Sashe 27
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rayuwan aure mai tsabta suka shimfida a tsakaninsu a ranan inda yakwana yana lalashin amaryan nasa wace ya sameta da mutuncinta da kimarta na ya mace. Zamanta a daji ko rayuwan birni baisa ta zubar da kimarta na ya mace ba a waje daga shi har ita sun shiga wani hali bayan zazzabin daya rufeta zuwa safe hakan yasa ya fara tsaguwan kansa tare da tuhuman kansa dabai rangwanta mata ba. Wanan yasa daga masallaci part din iya ya nufo ya samesu a falo suka gaisa nan yake fada mata cewa Maria ce ba lafiya. Wallahi tun asuba jikinta yai mugun zafi tana kuma rufe da bargo tana rawan sanyi ko asibiti zasu tafine da ita ? Haba dai kaje iya na tafe mama ta bashi amsa lokacin na fito da tsinya a hannu na tsuguna ina gaidasu da kwana na wucesu ban tsaya ba. Tsakar gidan kamar yadda muka saba share gidansu hjy a abuja hakan na duka na fara shara. Don gidan yana bukatan gyara saboda gidan tunda akai buki ba a samu wanda ya tsaya ya gyara wajen ba ganin hakan yasa na kwana da niyar gyara wajen na fito tunda safe . Daga bangaren Anty yanda na fara na gangaro dayan part din da babu kowa a cikinsa har zuwa part din wa yan nan matan dana shiga jiya nakai masu abinci. Duke nake na shagala naji mutum a kaina yana gaidani na amsa kafin na duka ina gaidashi farine dogo yana saye da jallabiya a jikinshi suna da kama sosai da yaya Abubakar. Saidai yaya Abubakar bai kai wanan fari da tsayi ba shi wanan jin dadi ya huda jikinshi kallo daya zakiyi mai ki gane yana jin lokacinsa. Duk a kallo daya da nayi mai na zayyano wanan kamanin nasa dana hango lokaci guda tas nayiwa gidan kafin na samu komawa part din iya inda na fara gyara tare da tsabtaceshi na fito falon daga kitchen dinsu dan soma sharo falon na iya a lokacin ya kara sallama ya shigo wanan karon ya sauya tufafin jikinshi zuwa wasu kananan kaya zakice shidin ba dan hauwa bane . Kayan sun matukar karban jikinshi sun fitar mai da kurciyansa a fili saiki rantse bai taba auren farko ba suna fadin Abubakar yayi rigima wanan mai mata biyu din ashe shine mai rigima din. Mama dake zaune tana jan tasbaha a hannunta ya kalla yace wai ina kuka samo wanan yar mama tun dazun naga tana aikace akaice gidan nan ? Kai dai bari yar albarka yar uwar amaryan Habuce da suka bar mata ita a nan shine ta tashi da wanan aikin ina su Sare ya tambayi kannensa mata . Wa yan nan mashiriritane ai suna daki kwance ko gyaran kwanciya basuyi ba balle susa niyar tashi iya fa ya tambaya ? Ta shiga gun Habu ta duba amaryansa ina ganin yarinyar yar albarkace yazo wai zai kaita asibiti nace iya ta fara duba mashi ita a gani. Fuska ya daure a cikin wani yanayi ya kai zaune yana fadin da anbari sun tafi asibitin kada wani matsala ya biyu baya kuma. Inba zamani ba ba komaine ake zuwa asibiti ba rashin sabone ga dai iya din can taje ta dubata ai tun dazun wayansa aka kira ya dauka ya cigaba da wayan karshe ya mike ya fita. Saida nagama aiyukan gyaran ko ina na nufi part din antyna inda nayi mamakin ganin tsohuwar a wajen ban tsaya ba na gaidasu na shiga dakin da kayana suke ciki wanka nayi na gyara jikina fes kafin na fito na samu tsohuwar ta fita daga wajen. A hankali nakai zaune ina duban kofan antyna din duk da ake cewa mu fulani bamu da hankali kankantana a lokacin baisa na fada dakin nata ba kai tsaye don muna da tarbiya zaman muna birni bai barmu da duhun kai ba. Bayan hakan kuma gwargwado muma fulani muna da namu addinin munsa abinda yake daidai da wanda bai dace muyi ba balle bamu taso cikin duhun kai ba ai. God so kind na iya kunna gas tun a abuja wanan yasa jin yayata shiru na fada kitchen tare damu mahaifiyar da yayata sukewa hjy Yaghana girki da mijinta . Haka diyansu su anty salma idan suna kasan nan mune suke sakawa muyi masu duk wani girki da zasuci har su bar kasan nan. Zaman na shekara biyu da rabi ko ukku a wajen baffa baisa komai ya fita kanmu ba tunda a cikin hakan muka tashi. Haka yasa na dora ruwan zafi na debo dankali na fara ferewa ruwa yayi zafi na juye a flask na dora suyan dankali duk a zatona suna dakinsu kwancene basu tashi ba kafin wani lokaci nagama hada breakfast na zuba a kula na fito daidai lokacin ya Habu ya shigo gidan da ledan magani a hannunsa. Zaka gane anyi girki don kamshin da gidan nasu keyi gaidashi nayi da dawowa na juya zan fita ya tsaya yana fadin kinyi breakfast ne Ramaah ? Ehh na hada yaya gashi can a dining na fada a dan ladabce yadda mukewa su anty salma a Abuja sai naga ya dan kalleni na second sai kuma ya juya zuwa ciki . Komawa nayi kitchen ban fita ba na wanke kayan da nayi aiki dasu na tsabtace kitchen din yadda ummah na koya muna tun muna kananun mu. Dama kuma idan kinsan bafulatana badai kazanta ba don tsabta kan akwaishi wajen fulani ko cup aka fara darazanshi wajen wankewa sai yayi fari sol za a barshi haka kore da sauran kayan aikin mata. Muryansu naji yasa na fito daga kitchen din dauke da kayan abincin part din tsofin dana wa yancan mutanen kamar yadda naga anty Yanda ta zuba masu a jiyan. Nasu na fara kaiwa suna falo dukkansu biyun nayi sallama na shigo bread ne ko ina baja baja a falin yaransu suna wasa dashi . Kyan kyami naji haka na ratsa ina gaidasu na aje masu abincin na juya da zumar fita daga wajen naji muryan wata na fadin. Ke meye wanan din kika kawo muna jin hakan yasa na juyo ina fadin abin karyawane sai akace daku bamuyi ba anan sai an kawo muna ? Ita kuma Asmau cewa tayi kice a daina kawowa hakana mun gode basai ta wahal da kanta ba kinji zoki dauka ki tafi dashi ta kara fadan hakan. Kallonsu na danyi kafin na yunkura zan dauki kulan abuncin naji muryanshi yana fitowa wani daki yana fadin ke ajeshi nan kice an gode ni aka kawowa baku ba da zaku yanke hukunci kuba da dokan kada a kara sako min abinci. Lah illah amma wanan kan gaskiya baiyi ba dan abin karyawan ma sai ankawo muna saboda me za ace a zubo muna. Nikan tunda yace in tafi na fito part din da saurina na barsu sunayi bansan ya suka karasa ba a wajen. Na koma na dauki na tsohuwar na kai mata suna daki suna hira na shigo ina gaidasu suka amsa na aje abin karyawan nasu a gefe daya. Wuri na samu na zauna gefe daya tunda ba sabawa nayi dasu ba lokacin sai ga mama dubu ta fito daga daki alaman wanka tayi tana fadin . Badai wanan yar girki tayi ba yanzu nake cewa idan na fito akai mata abin karyawa can wajen ku ai sai ga kuma wanan abin ta nuna kulan dana shigo dashi da hannu. Nice nayi mama anty Yanda tana daki kwance ina gani na fada yar albarka irin yaran nan ai bakuntanku baida wahala a waje. Meyene kuka dafane Sare data mike zuwa bude kulan abincin take fada tana bude kulan don taga abinda ke ciki Arish ne sai kwai da suyanshi yayi kyau sosai bai kuma yamutse ba zakice wata mace ce tayi aikin. Ke baki da kunya ku diba kuna daki yarinyar nan duk fadin gidan nan itace ta shareshi tas ta gyara nan ta gyara wajen yar uwata yanzu kuma ta hada masu abin karyawa. Kai amma kuwa dai tayi kokari Sare din ta fada nikan hankalina yana ga tv dake aiki ina tuna wani rayuwa a baya idan an saka waka muka kama rawa muna nishadi a falon yara gidan daddy na Abuja. Anty Salma yar daddy din itace ke koya muna rawa da waka sai mu dinga rawa ina yawan cin gasa idan ana competition a tsakanin mu yara. Sweet zata sayo da cake da yought a dinga rabawa a wanda ya iya rawa wai tana da saurayi mai rawa da waka shine take koyon waka itama. Yadda ta fado muna dakin zaisa kaji tsoro tana haki yasa gaba daya muka mayarda hankalin mu a kanta muna kallonta. Mijin ne yashigo a hasale ya nufota ta boye bayan mama Jafar meya hau kanka hakane kanka daya kuwa duk iskaci ai ba zata zo gurina kace zaka biyota ba ? Nikan tsorone ya kamani sosai da har yasa na mike tsaye juyawa yayi ya fita sai bayan fitanshi ta soma magana tana fadin. Kawai don nace ba zaici abincin wacan yarinyar ba shine wai zai dakeni mama din tace wace yarinya ke nan matar Habu dake sako muna girki idan tayi . Shine yake ci tun jiya yau nace ba zaici ba na zubar shine ya biyoni zai dukeni kafin takai aya mama tace kika zubar da abinci Nusaiba har kike fadi kin zubda ? Mama akan me zai zauna yana yaba girkin yarinyan nan daga zuwanta yana fadin haka aka san mace da iya,,,,,,,, Shiru tayi don ganin Habu dake tsaye kofa ya harde hannayesa a waje daya yana saurarensu don tunda suke rikicin har fitowanta yana tsaye kofan part dinshi. Ganin mijinta ya fita hasale ya shigo ya gaida mama ya samu tana kokarin aibanta matarshi da kwananta biyu kawai a gidan . Zama yayi su Sare suka fara gaidashi ya amsa a dakile yace mama kiyi masu kashedi akan maria idan suna rikicinsu da mijin su ya tsaya iyasu amma kada su kara hadawa da matana balle mace tace zata aibanta min mata. Sam ba zan dauki wanan ba ban shiga zancen yarinya ba mama kada wata mace ta kawo min zancen banza za a jini da mace a cikin gidan nan. Nasan za a rina da