← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 185 OF 306

Sashe 185

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kasheki hakan ba damuwansu bane su . Kece dai din a tsaya don sauya masa tufafi ita mai fadan gashi ta kasa mashi komai amma don daurin gindin iskanci nan tazo tana muna sababi dazun . Yanzun gashi don bata da kunya ta kasa daukan kayan ta wanko ina nan iskancin nan ba zan lamunceshi ba idan ta samu dubune tana juyata yadda take so niba zata sameni hakan ba . Yaya da dai kin saka masu ido don koda kikace su sauya mai kaya ta kuma daina daga murya bakiga irin kallon da taimaki ba ? Amina na sani sarai shiyasa nake son nayi maganin rashin kunyar yarinyar nan a wajen nan tea maria ta hado min mai zafi ta ban nasha don haka mama idonta yana a kaina. Su ummah da mijinta da maria ta kira a waya ta sheda masu halin da yaya J din take ciki suka taso daga kaduna da yaransa maza biyu suka zo ganinsa. Mun jima dasu a cikin dakin yayin da saiba din tazo ta zauna ta kafemu da idanuwa saikice taji labarin zamu bashi wani mugun abinne da bata yarda da hakan ba. Koda suka fito donsu wuce mun jima da ummah tana bab magana banda kuka ba abinda nakeyi shima mijinta haka ya ban baki danayi hakuri hakan jerabawane a gareni. In dage da addua da rokon Allah ina nema mashi saukin hakan a wajen Allah inda ummah take fadin sunyi magana da Hardo yace akwai abinda zai turo muna zuwa gobe. Sun tafi ina jin kamar kada su tafi su barni a cikin wanan halin dana tsunci kaina a cikinsa don gashi ina kallo farin cikina a cikin wanan halin . Haka anty Barakha ta iso zuwa yamma itama inda tasha kukanta tare da nuna alhininta ga halinda dan uwan nata keciki nice na debo mata abinci ta samu tayi sallah ta zauna taci suna zancen da yan uwanta mata su salima da saare. Gudu kawai ya habu ke shegawa tun suna dan hira a motan tsakanin iya da yayanta har yakai duk sunyi shiru saboda tafiya da nisan wajen da suka dosa din. Sai iyace da tayi barci ta tashi take fadin kai Dauda a ina kasan wanan wajen da har kazo a lokacin ? Iya me nema ai baya ganin nisan waje idan yana da bukata nima wata yar uwar Hafsatuce ta nuna min wajen don ita wajen zuwantane a lokacin. Hafsatu ke mata hiran ita halima shine tace da za aje wajen za a dace don ba wanda yajen bai dace ba . Kinji dalilin dayasa na shawarci ita halimatu din da mijinta a lokacin don da a tare zamuzo dasu sai bai bada goyon bayan hakan ba yasa nazo ni kadai a lokacin. Saidai bayan nazo dinne na fahinci irin aikin mutanen da garama da banzo dashi ba ashe don ba zai yarda muyi irin abinda akace ayi ba lokacin. Kinsan halinsa zaice shirkane ko wani abin kaucewa hakan yasa na karbo mata baki alaikum nakai mata tayi amfani dashi Allah kuma ya kawo rabon. Kaiya rabon wahala ko tunda lokaci yayi idan akai hakuri ai samu za ayi tunda komai dan lokacine Allah ya riga yayi tana da rabo don haka ba mahalukin daya isa ya hana yaran nan zuwa duniya nan. Don ni tun a lokacin ban so irin wanan abinba dauda kaida matarka kuka kafe akan hakan har kukafi yar uwar taku damuwa hakan a lokacin Yanzu ina dadin hakan don Allah abinda a karshe ake wanan irin wahalan yaron nan Allah kadai yasan irin halin rayuwan da yake tsintar kansa a cikin sa. Yau har abin yakaishi ga halin da ba aso yanzu dadin kuke nan anyi ba ayi ba ke nan wanan abin kana ganin idan yaron nan ya mutu a halin nan zai yafe maku dauda . Iya kinsan halin hafsatu fa kinsan ta da yarda da irun abin nan balle da taji ance ba zanyi arziki ba sai yar uwata ta haihu a duniya tun lokacin hafsatu tasakawa kanta damuwa. Kaji wani shirme dan Allah diyan dubu diyan kune kai da hafsatu ko diyan Dubu ne ita da mijinta ko yanzu da sunan ku suke amfani ? Ni dama nasani nadade da sanin da manufa kuke wasu abubuwa akan yaran nan ka taba jin inda dan wani ya zamo jinin wani inba shirmen ka ba dauda ? Yaron nan Jafaru yana da kawaici yasan komai ya dade da sanin komai da kuke kulawa akansa kaida matar ka amma ya kyale yake binku a hakan . Yau na tabbarta da ba jafuru bane abin nan ya sauka a kansa haka har ya sani kana ganin bayanshi akwai wanda zai kyaleku haka a cikinsu ? Dauda kaji tsoron Allah ka daina wanan rayuwan banzan yau gashi saboda son kanka dana matarka kun jefa rayuwan mu a cikin wani hali mara dadin fada ? Yaran nan sun san komai ido kawai suka saka maka dauda saboda kawaicinsu da uwarsu ita kuma tana shirme kamar tababiya ta kasa kwantar da hankali ta fahinci hakan a gareka. Sun sani fa iya kikace kawu din ya juyo yana tambaya tace kwarai ga habu nan sun jima da sanin komai a kanka har uwar tasu sun dai kyaleku kawai ne . Zufane ya fara karyowa kawu lokaci guda da har yakai ga cire fulanshi dake kanshi yana fitara dashi lokaci guda. Kalloshi Habu yayi yana gyada kai kafin yace kawu abinda nake so dakai yanzu shine ka fada muna gaskiyan zancen nan tun a nan ba sai munje gaban mutanen nan ba ? Menene asalin abinda ya kawo hakan don Allah don a gaskiya ni dai ina yawan mafarki da wata mace kai bama mafalki ba wallahi matar nan sau biyu ina arba da ita a zaria . Na farko a gidanmu nan tudun wada ta shigo da kwalan maciji tana tallah muka bata sadaka a ranan da zanyi tafiya zuwa kasan su maria a bakinta naji cewa zan hadu da maria. Bayan na dawo kuma da kwana biyu na sake haduwa da ita take fada min in fadawa mama tazo ta ganeta tun kan mai faruwa ya faru damu. Saina dauka zance ne kawai irin na mutane don haka ban dauki zancen da muhinmanci ba amma na fada ma mama a lokacin. Koda ka fada min ai munje bamu sameta ba ta tafi mama da damuwa ya dama ta tsoma masu baki karo na farko a motan . To bayab haka ban kara tuna komai ba akan zancen sai lokacin da Jafar ya kwanta ciwonsa na farko nayi mafalki da wanan matar tana min gargadi sosai kan wanan maganan . Kodana dawo kuma saina samu J a cikin wanan halin tun lokacin na san zancen nan ba karami bane haka kuma yana cikin abinda yasa kukaga J ya auri wanan yarinyar Rahama. Don yadda matar ta fada haka ya faru bazan boye maku ba yau don boyo baida amfani ita Rahama itace tayi amfani da wani magani a lokacin da j ya kwanta wancan karon itace wace tayi amfani da daman data samu ta dinga mai amfani da wani magani na gidansu har ya samu sauki. Rahama mama ta fada yace wallahi ba wanda ya sani sai Nafisa dani a lokacin don saida ta kafa huja kada a zargeta yadda wallahi nayi mafarki akan gun Rahama za a samu maganin nan haka abin ya faru shi j ya fada min komai a lokacin. Shine kukaga yayi hanyar daya aureta ake ta zarginsa dayaci amana ya fifitata akan matanshi. Amma ai baku fada muna ba mama ta fada yace ko mungaya maki mama ba yarda zakiyi ba saima ki juya zancen ta wani tsiga tunda gashi kuna fadan sun mallakemu. Ni dama nasani wallahi nasan dole akwai jafaru ba zai amfakawa yarinyr nan haka a banza ba dole akwai abinda kuke boye muna wanan ai taimakon kaine tayi balle ace za a zargeta akai iya ke fada. Iya kinsan su wanda suka tashi wajenshi aikinsa ke nan bada magani kaf nahiyarsu asan dashi zuwan da mukayi nakaisu ganin gida lokacin dansa ya bata maganin akai dace kuma ta gwadawa jafar din yayi amfani. Dole taji tsoron fitowa fili ta nuna tana bashi magani irin haka don gudun zargin matansa shi kuma dayaga ya mike shine ya ban shawaran yana son ya aureta tunma da ita Saiba tayi masu wanan zargin suna tare saiya kasance kamar ta zugashine akanta. Aida kun fada da duk hakan bai taso ba nasan Rahama zata iya komai daka fada habu don yadda ta nuna damuwata akan shi lokaci ko ciki daya suka fito ya tsaya a hakan mamake fadi. Tacigaba da fadin na dauka daga baya tayi hakan ne don kawai ta samo kansa ya aureta tayi wanan ladabin shegu din a lokacin. Ko ladabin shegu tayi ai ta cancanci hakan don ni jafaru yayi min daya aureta kece dubu yakamata ace kin gane hakan tun lokacin. Yarinyar da bata kyamarsa bata gudun ta dauki ciwon dake tare dashi wanda matansa na sunna da yan uwansu suna gudunsa don yadda fatan jikinsa kuraje suka feso masa banda ita da Nafisan a lokacin waya tsaya ya taimaka masa bai kya macesa ba ? Amma haka kika rufe ido kina nuna baki kaunan yaran nan har jininsu kada kice ko ba a fahinciki bane har yaron nan dan wajen Habu kirikiri kike nuna laifin iyayyenshi ya shafeshi kowa kuma yasani. Yanzu ga komai ya lalace maki magani a gonan ki kin kasa tsayawa ki fahinci hakan sai bin yarinyar banzan nan da kikeyi tana cusa maki bakin ciki a banza. Idan har Jafaru ya mutu a halin nan wallahi ki nemi gafaran ubangijiki biyu don alhakin yaron nan sai ya kamaku dake da dauda bama shi kadai ba tunda alama ya nuna akan diyan kaf abin yake. Innalillahi mama din ta ambata tana fadin nifa iya ba wanda ya taba tsayawa yayi min bayanin wanan abin haka inba yanzu ba. Ni yaya ake son nayi don Allah shi yaya bai tsaya ya fada min gaskiya akan maganin ba lokacin daya kawo min balle in dauki abin da muhinmanci a raina ? Dubu laifin hafsatune wallahi kuma ba komai yasa hakan ba ta
Chapter 185 · 0% Book details