Sashe 19
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
akan wani harka da nake son fadawa shine nace barin nemi shawaranka muji indan hakan zai yuyu ? Nan ya kwashe yadda sukayi da Meiambe ya fadawa kawu din shiru kawu yayi inda Jafar din yaga yana kokarin tsugunawa kasa shima yabi sahunsa suka kai kasa din. Can yanisa yace tau malam Jafar bakin wanan abin ba son hanyar karuwace saidai ina tsoron harkan kudi a yanzu . Don rikon amana haka abune dake son taka tsantsan duk da banda shamakin hakan a kan Jafar saboda kai ko ince har yan uwanka kuna da natsuwan zuciya sosai kan duniya don gwargwado kuna da kamun kai har yau Allah ya tsare ya kara karewa babu dan daya taba dauko muna magana a cikin ku. Don haka Jafar ba zanki shawaranka ba tunda hanyace ta samu amma shawaran da zan baka shine kafin muyi komai ya kama mu binciki idan ba wani matsala ka bari zanje gidan yaya sale na kusfa na fada mai a roka muna Allah a cikin lamarin . Saida Jafar din ya sauke ajiyan zuciya kafin ya karawa Kawu haske akan yadda abin zai gudana da kuma irin yadda yake so shima a ta bangarenshi abin ya kasance kawu yace ya fahinta insha Allahu zaiyiwa yayansa magana zaiji komai da yardan Allah kafin ya tafi da haka suka rabu da kawu din kowa ya kama gabansa. Suna fita daga cikin gidan nasu ya kama fabanshi yafi ganewa wanan unguwan daya taso a cikinsa don ana kowa nasu yake wancen wajen a yanzu ya zama kamar sabon wajene garesu. Abubakar din shagon sanusi ya nufa sukai daidai da sanusi din yana shagon nasa ta sayar da waya a kofa ya tsaya bai shiga daga ciki ba duk da ya saba shiga din amma a yau daga kofa ya tsaye. Sanusi yaji dadin ganinsa sosai sai faman washe baki yake yana fadin kai mutumina kace min har kun dawo ashe tafiyan bamai jimawa bace dama ? Tafawa sukayi suka soma hiran bayan rabo inda shi sanusi din ke bashi labarin abinda ya faru cikin unguwa sai yaga hankalin Abubakar din baya tare dashi lokacin sai waya hannunsa dayake faman dannawa hankalinsa ya dauke dashi. Yasan halin abokin nasa don haka ya bashi lokaci tun safe yake faman kiran layin ta amma baya shiga sai kuma hakan ya daga mai hankali a zatonsa an karbe wayan ne don yadda yake tunanen suna cikin matsi akan hakan. Dafashi sanusi yayi yana fadin lafiya kake kuwa abokina naga kamar kana cikin damuwa niko naso na gama baka labari in fada ma riban da aka samu bayan tafiyan ka. Barshi kawai zuwa gobe idan nashigo ya fada ya juya ya soma tafiya hankali tashe har lokacin yana gwada sa,anshi ga kira ko zai shiga. Garba sadauki garba gagare Abubakar mazan fama irin ku biyu ke gyara gari kwana biyu ashe ka dawo daga tafiyan ? Kai ya daga a hankali ya kurawa matar ido yana son tuno ta kwalan kanta yasa yayi saurin ganeta ita matar ranan da sukai tafiya data shiga da maciji gidansu. Fuska ya tsuke a waje daya sai dai duk da hakan saida yaji kawai ya gaida ita don baisan wacece ita din ba da take faman bibiyan shi tambayan daya fara yiwa kansa kenan a zuciyarsa. Baabba ina wuni ya fada sai tayi murmushi tace dashi kada kaga na kulama yarona akwai abinda nake son ka sani game da rayuwanku na fadama ka fada wa mahaifiyarku inda nake ko baka fada bane yasa bata zo ba ? Yanzu haka naga hankalin ka a tashe yake don baka samu mutumiyar ka bako kada ka damu zuwa yamma insha Allahu ka gwada zaka sameta. Saidai ka kula da amana taraiyanku akwai nasara don kusan ince ka tsira daga sherin magautanka habu. Saidai yan uwanka amma a gaskiya in mahaifiyar ku batayi da gaske ba za,a dukar daku gaba dayan ku . Ka maida hankali akwai alheri da nasara daga wanan yarinyar daka hadu da ita acan saidai iyayyenta mutanen banzane shine kadai matsalan da zaka dan fuskanta. Habu yau fiye da sati fa ina cigiyan ka garin nan muryan Sabi,une abokin shi yake fadan hakan ya juya yana cewa sabi,u yaya nima ai naso ganin ka sai na danyi tafiya ina zuwa ya fada ya juya girin wanan matar don yace yagode. Saidai wayau baiga kowa a wajen ba cikon mamaki ya juyo ga abokin nasa sabi,u yana fadin ina wanan matar tabine sabi,u ? Wace mata ke nan fa sabi,un ya tambaya matar daka samemu mana magana a nan mana naga kamar nan tabi ya fada suka juya gaba dayansu har sabi,un suna kallon hanyar cike da mamakin ta. Ikon Allah kasantane ya girgiza kai alaman a,a amma dai ranan tashiga gidan mu anan taji sunana ta rike sai ya canza topic din don ba zaiso ya matsa mai da tambayan daya fara ba yasan halinsa bakinsa baida sirin rike magana. Yanzune ma zai iya juya zaicen zuwa wani tsiga ta daban ya dauko mashi zancen magana da soka soma dashi a ranan zasu hada kudi su sayi wani shago anan cikin unguwa suba da haya. Ire iren hakan yanayi sosai da abokansa na kut da kut dama yan zaria basu da wasa wajen sana,a rigima da naci kawai kanawa suka fisu 😍. Har suka rabu da Sabi,u a wajen sallah yana tunanen zancensu da wanan matar dake yawo da kwalla tana tallan maciji a cewarshi. Saidai abinda ya daure masa kai shine zancen data soma ta katse ta yaya tasan cewa yana gwada kiran layin Yanda tun safe bai samu ba. Gabanshine ya fadi lokaci guda wanan wata irin matace take kokarin bibiyan rayuwatane wai meyasa ta lake min hakane ? A iya tunanesa baiga alaman tana nemam wani abu a wajensa ba tunda bata tsaya karban komai garesa ba yauma amma kuma me take son fadawa mamane wai ? Data matsa tana son yin magana da mama me zata fadawa mama din akan shi shirme ya dauki zancen da sallon yaudara irin na mutane. Wata zuciyace ta bashi shawara ya gwada abinda tace mana ya gani idan hakan gaskiya har yakira yanda ya sameta da yamma to akwai kamshin gaskiya a cikin zancen ta ke nan yake fadawa kansa. Zama ya gyara yana fadin abu sai kace almara meye hadina da wanan matar da take son shiga min rayuwa ya akayi tasan dana hadu da Yanda ? Gaskiya dole ya sanarwa mama barazsn matar nan a kanshi kada sai abu yazo ya faru dashi ba yadda za ayi a lokacin yace zai sanar da ita daga baya. Anan cikin unguwar yai sallah magariba da isha,i yana fitowa kuma suka dauki hanya da sanusi daketa kokarin masa bayani kan shagon nasu na saida waya da kayan wayoyi din wanda ba kowane yasan da kudin habu a cikon shagon nan ba sai iyayyensu kadai suka sanda wanan. Kusan lokaci guda suka iso gida da yayansa do zakice tafiyarsu gudane yadda suka shigo din shi jafar part dinsa ya nufa shi kuma habu ya tsaya nan jikin motar yayansa yana gwada kiran layin Yanda da son ya kure karyan wanan matar don ya samu madugaran yi mata kashedi akansa. Ga mamakinsa yana kira kiran ya shiga mamakine karara a fuskanshi yaji ta dauka tana sallama da muryantan nan mai nuna sanyi hali irin nata. Kamar kullan yadda take fadan amincin Allah ya tabbata a gareka hakane ko lokacin ta fada gareshi a cikin sanyin murya daya sakashi cikin wani irin yanayi shauki. Tare dake sahibata ya fada ba tare da yashirya furta hakan agareta ba sai yaji sautin murmushinta na jin dadin abinda ya fada a gareta da Sahibata. Tun safe nake gwada kiranki baya shiga da fatan dai lafiya hakan ko take bashi amsa da fadin lafiya kalau kasan da zaran bakwai yayi muna daji muna kiyon dabbobin baffan mu nida sister . Duk da kuwa a kwai maza da yakamata suje kiyo amma mu baffa ya zaba da mu dinga fita mashi da shanunsa wajen kiyo acewarsa don mu koyi wahalan ruga da bamu taso a cikinsa ba a baya. Shi wani irin mutum ne da zai yanke hukuncin hakan yasan abinda gobe zatayi a kanku hira dai sukayi sosai dashi wanda a cikin irin hiran yake tsuntan wani abu daya shafi rayuwansu na baya ita da yan uwanta.