← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 306

Sashe 113

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Anan muka kwana dasu salima dake tayi min sheri wai itace ango din zata wakilci yayanta ita da Nafisa ko a cikin dare muna shirin kwanciya saida aka kara kawo naman gashi mai, mai da tsoka anyi mashi irin gashin nan mai ruwa ruwa ga yaji da su kabeji da albasa an cakudashi mai yawan gaske da abinsha na kwalaye.
Daga dakin da muke muna jin su hjy yabi suna guda ganin irin gadan da ake baje masu a cikin bajinta don duk basu zaci hakan ba.
Daga falo ina jin hjy yabi na kwalawa anty salma kira tana fitowa tace yoo Salma kinga abin arziki haka yaki karewa a gidan kanwarki ?
Ai nace munga wajen zama mukam kila sai angon ya dawo ya tasamu gaba ya maida mu gida irin wanan gada haka aiba zamuso komawa gidaba mukan ana kawo muna wanan arziki haka.
Fadawa yarinyar nan ta kara zage damtse taci arziki tabar arziki a inda ta ganshi don wanan wajen sakata da walawane ba irin na zubarwa ba.
Ta fita zancen wayan nan matasa nata ta kama mijinta duk macen da take gidanta ita kadai sai taso saka kishi a kanta kan kishiya tasaka batama da wata kishiya a duniyan nan.
Yo mai zai dameki yar nan tunda ba unguwa daya kuke dasu ba iyaka kiyi hakkuri tare da matanshi kika sameshi don haka kada ki yarda kiyi dakon kishinsu a zuciyarki ki wahala .
Idan yazo miji ya tafi sai an dawo sai kiga an zauna lafiya duk abinda zai masu ko zaiyi da wata a cikinsu kada ki yarda wai ranki ya baci .
Don haka wasu mata suke wanan yasa ake wahalan aure a yanzu ka samu mutum da iyalinsa kace saika rabasu da karfi da yaji.
Wanan yasa matan yanzu da yawa basu son kishiya don basu san ko da wace ka shigo masu ba munji ta soma hauka kada ki yarda saboda da kishiya Allah ya konaki gobe kiyama ki barta ita tayi tayi duk abinda zatayi ke dai rike Allah da Annabinsa makami a gareki.
Komai tsiya dai bata tasowa tazo nan sai ranan da kuka hadu in har wani abu ya haduku nuna mata kawai ke baki da lokacin shirmensu.
Shiko miji da ance yau yana gidan ki ko baya gidan ki kyautatawa a tsakanun ku kada ki yarda kiyi sanya wajen ganin farin cikin maigidan ki.
Sunyi maganganu masu inganci da in mutum nada hankali zai dauka don babu shege a cikin zancensu da farko inda daga baya kuma suka koma barkwanci anty salma na zolayansu da ko a koro masu naman ne ?
Washegari tunda naga suna shiri na shiga damuwa don sammako zasuyi har matan kaduna su hudu da ummah ta hadomu dasu lokaci daya suka juya tare da tukwaicinsu na kawo amarya da anty su babba ta mika masu daga ango.

SOUTH AFRICA
Chapter 113 · 0% Book details