← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 306

Sashe 125

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Saiba dake zaune tana cika tana batsewa don haka ta kwanta takuma tashi a hakan ga kuma wani bakin cikin daya kara izo mata .
Don tun safe bai shigo gidan ba har wanan lokacin haka yasa ta mike zuwa falo a cikon fushi ta samu Asmau da yaran suna cin indomie a plate daya.
Ta zauna tana jan tsuki Asmau ta dago kai tana fadin kin tashi ke nan ta wani kallota tana fadin aiba barci nakeyi ba dama.
Wai kinga dan iskan mutumin nan har yanzu bai leko gidan nan ba tunda ya aje dabbobi a gida yoko dabbobi ma muke ai ya bamu kulawa gari ya waye haka har daya da wani abu ?
Asmau tace wa,kenan fa ?
Ta yo mata kallo mai kama da harara tana fadin J mana don ranan bai samu sweet J din ba a bakinta sai J data kirashi dashi cikin hasala.
Keko dai amaryace fa dashi Nusaiba yana can yana soyayyewa tukun ai dolesa dai ya lekomu dama don ya huta ya ki kawota nan cikin mu ya kebeta daban ai.
Wata amarya har ina amaryan take abu haka kamar kara shi yaga mutum har yaje zubar da mutuncinsa akan wanan yarinyar.
Ni wallahi ba zan dauki hakan ba shima ya sani akan wanan yarinyar ya dinga nuna mu bakomai bane itace mutum mu tashi tun safe yaki ko bugo waya ya tambayi lafiyan mu dana yaran nan ?
Ruwa Asmau ta dauka tana bawa yar wajen Nusaiban ba tare data kula da abinda saiba ke fadi ba sai abincinsu sukeci da yaran.
Taja tsuki ta rarumi wayarta dake gefe tana fadin wai don iskanci harda kashe wayoyinsa tun safe nake gwada kiransa ana cewa wayan yana kashe.
To aina fada maki baki yardaba ke nan da zancena amarcifa yake sha ai dole ya kashe wayansa bakiji ance amarya kona kara bace amaryace balle wanan yar filoce fa.
Koba hura sai asha nono don dara dara surbajo ce yana can ana gigitashi da abin na amare.
Kiran ya shiga yayinda take watsawa asmau wani harara da take dauka sakarai bata san ciwon kanta ba ita kan taji ya dauki wayan ba bata lokaci tace dashi.
Malam dabbobin daka aje a gida ba kulawa suna bukatan ka anan kan wanan sakaran yarinyar har zaka nemi ka wullakantamu kaki shigowa tun safe wajen mu ?
Ohh Saiba Allah ko gari ya waye ashe shaf na shagala an rudani bansan har gari ya waye hakaba ai wallahi ashe kuna son ganina ?
Na dauka baku da bukatana ai yasa na shagala a inda akasan muhinmancina namji mutumin dake gudun ka yake kyamarka kada ka shafa mai ciwo ya naka a yanzu ya samu wanda bai kyamarshi me kike gani ke nan zaiyi a yanzu ?
Yar iska sallon yaudaran datazo ma dashi ke nan dama yasa akai munafuci aka koramu gida don a samu shige maka wallahi mu zubo dani da itace a gidan nan.
Zakizo nan ke nan inda muke Ok fine sai kinzo din ai gara kizo kiga inda aka san zafina da darajana zaifi ta kashe wayan a cikin takaici da kunnan rai.
Kinji ko meyana fada maki a yanzu yana cikin gigin amarci komai yana iya fadawa mutum idan yai magana dama kyaleshi kikayi .
Tunda duk tsiyarsa dai baikai dare bai lekomu ba nan don haka meye zai damu mutum akansu yanzu.
Taja tsuki ta mike tsaya zuwa dakinta har ta zauna kuma ta fito saigani Asmau tayi ta fita ta girgiza kai tana murmushi tana fadi a fili wahalala kawai ba dadi ashe ?
Tasan dai ba fita zatayi ba a yadda ta fita don ko mayafi bata dauka ba don haka kila cikin gida zata tace ai cin tuwon kishiya rankone.
Nusaiba kuma part din iya ta shiga ta samesu zaune dasu anty baraka suna hira iya ina mama take keya baraka ta bata amsa taja ta tsaya saiga habu ya shigo yana fadin.
Ina mama karfe hudu mutanen nan zasu shigo a zauna na kira J yace dani zai shigo kafin lokacin yau hutu yakeyi yasa bai shigo ba.
Ai dole ya huta yau angone fa balle jafaru da bai samun hutu kullum a uzurce yake da tsabga baida lokacin kansa balle na wani.
Yanzu ko dole yabawa amarya hakkinta ai ya zauna tare da ita na dan lokaci su huta tare itama akwai gajiyan buki a tare da ita iya ke fadan hakan cikin rashin damuwa da saiba na wajen lokacin.
Balle yau Rahaman bata jin dadi tun safe ya kirani na kawo masu abin kari daga nan nakai masu har na fito bata san nashiga ba tana kwance.
Kai masha Allah kace abu yayi kyau haka yar albarka kenan haka muke son ji ko yaushe Allah ya shirya muna yayan mu a tafarkin addinin musulunci ga baki daya abu yayi kyau wallahi sosai.
Ba a kawo amarya washe gari ka ganta kwashi kwashi da idanu ba kunya ba tsoron Allah tana rawan kai da guloto sakarai bata san mutane na mata kallon banza bane sun dauka hakan wayewane yanzu banda sakarci.
Dariya habu yayi ya juya zai fita mama ta fito tana fadin Habu naji muryanka ina bandaki ya juyo yana fadin ehh mama dama zancen malaman nan da zasuzone nazo fada maku da karfe hudu sukace zasuzo yau.
Don tsabga garesu saida J ya kirasu dazun da naje wajensa shine sukace zasu shigo da karfe hudu din in sha Allah.
Yanzu fa nake tunanesa na dauka yayi tafiyane ai banga ya shigo gidan nan ba yau yana nan mama yana hutawane kawai zai shigo anjima.
Yana dai jinya zakace anty baraka ta fada tana dariya mama dubu tace jinya kuma jinyarwa shidai habu ya fita yana dariya sai anty baraka ke fadin amaryansa mana.
Itace wai yau ba lafiya saida shi habu yakai masu abinci dazun toooow Allah ya sauwaka tun yanzu an fara ciwo kuma haka ?
Kaiya banda abinki dubu kaji ance amarya ba lafiya a daren farko ai kasan meya gudana kuma haba dai kina magana haka ba lissafi kuma dai ?
To iya me kuma nace Allah ya sauwaka yakai yan baya ga danshinta mama dubu ta fada tana zama saiba ta juya kawai ta fita daga part din ba tare dayi maganan daya kawota ba.
Munafuncin banza da wofi Allah iya nan idan batayi hankali dani ba wata rana saina faceta a gidan nan .
Iya din Asmau dake kishingide ta dago tana fadi tace kada ki soma gangancin hakan ga iya don wallahi ba zakiji dadinsu ba kaf dinsu idan kika taba iya ko mama gidan nan.
Kansu fa a hade yake jallone da mufinsa idan kin kula da tafiyan mutanen gidan nan daya bayayi saida dan uwansa .
Kaf dinsu yaya J shike juyasu gidan nan kin taba iya donshi zasu kyaleki kike zato ki dai tsaya akansa shidaya munanana maki a yanzu.
Tsuki taja ta mike zuwa daki a cikin wani irin jin haushin kowa a gidan don ba wanda ya damu da halin da J din keson nunawa akansu yanzu itako ba zata yarda da hakan ba.
Don wanan yar fillon me zubin mayu daya dauko zai nuna su ba matane ko me gaskiya hakan ma ba zai sabu ba wallahi.
Sai karfe biyu da rabi ya shigo gidan duk da sunga anshigo da wasu kaya sun san shine ya shigo gidan amma bai zo part din ba tukun.
Asmau dake falo kwance tana wayane ita kuma saiba na kitchen tana hada abinda zasuci maigadi ya shigo da kayan ko kallon kayan batayi ba inda ya aje ya fita a kofan kitchen din.
Saida Asmau ta shiga kitchen din take fadin au baki dauke kayan nan ba ina ganin yaya yazo dasu fa kayan miyane nasan aka sayo ta duka tana bude buhun kayan.
Su kayan gwarine da nama mai yawa sai mai gallon biyu a gefe aje da kwalin taliya dana indomie zasukai shida duk a kofan kitchen maigadin ya zubesu wajen.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Chapter 125 · 0% Book details