Sashe 1
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
MARFIN JALLO,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Hayaniya irin na babban gida shine ya tayar da mama daga barcin data dan samu ta runtsa na safe ,bayan idar da zikirin safe data sabayi a duk safiya .
Wanan dabi,an kusan ya zama mata jiki akullum idan ta idar da sallah zata zauna tayi zikiri har sai rana ya foto sosai kafin ta dan kwanta ta ba ido hakkinsa.
Daga inda take kwance din tana jin yadda yaran gidan nasu da manya ke kara,kaina a tsakar gidan kusan hayaniyar babban gidan nasune ma ya tayar da ita a lokacin.
Salati tayi tana dagawa a kasa inda take kwance saman sallayanta ta dan jima a zaune don gargadin likitoci dake fadin.
Idan ka tashi tsaye barci kada kayi saurin mikewa tsaye a lokacin don min a daidai lokacin jinin dake kwaranya a zuciya bata gama sauka ba yana yuyuwa ka mike hakan ya ja maka matsala a rayuwanka a cewarsu.
Ana son Sai ka dan bada yan mintuna a zaune kafin ka mike tsaye don kariya ga lafiyan ka a lokacin wanan dokan da mama taji illanshi.
Baga yaro ba baga babba ba dokace da likitoci suka bayar don gujewa fitinan lafiyan jikin bawa daka iya haifarwa mutum ciwarwutan zamanin nan .
Hakan yasa wanan boyar Allah ta rike wanan akidan ta dan bada lokaci a wajen zaune daidai lokacin da aka turo kofan dakin nata tare da daga labulen dakin aka shigo ciki da sallama muryan danta na ukkune yake sallaman tare da fadin ashema baki tashi ba mama ?.
Daidai lokacin ta dago kai tana sauke mai kallo tare da fadin na tashi Habu badai har rana tayi hakaba kuna shirin fita ?
Rana tayi mama yanzu kusan karfe takwas da rabi ake nema zuwa nayi muyi sallama don yau balaguro zamuyi har wani kasan ba lalai bane mu dawo a yau ko gobe saidai kun ganmu dai zance.
Kallon mamaki take binsa dashi tana fadin haba Habu wai sau nawa zan maka fadan irin haka don Allah ?
Mutum zaiyi tafiya mai nisa irin haka bazai fada a gida ai masa addua ba ka raina da dan adduan da muke binku dashi ko yaushe ke nan ?
Zaune yakai saman kujeran dake gefe ciki da kaya yayiwa kansa wajen zama a gefe yana fadin mama muko muka san amfanin adduan ku akan mu don duk abinda muka dafa muna ganin alheri a cikinsa.
Murmushi matar tayi tana fadin yanzu dai ina kuka dosa Habu ko kudun zaku kuma yau dinma ?
a,a mama wajajen Camero muka dosa wajen wani taron gargajiya da za,ayi a can kinsan aikin mu ya kumshi hakan sai munje don dauko rahoto.
Shine zamu dauko rahoto akai da zamu yadawa al,umma su gani ikon Allah yanzu habu har camaro zaka hankalinka kuma a kwance ?
Batare daka sanar da mu ba sai yanzu ka shirya tafiya kazo kana fada min Habu ?
Wai meyasa kudai maza baku mayar da tafiya a bakin komai bane wai ?
Kako san nisan dake tsakanin zaria zuwa camero ? camero din nan da kake ji kawai a baki tafiyace mai nisa fa daga nan .
Ya amsa da fadin kuma tafiyan mota zamuyi mama saboda kayan aikin mu dole mubi mota zuwa wajen taron wanan yasa zamu tashi tun yau ai a dai muna addua muje lafiya mu dawo lafiya.
Insha Allahu lafiya zakuje ku dawo lafiya Abubakar alherin dake cikinsa ubangiji Allah ya sadaku dashi sherin dake cikin tafiyan kuma Allah ya nisantashi daku alfarman Annabi da alkur,ani ya amsa da amin cikin jin dadin adduan mahaifiyar tasu a gareshi.
Sallamu Alaikum ga nakiyar baby muryan wata dattijuwa dauke da kwala a kai data shigo babban gidan Alh talle din ta tsaya daga kofane ya karade gaba daya gidan.
Daga can dakin mama din inda take bankwana da danta taji muryan wanan matar cikin mamaki take sake zancen da sukeyi da dan nata.
Cikin mamaki take fadin nakiya kuma da safen nan ?
Har yakai a fara tallan nakiya gida gida haka me mutane ke nema da bindan kudine wai nakiya dai a sanina sai bukin aure ake nakiya don ango.
Murmushi Abubakar yayi yana fadin barin inje mama kada in makara abokan tafiyana suna kirana tun dazun.
Nan uwar ta dago tana fadin kaje kuyi sallama dasu hjy kafin ka tafi bana son irin korafin su na baka sallamesu ba din nan.
Insha Allahu ya fada yana mikewa tsaye barin dubasu in dawo mama ya fada yana mai barin dakin cikin kuzarinshi irin ta namiji mai jin lokacinsa.
Dakin hjy babba ya nufa ya gaida ita tare da fada fada mata inda suka dosa a ranan ba yabo ba fallasa tayi mai Allah ya kiyayye hanya.
Ya fito yana kokarin shiga wajen hjy Nana ya hangosu gaban wanan matan dake faman kwada sallama suna leken wani abu a cikin kwalan da matar ta shigo dashi.
Hakan yasa ya doshi wajen saura kiris ya karasa yaga yara da manya sun watse wasu harda faduwa kasa don tsoro ga ihun da sukeyi suna neman inda zasu shiga saboda firgici .
Wanan ihun ya dakatar dashi yaja ya tsaya yana binsu da kallo fuska daure kafin ya mayar da hankalinshi wajen matar da sai murmushi take a fuskanta.
Lafiya boyar Allah tace nakiyar babyce na kawo masu gashi kuma sun watse sun barni dashi .
Kallon matar yayi cikin mamaki murmushin yagani a fuskanta yasa ya karasa wajen yana kokarin kallon kwallan dake gabata bude.
Ido ya runtse lokaci guda don wani katon maciji kalan da sai a cikin film yake ganinsa.
Ya nade a waje daya ya cika kwallan har baki sai kansa daya dora a saman jikinshi yana kiu kiu da idanuwansa dake bude.
ALLAHU LAH ILLAHA ILLAH ANTA SUBBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZULLUMIN ya ambata a fili .
Muryan matar yaji tana fadin kada kaji tsoro kai namijine kuma sadauki ba asan maza da razana ba sadauki.
Daga can bayanshi yaji muryan dayan kanwarsa tana fadin yaya Habu kada kaje kusa don Allah macijene a cikin kwallan nan babba.
Jin sunansa da aka ambata yasa matar fadin Garba sadauki garba gagare kai sadaukine ko a fagen fama kafiran makka sun buga sun barka sarki rikon amana mai alkawari ya cika har bayan rai,,,,,,,,,,
Dubu biyu ya zaro a cikin aljihunsa ya mikawa matar takai gwiwa biyu tana zabga mashi addua da neman tsarin ubangiji gaba da bayanshi.
Ya juya da niyar komawa dakin muryan hjy Nana yaji tana fadin boyar Allah aida kin fada kwai a miko maki abinda Allah ya hore ki tafi .
Yayin da matar tacigaba da fadin da yardan Allah kayi gaba saudaki sara da sassaka bai taba cima a rayuwa insha Allahu sai dai makiya su buga su barka.
Mama data samu ta mike don ganin abinda ke faruwa a wajen taji yadda matar kewa danta Abubakar addu,a ta fahinci kudine ya bata yasa ta dauki dari biyu ta fita ta mikawa matar nan ta dasa sabon addua kuma tanawa mama jam,i ga duk zurianta.
Ta dauki kwallan ta tafi don taga sauran iyalin gidan basu da niyar fitowa balle su sallameta saida sukaji fitanta suka fito suna mayar da ba,asin zancen a tsakaninsu kowa na fadan abinda yagani a cikin kwallan hankali tashe.
Mama dai bata gani ba amma ta mikawa matar sadaka don tasan wanan matar banza ba zai fito da ita gidanta haka basai neman rufin asiri da taga wanan hanyarce mai sauki a gareta.
Zancen mai nakiyar ya hana su mayar da hankalinsu ga Habu da zaiyi tafiya don da tsegumin tafiyan shi za,a fara sai Allah ya fabeshi a ranan dan shigowan wanan matar mai yawo da macijin maisa a cikin kwala tana cewa ga Nakiyar baby.
Idan kuma tasan sunan wani gida a gidan zata ambaci sunan maishi tace ga nakiyar wani sai wanan abin tashin hankalin da mamaki ya tsaya masu a rai har mahaifiyarshi ta fito rakiyarshi da iya kofa ta tsaya tanawa danta fatan Narsara da Allah ya tsare ya kare wamda sai lokacin hankalin hjy babba ya dawo garesu.
Daga kofanta take tambayan yau Habu kuma ina za a haka tunda safe ni yazo muna gaisawa hankalina yana gun wanan bakar matar data tayar muna da hankali da safen nan.
Daga kofa mama din take bata amsa da camero suka nufa lokaci guda matan da yara dake wajen suka amsa da fadin camero kuma ?
Wasu na Allah ya tsare wasu kuma sunyi gun suna zancen zuci inda sabo ta saba da hakan zaman gidan yawane duk yadda kayi sai wani yaga bakai masa daidai ba irin wanan zaman.
Ya fito daga cikin gidan yana kallon agogon hannunsa saboda ymshi kansa yasan da ya makara saidai dole su jirashi sai yaje wajen aiki inda zasu hadu.
Kamar daga sama yayi ido biyu da wanan matar ta sauke kwallan macijinta sai faman murmushi take zabga mai a fuskanta kai ya kawar da sauri yana barin kallonta.
Habu bakari don ka na tsaya nan duk da dai shigan tsugula zan ma tunda na kula sauri kakeyi ka kula da addua don kai din kana tare da tsarin Allah ga kuma tarin mahassada a tare dakai.
Nagode mama ya fada yana kokarin wuce ya sake jin muryanta tana fadin ka kula sosai don alherin ka da nasara yana inda ka dosa .
Kudi dai wanan matar keso gareshi ya nasa hakan a zuciyarshi ya sake cusa hannu a aljihu yana dauko dubu daya ya mika mata.
Murmushi tayi tana fadin wanda kabani dakai da mahaifiyarka nagode maku Sarkin da akaiwa ya sani.
Naso magana da mahaifiyar ka saidai gidan ku gidan yawane dana fada mata wani magana amma ba laifi idan tana son ji ko kai ina can gidan hjy indo mai kosai a nan na sauka.
Allah ya tsare ya kare ya amsa da amin yana aje mata dubu dayan da taki karba a hannunta saman kwallan yasa kai ya tafi don ya dauka zancen shirme take masa a lokacin don kawai ta yaudareshi yasan halin mutanen yau da yaudara.