemu don tunda ya tafi bai dawi ba sai a daren sunan komai a waya aka shirya yadda za ayisa a taron dashi. Ina zaune ina bawa yaro nono mama tana zaune kasa tana cin abinci muna hira mukaji muryanshi suna gaisawa da iya a falo ya gama ya shigo suka fara gaisawa da mama har yake tambayanta ba dai matsalan komai ko a nan ? Ai ba a rasaba yanzu dai ai gashi an kwaso mata maijegon an kawo mata bari muga iya gudunta kuma dubu kam lamarinta sai addu,a gaskiya. Kibar yarinyar nan ta zauna dakinta ayi suna kin kafe sai ta dawo gudan nan agabanki nan ayi komai ko anyi nan gabata zata iya hana komaine ni ban sani ba ? Ba komai iya gara da aka dawo din nan zaifi sakewama don can karshe a bata mata kayanta da sauran abubuwa ba daida anyi suna gobe saita koma ba ? Akace maka nifa nasan dubu nasanta sarai yanzu zata iya cewa kuma sai a bari har wani lokaci sam iya hakan ya zama takurawa ai idan anyi suna su koma can kawai zaifi nan banda tsegumi me zata zaunayi kuma ? Daga kofa mama data mike ta fita ta saka masu baki tana fadin tunda anyi suna me kuma za a tsayayi nan kuma ta koma dakinta kawai mana tunda ba wani wanka irin na da can yaran yanzu keyi ba ai. Shina gani mama an daice sai tazo nan anyi suna tunda nan kowa yake anzo gobe da yamma idan an watse zan mayar dasu gida insha Allahu. Ya gama dasu ya shigo muka gaisa nan yake tambayan lafiyan mu dana yaro nace Alhamdullahi ba inda ke maki ciwo kuma yanzu ko ya tambaya nace naji sauki sosai ai. An kawo dinkunan naki nace ehh tun jiya anty salma ta ba driver Aminu ya karbo a gareji good ina hanya na tuna wallahi na sake fadan ankawo ai. Ya dan tsaya mukai hira kafin yai muna saida safe ya fita don gidan akwai baki da zasu kwana ga yaya barakha da sukazo daga zamfara ita da kawarta. Wai dan shigan da yayi ya jima hakan ashe ya zamo laifi kuma wai anshiga hakkin madam Saiba saida sukai fadan hakan a cikin daren nam dashi yayi mata tas . Don harda cewa tayi ana tauyesu ana nuna masu banbamci ga komai yazoyi saiya nuna bambamci a kaina ya fifitani dasu don me zai yanka saniya a hada wajen bukin. Nan yace koda sunan Buhari ban yanka shanu ba ko wanan ne zakiwa bakinciki kuma koka yanka ai baikai wanan girma ba yake fadin. Ooh ashe ke diyar sarkin fawane ban sani ba har kin fita kin duba shanun kinga wanan yafi girma ko to komai da sa,anshi yake zuwa ina dashine yasa na sayi babba. Ai Allah yana ganinka duk zaluncin da kakeyi da fifitata akan shi kuma zai saka muna wallahi tunda haihuwa ai baifi haihuwa ba ? Wanan yakawo masu fada sosai ya gama ya shige dakinshi don akwai gajiya a jikin yasa ya rufo dakin da key ya kwanta bayan ya gama komai don ko abinci ita mai fadan bata aje mashi ba. Koda ta fahinci ya kargame kofan dakinsa hakan ya kara bankata mata rai kuma dakyat taga safiya a ranan ba abinda ke damun ta banda irin yadda labari yazo masu cewa katon shanun da jafaru ya yanka a shagalin. Akan shagalin sunan da sukaiwa ikirari da farko haihun rashi saiga ubangiji ya sauya abin a lokaci gashi yaya Auwalne jagoran abin ba wanda ya isa ya kawo mai raini akan zancen aikin da akeyi din. Kamar yadda jafar yace ayi da naman hakan akayi kowa don an rabawa yan unguwansu makwabta na kusa dasu sadaka kana ya aika gida gida dukka tan uwa dake cikin gari asa albarka. Kafin abinda ya rage ya aiko da wanda zayi aikin shagalin dashi nan gidan mama sai abin ya bakantawa mama rai sosai don me Auwal yayi bugun gaba da abin danta haka bayan gasu ga tan uwasa zai shige masu gaba. Allah ya taimaka yaya barakha ta iso lokacin ita ke fadin mamanmu yaya Auwal nefa wallahi kina cewa wani abu yanzun nan duniya zatajiku dashi. Gara ki kama bakinki tunda shine a matsayin babanmu a yanzu shine babba kowa na bashi girman shi yau don danki ya yanka shanu yaya Auwal ya raba zakice baki yarda ba da hukuncinshi. Aishi jafar yasan me yakeyi da yake sakasu gaba a komai nasa mutanen nan duk da yan ubanci da adawan da suke nunawa a garemu basu yarda sun nuna cewa muba yan uwansu bane. Komai namu ya tashi suna gaba sunayj gwargwado yadda duk wani dan uwa zai tsaya yayima a cikin gata tanzu akan wanan abin saiki nuna ke baki yarda ba. Ke kuma Nusaiba zan fada maki wani magana da baki sani ba akan yan uwanmu uban mu daya dasu dukkan mu kuma a tare kika zo kika samemu muna zumuncin mu. Har idan ba zakiba mama shawaran alheri akansu ba to don Allah ina tokonki da kiyi shiru ki daina kawo mata tsegumi tunda kinsan tana daukan zancenki kada ki hadamu fada da yan uwan mu don Allah ? Ubanmu ya mutu ya barmu a tare dasu kada kiyi sanafin raba wanan zumuncin namu don kin zama mai yukan yanke zumunta ke ? Nina gane a yanzu tunda kika shigo gidan nan lamarin mama ga baki daya ya sauya wallahi a,a anty barakha kada kiga laifina mana don Allah ? Kafa biyu da kayan ciki fa aka kawo gidan nan ba dole inyi magana ba ace an yanke shanu wanan kadai za a kawo muna ayi komai dashi ? Kuyi amfani da iya abinda kuka gani mana wai tsaya ma in tambayeki kokin manta da bakece mai haihuwan ba waib? Don ita data sha wahala ta haifi danta inma korafi itace ya kamata ace ta fito tayi wanan tsegumin baku dai da yunwan wani nama ko wani dangin abinci a cikin gidan nan to ki bari ayi taron nan lafiya don Allah yadda ya tsara abinsa a tafi a hakan yafi ? Gaskiyane dai baku so ni tsoron Auwal nake ji baby bani tsoron Auwal balle uwarsa karane kawai nake masu tunda suna muna suma . Ni dai na fada maku kada ayi wanan zance in kuma kince sai kinyi zakiga abinda zai biyo bayan hakan muna dai zaune kalau dasu don Allah mama kada abin duniya ya rufe maki ido kuma yanzu. Wallahi maman mu yanzu ya kamata ki natsu girma ya kama komu da kuka haifa muna kawar da idon mu ga abinda mukasan ba hirminmu bane a yanzu don Allah ki barbin ta yaran nan suna bata maki suna. Ita mai haihuwan haka kuka sakata gaba da abinda ta haifa dakinkine fa ya ajeta itama ba wani bare ba wace tafita gidan nan yadda kowa yazo aure haka itama tazo aure danki don Allah mama ki bari ayi wanan abin lafiya a watse lafiya kada aji bakinki ga komai don Allah ? Kin daice sai nan za ayi suna yaran nan basuki ba sunzo nan din babu jayayyan komai don haka kada inji bakinki ga komai don Allah ? Wanan yasa dole ta kyale batayi fada ba da Saiba ta zugata wai an kwashe nama an kawo masu kadan a gidansu tunda so tayi akawo shanun gaba daya a nan gidan. Yaya barakha kuma a yanzu nagama da ita tana bayana akan diyanta don da sukazo bukin saratu suka kwana gidana na kwaso duk tsofin kayana na basu ga Aminu dake karatunshi yanzu ta sanadina idan ba butulu ba ai hakan dole ta soni ? Washegari kuma tunda safe da nayi wanka na saka wasu atamfar super cikin wanda da akayo min