← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 306

Sashe 56

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sosai da daukata da yayi a motarshi yau. Ban ko kai karshen zancen zuci ba wayanshi ya katseni naji ya dauka yana fafin umm,humm ina jiki ta fara fada Jafar ina zaka da yarinyar nan baka fada muna ba ? What ki shiga hankalinki wallahi Nusaiba kina wuce gona da iri fa a rayuwata dolene sai na fada maki inda zani da ita ki je ki tambaya idan kin damu ? Naji ya kashe wayan yana tsoki dama nasan za a rina yadda take da zafi akanshi tunda Salima ta tayar dani tace dashi zamu tafi gaba saida ya fadi nayi wanan tunanen da sai wani abu ya faru kan hakan gashi kuwa. Tsuki ya kara ja yana lalubo wayan daga inda ya jefata da farko ya dauko yana tuki yana neman lamban da yake nema a lokacin. Can naji yace mama wallahi idan Nusaiba bata yi hankali ba yau din nan saina saketa kafin ta bata min suna a banza. Banji me uwar tace dashi ba naga ya kashe wayan nasa a hasale yana faman jan tsuki akai kai saida muka tsaya gida mai a kaduna ya tsaya magana da wani kafin ya dan sake. Hanya muka kama sosai inda barcin azumi yake dan dibana a wajen lokaci lokaci saboda sanyin AC motan nasa daya sake . Maganan Salima ya tabbata don ganin mun shigo Abuja ga signboard din THIS ABUJA baro baro a jikin allon shiga iyakar Niger da Abuja din. Wani unguwa zakije ya tambayeni ba tare daya kalloni ba na amsa da maitama kinsan gidan ke nan zaki gane na amsa da ehh . Har yayi shiru naji ya kara fadin idan ba zaki gane ba ki kirasu a waya suyi maki kwantace nace banda waya amma zan gane gidan. Cikin mamaki ya juyo da kyau ya dubeni yana fadin baki da waya fa shi Habu yana me da basu saya maki waya ba ? Shiru nayi don ko da zan taso saida mukai zancen waya da yayata da salima kuma har Salima tace zata ban karamin wayanta bansan meyasa kuma ta fasa ba. Shiga wanan lungin fada wanan muka isa wani katafareb shago yaja ya tsaya ya dauki abu naji yana fadin ina zuwa jirani kadan in dawo don Allah . Ya fita lokacin na sauke ajiyan zuciya a hankali ina bin wajen da kallo shagone babba don jama,a sai shiga da fita sukeyi a wajen. Can na hangoshi da ledoji kusan ukku rike a hannunsa ya nufo inda motarsa yake ya bude ya baya yana aje lodejin aciki kafin ya juya zuwa gaba wurin driver ya bude ya shiga. Sorry na dan dade a ciki na barki zaune bakomai yaya saida ya zauna da kyau ya dauki hanya muka bar wajen hanyan maitama naga ya dauka kai tsaye. Ajiyan zuciya na dan sauke an karaso gida ko naji ya fada na danyi murmushi ban dauka yana da saukin kai irin haka ba. Wancan layin na fada ya mike zuwa layin dana fada muka shiga dab tafiya kadan nace wanan gidan mai bakin get nan din gidansu hjy mamace daga waje ya tsaya ya juya yana dauko ledab a bayan mota naga ya fitar da waya sabo dal a kwalinsa ya fara duba lambobi a cikin wayansa yana lodawa kafin ya miko min wayar yana fadin layin mama dana Salima saina habu suna saka maki . Saida na dan dubeshi nayi kasa da murya ina mika hannu nace nagode yaya Allah ya kara arziki amin yace a uzurce da alama sauri yakeyi a lokacin. Horn yayi sai ga wani dogon sauriya ya leko yana duban mu kafin naji yace daga Zaria ko nace ehh sorry duk basu gida sun tafi umura last week amma anty salma tace idan kin iso a kaiki gidansu . Sai lokacin naji zuciyana ya dan sake da har nashiga vibration inane gidan nata yake naji yaya ya fada tana Aso rock muje ka nuna min ya fada. Saurin yace ga mota nan da tace in kai ta sai naji yace. No muje dai ka kai,mu naga gidan na ajeta baiki ba naga ya juya ya fito da mota muka bi bayanshi har gidan anty Salma din. Duk wanda yaji ance gida a Aso yasan ba karamin gida bane ke nan za a gidan ya hadu iya haduwa mijinta wani babban dan kwangilane mutumin maiduguri. Gaeinsu daya asalima yan uwa suke dashi itace matarshi ta biyu yanzu anty salma yaranta biyu dashi bayan barin mune akai aurensu dashi mun dai sanda zancen auren kafin Allah yaiwa mahaifin mu rasuwa mu koma gida. Ko kuma Allah na tuba ka yafe min inji mata gashi kuma zan fada ince Baffa ya cinyeshi don shi yai sanadin barinsa duniya duk da lokaci yayi dama. Tsayar da motar yayi yana fadin kice min gidan manya kikazo dama murmushi kawai nayi ina mashi godiy. Ledan ya dauko daga bayan mota ya cusa kudi a ciki ya miko min yana fadin rike wanan inda matsala ki kira gida a zo a daukeki . Na amsa da godiyana na fito daga motan ya fito ya bude baya aka fito min da kayana zuwa ciki ban shiga ba saida na kara mashi godiya naga tafiyansa na sa kai zuwa cikin gidan. Ina shiga saiga anty salma da gudun ta muka rugume juna da ita a cikin murna kafin ta sakeni tana fadin wai Ramaah tace nan haka ta zama yan mata ? Nayi murmushi ina fadin nice anty muka kwasa zuwa cikin gidan nasu tana nuna min kauna don haka muke da ita tun ina karamata . A zaria motarmu na dagawa ta juya zuwa part din su mama a hasale take babu ko sallama ta fado masu a falon ta samu kowa a falon zaune. Mama tana ganinta hakan hankali tashi ta soma fadin Nusaiba lafiya kuwa na ganki a haka hankali tashe ko wani abu ya faru ? Babu komai mama dama karan J na kawo maki mama ta dan sake kallonta tana fadin jafar kuma me kuma ya hadaku dashi ? Mama din ta tambaya cikin kulawa don ta kwantar da hankalinta tayi mata bayani yadda zasu fahinci abinda ya hadasu . Mama don ya dauki yarinyar nan Ramaah ina tsayar dashi zanyi magana amma J ya daka min tsawa ? Bai saurareni ba ina ruwana da inda zai tafi da ita tunda da ai an,san ya dauke ba a hanashi ba saboda ita zai dinga muna wullakanci haka mama ? Haba yar nan ki saurara mana kada kiyi furci irin haka ga mijinki don Allah koda kika ganshi da yarinyar nan Rahama hanya ya rage mata ai. To don me ina tsayar dashi in fada mai yarinyar nan jikinta yana zafi amma yaki tsayawa saboda Ramaah zai min wullakanci mama ? Point of correction ki gyara zancen ki kwarai da sanin su ya dauki Ramaah zuwa Abuja kada ki tsaya boyewa don kinj zafi ya dauki wata a tare dashi salima ta fada a hasale. Ki barta tayi maganan ta mana ke ina ruwan ki salima wajen mama tazo fa ba wajen ki ba Saare ke fadin hakan . Dole inyi magana don mu ba yan iska bane da kike son fadan hakan a gaban mama tana fadin wai saboda Ramaah ? Kinzo nan ne kiji dai ina zai tafi da ita to Abujan daya nufa can zai kaita gidan yan uwanta a can zatayi sallah In kuma ya Habu daya bashi ita yakai yaji an juya wanan zancen wallahi mama rai zai baci sosai a gidan nan don sai yaba kowa mamaki matakin da zai dauka kowa kuma yasan hakan . Kada inyi magana ita din muharamince halan da zai dauketa daga shi sai ita a mota da zakice kada inyi magana mijinane fa J dole inji dalili ? Mijin kwace ba da kika kwace wa kawarki mijin har zakizo nan kina kokarin karantawa mutane hauka kega mara kunya don ana kyaleki ? Wai Salima me kike nufi da bazanyi magana ba naga kamar dama kina jirace dani ashe ? Jinan Nusaiba tunda kinji abinda ke nan sallah yarinyar nan zata Abuja tayi gidan yan uwansu shine habu ya hadashi sa ita ya sauketa banga abin hayaniya ba a nan ? Mama niba hayaniya nazoyi ba kawai dai nazone in fada maki abinda yai min akan Ramaah saiya dinga nunawa mutane banza muke mu ? Wasa wasa zancen dai ya koma na Salima data gaji da halin Nusaiba fada sosai sukayi a gaban mama tana zagin Salima din don me zata hanata magana a kan gaskiyarta. Hayaniyan su ya fito da ya Habu daga part dinshi yashigo yana fadin wai meke faruwa hakane meye haka ga mama zaune ga iya kuke wanan abu haka ? Sam bata san yana gidan ba ta dauka ya fita ko bai gari ta don basu sani idan ba sun gashi ba tasan waye Habu din bai dariya da kowa a gidan balle aje ga wasa . Nace meya faru duk sukai shiru ya juya wajen Saratu yana fadin ke Saare meya hadasu fada da safen nan haka ? Bafa fada bane ita Nusaiba tazo wajen mamane da magana shine ,,,, Yaya zakice ba fada bane ita mama din sa,artace da zatazo tana fada akan ya J ya dauki Ramaah a motarsa salima ta tare Saare dake kwana kwana da zancen tana kokarin dora mata laifi. Kai ya girgiza cikin takaici yana fadin don J ya dauki Rahama shine abin fitina ba dan uwana bane J Rahama kuma tana zama kanwar matatace a gidan nan . So baki da right din da zakice kada ya dauketa wai ma a gaban mama kika zo kina wanan haukan ke yanzu bakiji kunyar wanan abinda kikeyi ba don Allah. Assuming nine yanzu zani kaduna saiga kanwanki zata sai ince ban daukanta don ina tsoron Maria kada ta shakeni ko ranta ya baci kome ? Ai yau naga mamaki ga yarinyar nan gara da Allah yasa kana gida ka ganewa idonka irin cin kashin da sukewa uwarku a gabanta ba zagin da yar nan bataiwa Salima ba yau don ta raina arzikin uwarku balleni ? Bazan ce komai ba sai mijinki ya dawo daga Abuja shida ya ajeki zanwa iyaka da shigowa part
Chapter 56 · 0% Book details