← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 306

Sashe 181

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajena muna magana kafin suja mota su tafi maigadi ya tareni yana fadin ashe abinda ya faru ke nan ? Yaso ya bisu zuwa asibitin sai yaga ba kowa a gidan Allah ya bashi lafiya ya tada kafada na amsa da amin nashiga ciki. Habi bata gida nasan tana gidansu donshi na shiga dakina kai tsaye wanka nayi na fito na gyara jikina a yanayin da nake ciki banko tuna da abinci ba a ranan . Tea na hada da niyar insha kada in kwanta da yunwa saidai na kasa shan koda rabin kofi ne a lokacin don bakina da nake jin ba dadi. Ina ganin kamar ko wani lokaci zasu iya kirana suce min ya cika a yadda na barshi din ga gidan ba kowa sai hakan yasa tsoro ya kara shigana duk da maigadin mu yana daga wajen gidan a lokacin falo na dawo na zauna a cikin zulumi ina jan tsabaha tare da tunanen yanayin da yaya din yake ciki. Daga karshe dai na mike na rufe kofa na koma cikin daki bayan na kashe wuta ko ina a gidan ina cike da zullumi a zuciyana. Alwala na dauro nazo nayi sallah nafila nakai wani lokaci ina nemawa yaya sauki a wajen Allah kafin dan barci ya saceni zuwa dare kuma na falka ban kara runtsawa ba har safe ina idar da sallah na fito zuwa kitchen abinci lafiyayye na hada inda shi kuma nayi dabaran dama mashi kunu ko za a samu ya dan sha. Karfe bakwai har nayi wanka nashirya na fito na kulle gidan na doshi asibitin gabana sai faduwa yakeyi. Tunane kan nayisa kala kala a zuciya yau idan na rasa yaya yaya zanyi da rayuwata ina zan shiga a duniyan nan mutumin da nake mafalkin shimfida rayuwa mai inganci dashi nan gaba gashi kuma Allah ya jarabeshi yana cikin halin hau,ula,i a rayuwansa yanzu. Zance nice ta farkon isa kota biyu na samu su yaya na ciki suna tsabtace masa jikin daya bata Allahu akbar bansan lokacin da kuka yazo min ba. Sammakona yasa na samu daman shiga gurinsa kai tsaye yana kwance kamar yadda muka barshi dai a jiyan dan bambanci sun sauya mashi kayan jikinsa zuwa jallabiya tufafin nasa da suka cire mai yaya isah ya miko min na karba. Iya tashigo tana fadin ga abin karyawa nan tazo muna dashi shikan ai ba abinda zai iya ci a hakan da sauri nace na dama koko ko zai dan karba a gwada a gani. Shawaran hakan suka karba na hada kunun na dan fifitashi saidai mazane sun rasa dabaran da zasuyi su bashi. Nice dai cikin karfin hali na gwada karban kofin a hannun yaya na doshi gadon ina sunkuyawa nace sannu yaya ya karfin jikin kuma Allah ya bako ikon cin jerabawan nan . Suka amsa da amin amin yaya ka dansha koko gashi na dama maka koda kadan ne don Allah cikin ka babu komai a cikin sa cikin ikon Allah sai yai kamar ya lumshe idanunsa a lokacin. Na dibo na fara dan dago kansa a hankali ina dura mashi kokon yana shiga cikinsa har muka samu ya dansha kamar spoom biyar haka dai suna fadin Alhamdullahi wanan dabaran yayi kuwa na shan koko din. Iya ke fadin aiko yunwa ya isheshi mutum kwana nawa cikinsa babu komai a lokacin su mama suka shigo dukkansu da kishiyoyinta aka fara gaisawa. Yaya Auwal ke fadin amarya tayi dabaran bashi koko ko zaisha gashi ko mun samu cikin ikon Allah ya dansha din sai mama tace nima nayi tunanen hakan a raina. Nan yan uwa suka fara cika dakin da abinci da kayan dubiya ina zaune a gefe takure har kishiyoyina suka iso saidai su Maria sun rigasu isowa tana fadin mun biya mu daukoki maigadi yace muna kin fito tunda safe ai. Kafin na amsa iya ke fadin zuwata ai yayi muna rana tunda an samu ya dansha kokon data damo mashi ta bashi ya karba sosai yasha. Irin maganganun nan da ake fada akaina mai kamar da ana yabona shine ke kara hadasa min kiyayyana a zukatan wasu a wajen irin kishiyoyina da su Saare dake gani iyyye iyye ne kawai irin nawa da son nuna ni din watace datafi kowa. Itako iya kamar zuzuta zancen takeyi a lokacin don suji haushi don sai kara cusa magana takeyi tana fadin ai ko dazun da yarinyar nan ke mashi addua ya karba. Muryan ya habune ke tambayan kawu ya fito akace bai karaso ba tukun yace iya tazo suka fita ashe zancen zuwa wanan wajen yai mata. Take fadin ya kamata kan aje din aiko wancan karon banso ya tafi tafiyan nan basu je ba amma da yake Dauda munafukine sai yakawo uzuri ga tafiyan yace wai yana gudawa lokacin. Koma dai meye yau din nan iya nake son muje din don nayi mafalki jiyan nan ba dadi wallahi ciwon nan haka zaita bibiyan mu bawai Jafar kadai ba kowan mu sai hakan ya nadesa idan har ba a dauki mataki ba. Ga zancen nan ba kowa ya kamata yasan dashi ba tunda ba zancen da za a fito a fada a fili bane har wani yaji abune daya shafe mu mu kadai wanan. Amma saidai naga kamar dole a fasa din don yau idan kawu ya kawo min uzuri wallahi za a jimu dashi a wajen nan wanan yasa na kiraki iya. Wanan shine daidai na rasa me dauda kewa noke noke ga zuwan nan gashi har ankai ga yadda ba ason akai din dole kayi masa jam ido ko zuwan zaiyi amfani a dace. Har ya juya ya dawo yana fadin sai kuma kula dashi ina son aba Rahama daman hakan ta dinga bashi kulawa idan tana kusa tunda yana jin muryanta yana bada responding kinga hakan ai alaman saukine. Shina fada jiya da dare ko yau kuma muga alama hakan don tabashi koko yasha da kanta hakan za ayi yanzu dai idan mun dawo idan babu cigaba nan asibiti sai mu koma gida dashi iya. Aje ayi na gargajiya a gani don ko lokitan nan dan Zamfara shawaran daya bani ke nan jiya yace abin nasa kamar akwai sihiri a cikinsa din haka sai mun hada dana gargajiya. Kawune ya doso wajen da matansa biyu sai dan amaryan nasa dake dauke a hannunsa iya ta kallesu taja tsuki tana fadin babu komai yanzu a cikinsa banda tabara akan wanan auren da yake ganin yayi. Suka karaso suna gaisawa tare da tambayan ya mai jiki din yace da sauki zai shige iya race barsu su shiga kaika tsaya muyi magana dakai ke hansatu idan kin shiga yi min magana da Dubu ina nemanta nan. Lokacin ne kuma muka fito dakin nida maria muka kebe muna magana dan nisa dasu sosai saidai jin yadda ya habu ke daga murya yasa hankalin mu ya koma akansu. Duk da bamu ji sosai amma na fahinci zancen tafiya sukeyi nasan kuma can din inda nakwana da tunane suke shirin zuwa. Sai lokacin nakewa maria bayanin komai tayi mamaki kwarai dana san hakan nace shiya fada min komai wallahi kamar yasan hakan zai faru dashi har dalilin dawowan iya wajena saida na bata labari. Take fadin kinga bambancinsu da ya Habu ke nan shi bai zama ya fadama damuwarsa ko wani abin rayuwansa saidai yayi tayin abu noku noku a zuciyarsa. Ya habu din ne yazo ya wuce mu a fusace ya shiga dakin bai jima da shiga ba likitocinsa sukazo hakan yasa aka fito daga dakin. Sun jima a ciki sosai kafin ya habu din ya leko yana kirana hakan yasa na mike zuwa dakin na samesu tsaye a kanshi na gaidasu. A cikin harshen turanci likitan ke fadin itace wanan ko ya amsa da eeh ya kalloni yana fadin madam sannu ko ya kuma mukaji da jimame don Allah wani aiki zaki danyi muna a yanzu. Muna son kiyi magana da maigida ko zamuga responding din hakan a garesa kinga in akwai improvement zamu dan gane musan abinda zamuyi mashi. Kin gane Rahama ana son kije kusa dashi yanzu ki danyi mai wani abinda zaisa ko ya dan motsa koya bada amsa ya habu ke fadin hakan a cikin damuwa. A hankali na motsa zuwa bakin gadon gabana sai faduwa yakeyi suko duk sun motso kusa sun zuba min idanu sai addua nakeyi a zuciyana. Hannunsa na koma a hankali na hada da nawa nakai zaune bakin gadon ina fadin sannu yaya Allah ya baka lafiya na shafo fuskansa sai yayi kamar ya lumshe idanunsa yana ajiyan zuciya. Great naji wani likitan ya fada a gefe ki kara yin wani abin madam wanan bahaushen ya fada gareni na lumshe ido nace dan gyara zama ina fadin. Yaya zaka kara shan koko ko abinci zakaci suna tsaye kamar sojoji sun kurawa ko wani part din jikinsa ido wanan karon da hannunsa yayi min alaman don hannun ya dan motsa yasa na kalli wajen hannun nasa da sauri danaji ya motsa din don hannaye mu suna harde lokacin. Sosai suke fadin akwai cigaba insha Allahu in bashi kunu din su gani hakan yasa na hada dan kunun koko din na fara bashi saidai wanan karon baisha sosai ba kamar farko. Suka daiyi dan bayanan su kafinsu fita zuwa inda suka fito aka barni da yaya Habu sakin dake cewa dani kada ki yarda kina matsawa kusa dashi Rahama ko yaushe ya kasance kina gurinsa . Ni zamu tafi wani waje dasu mama kila zamu kai dare bamu dawo ba don Allah ki kula kada ki yarda da zancen cewa ki matsa a nan din. Kin dai gane me nake nufi duk wanda ya kawo abinci ko wani abu kada ku bashi idan bakece kika hado mashi ba a daidai lokacin Saiba ta banko kofa tana fadin. Ai batafimu ba da za,ce sai ita kadai zata dinga shiga don ana son a nuna mu bakowa bane za ai muna haka tayi shiru don kallon da yaya Habu din ya banka mata yana fadin. Ke kin gane ba ko wani lokacine zaku dinga shigowa daki nan ba haka kuma ba ason hayaniya a wajensa donshine Rahama kawai sai yaya isah da yaya auwal aka amimce yanzu su dinga shigowa. Rahama din tafimune kome
Chapter 181 · 0% Book details