← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 306

Sashe 86

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

bai san lokacin da akai buki ba. Maria tace don bai sanki bane yasan duk kannensu ai ba zai dauka kema a gidan nan kike zaune ba aje kudin nan ki nunawa mama tunda ta dalilinsu ya baki shi. Mama kuma na fada ina kallonta tace to Ramaah ina gudun abin maganane wallahi kada yaya ya fada masu abindake nan suce kuma wani abin. A,a wallahi saidai inba yaya din inji me zaice ai dukkansu kyaleni sukayi a kitchen suka fita da bakon yazo don me zan basu nikan ba zan bata ba don tsab zata karbesu wallahi. Nafisa fa tace in anyi muna abin arziki mu daina nuna mata tunda karba takeyi bata bamu sai naji tace ke Nafisace Ramaah ? Waima ko sai yaushe zasu dawone mutumiyata naji kewanta sosai wallahi na zata kwana biyu zasuyi kawai a can ai sai gashi suna batum share kwana goma. Sun dawo jiya naji mama tana fadin ance sun dawo tana garin nan yana da wuya dama ta dawo gidan nan gaskiya don anty saare din dake gida yanzu nasu baizo daya ba. Don cewan da takeyi wai don kwadayi an mamaye komai anayi ta ina za a bari matan yaya su dawo a yanzu shine sukai fada har tayi fushi lokacin ta kwashi kaya zata koma gida saida akaiwa Saare din fada. Kingani ko dama saida nayi wanan tunanen a raina don wanan abinda kukeyi za a dauka da wata manufa ake hakan kinsan mutane yanzu da sheri. Yar uwarsu ke nan Nafisa sun fadi hakan a kanta ina gake da ba yar uwarsu ba ai sai sufi camfaki ga zancen don Allah kadai yasan irin abinda take fadawa matanshi yanzu tunda suna tare. Banjin tsoron duk abinda ta fada saboda nasan ban aikata hakan don kudi ko don wani abuba saidai ban jimirin daukan wullakaci a kan hakan yasa na kama kaina tun bata kawo kaina ba. Ita din yar uwar ya Habu banson nayi rikici dasu don yana mijinki idan nayi hakan bartabanki ne zai tabu a wajensu. Shiru tayi min cikin damuwa ta kasa ban amsa ga zancen ganin haka kawai na mike nabar falon da kudin a jikina don ba zankaiwa mama din ba kome za ayi kuwa tunda nice akaba. Ranan ya Habu ya dawo daga tafiya ya dawo da abin arzikinshi kamar yadda yake akida wajensu duk garin da sukaje zasu sayo abinda ake amfani dashi garin. Za ,a sayo azo dashi gida ayi amfani dashi saidai gajiya ya hana a raba ba sai washegari ya fito dashi daga motansa . Nice ya kira na dauka zuwa part dinshi danasu mama duk da ina kyautata zaton mama tana part dinsu ya J a lokacin. Iya na sama zaune na gaida ita da kwana ta amsa tana fadin yar nan za,ace baki gidan nan wai meke faru hakane kun dauke kafanku gaba daya da wajen nan. Babu komai iya ina nan saidai a yanzu ban faye zama ba ina zuwa makarantane kin sani ai. Kayya yar nan akwai dai abin da akai maki kika dauke kafanki haka ni zuwanki yafi min zuwan wa yan nan marasa lissafin ai ki fada min idan an maki wani abin ne na dauki mataki kan maishi . Nace iya ba komai karatune yasha min kai duk kwanakin nan sai naga ta yafutoni da hannu alaman in matso kusa da ita na je din kuma ta tausa murya tana nuna min dakin su salima tace. Ita wanan sakariya tun jiyan ta shige daki bata fito ba wai abokin yayanta take so kiji min ja,iba baki bari a nemiki ba sai kece mai neman miji don sakarci irin na saratu. Iya tana sonshine tace jam,jam ai mace takan jira furtawan namijine ba ita ta nuna hakan ba shine yayanku Jafaru yayi mata tas jiya da dare ta shige daki tana fushin banza. Ni dai na fita ina dariyanta don yadda tai maganan sai kayi dariya tana kallon labulen dakin zakice saarece a wajen tsaye lokacin. Nasan takaicin hakan tsohuwar taji yasa take neman abokin hira ta amaye abinda ke cinta a zuciya don basu shiri da Saratu sam suna konewa junan su mai ko yaushe. Ban,san ya akayi ba na dawo daga school na samu Asmau uwargidan ya J ta dawo gidan inda na gane hakan yarta dana gani tare da Abbati a part din mu nake tambayan ita dawa tazo maria tace min ita da uwarta sun dawo dazun ita ta kaduna iyayyenta sunce sai karshen sati zata dawo. Nasan suna kara shiri irin nasune don ance ba karamin shige shige suka iya ba ko wanan dawowan nasu yabawa kowa mamaki don haka kawai akaji mama tace su dawo dakunan su. Ance ya j din ya nuna bai son dawowan su amma mama tace aiba tafiyanshi sukayi ba natane don haka dole su dawo dakunan su. Sun dai muzanta na fada ina nufar dakin mu naji tace dani ga wanda yasan hakan ba ai tun karfe biyu tana gidan nan wajen salima nake jin tace Saiba basu gama shige shigensu bane a can. Amma wai mijin yace idan ta wuce gobe ba dai gidansa ba nasan zata dawo ga goben itama ke nan gamu dai gani ai duk fa sun lalace ba kamar yadda suka tafi ba daga ita har yar nata . Ban fito ba ban kcuma da niyar zuwa yi mata sannu da dawowa ina daki ko falon yar uwata kika shigo ba zaki ganin ba don ban zama a falonta sai daki saboda ya habu dake garin. Kamar yadda yaba da umurni sai gata tashigo garin wajajen karfe biyar na yamma bata dade da isowa ba ni dawo daga school motan gidansu dana hangone yasa na gane cewa Saibace ta dawo. Haka kuma na samu anty Nafisa itama ta dawo gidan nayi mamaki kwarai data dawo gidan a lokacin a zatona ba zata sake dawowa da sunan zama ba. Wai ashe shi yaya Jafar da yaya Habune da sukaje gidan suka dawo da ita nayi mamakin jin ya Jafar din ya fita a ranan zuwa cikin gari dashi da dan uwansa lalai sauki ya samu sosai gareshi tunda har ya iya fita zuwa cikin gari. Ina sallah magariba naji shigowan su anty Salima da Nafisa part din mu suna dariya ban fito ba saida na idar duk da naji suna tambayan ina nake ? Suna dariya wai iya tana can tana sakin magana hakan yasa suka gudu zuwa part din mu kafin ta hada dasu ta zage. Daga kofa na tsaya ina fadin anty Nafisa munyi fushi ta juyo tana fadin kada ki fushi Ramaah kina raina wallahi wayarkice ko yaushe mutum ya kira zaijita a kashe. Haka dai yaya yace dazun salima ta fada dazun ya kira layin ki wayar bata shiga ai yace bai ganki ba duk kwanakin nan nace kina nan sammako kiyi kina fita zuwa school. Yadda maria ta kalloni yasa na kawar da kaina gefe daya nima dai naji zancen wani iri balle yanzu da matanshi suka dawo gidan hakan zai iya kawo zargi a zukatansu.
Chapter 86 · 0% Book details