Sashe 255
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yana dariya nidai na shige na kwaso mai kayan abincin da dan uwan nasa ya karya dasu din na aje mashi a gabanshi. Duk da ina aiki ban tsaya ba lokacin amma ina cankar maganan da Jafar din keyi da mutumin akan kudine yake tambayanshi ba,asin su. Zance na dashi tun dawowana jiya nake nazari a raina wanda na gama kai karshen tunanena wanda abinda zuciyana ya ban shine dukiyan sun samu matsala saboda dalilin kwanciya rashin lafiyan nan nasa. Indai za a rasa dukiya Allah ya bar muna shi Alhamdullahi rayuwa ya nema dama sai anema din daga baya in Allah ya nufa da sauran rabon hakan. Kirana da yaya din keyi yasa na fito daga daki tare da amsawa cikin dan muryana din nazo gareshi yake fadin don Allah dauko min wani file na nan a dakina a drower kasa ki kawo min . Na nufi dakin na duba nagashi na kawo mai ya karba yana budewa na juya da niyar barin wajen naji sallama ko ban juyo ba nasan muryan yaya habune a lokacin ya shigo gidan shima. Hakan yasa na dakata don mu gaisa na gaidashi daga inda nake ya amsa min kan kadaram kadaham nima na juya zuwa daki ba tare dana tambayeshi iyalinsa ba. Ina shiga dakin naji ya sun soma magana tun baniin me suke fada har na gane musayan magana sukewa junan su karshe dai na barjin muryan yan uwan saina jafar din dake magana a cikin fada da bacin rai yana nuna sakacin da sukayi aiba shi kadai hakan ya shafa ba dukkansune. Ni dai naji yana fadi a karshe cewa yasan matakin da zai dauka idan ma na waje sun cuceshi har dasu baiyi tsamanin hakan ba ai. Nan na soma jin muryan ya habu yana fasin J ya kake son nayi kana sin kaga laifinane a banza cikin zancen nan. Kafi kowa sanin bakin jinin da nayi a zancen nan gida ba a barni ba J kasani balle waje mutane yanzu basuwa Allah . Ni dai tun ina saurarensu har barci ya daukeni bansan fitansu daga gidan ba barci na samu sosai nayi a lokacin yana zaune falo bai tayar dani ba don yasan harda laluran cikin dake jikina a cikin barcin. Ban falka ba sai wajajen karfe daya na falka nayi mamaki yadda na samu barci mai dadi haka a lokacin na fito falon na sameshi a inda na barshi yana duban takardun dana dauko masa dazun din. Gaidashi nayi hakan yasa ya dago yana fadin kin tashi na amsa da eeh ina zama nake fadin sun tafi ashe yace tun dazun suka tafi me zasu fada min tunda suyi shirme . Zaune nakai a hankali ina fadin na zata ai azahar tayi yace da sauran time kin fara zuwa awo ne ya jefo min tambaya ? Hakan yasa nima nake mai kallon mamaki yaushe zan fara zuwa awo bai sani ba duk da dai bangarin ai a lokacin don haka nayi shiru ban bashi amsa ba. Saida aka dan dauki dan lokaci ya dago yana fadin bakiji mena fada ba na dan rausaya ina kawar da fuska nace ni banjin komai ai yanzu. Ko baki jin komai baki zuwa asibiti a duba lafiyan ki dana baby din a gani dole ki fara zuwa awo zanwa yaya Ai magana tazo kuje tare ko kuma maman tudu . Ni banje na gaidasu ba sai a kirasu suzo kaini asibiti kamar banda lafiya nidai ka barsu karka kira kowa don Allah na fada a karshe. To me kike nufi ba zaki ba ke nan ko dole kije asibiti don lafiyan ku idan can gida zaki biya ki dauku mama din fine amma asatin nan ki je a dubaki please. Shiru nayi na kasa cewa kkmai saidai nasan tunda ya fada sai anyi haka din don idan ban manta ba sun taba fadan zuwa awo da Asmau a gabana kafin na aureshi da shigan cikin dan nan nata data yaye din wanda aka haifa bayan an aureni . Yana tafe a gajiye ya fito filin kwalo rigansa na kwalo yana rataye a kafadansa saidai yana sharo kwanan gidansu ya hango dandazon yaran unguwa a kofan gidansu. Sauri ya kara ya iso kofan gidan fada ya fara da yaran yana korasu duk daya fahinci fadan da akeyi a cikin gidan nasu da yanzu ya zama kamar gidan haya suka zo kallo. Gidan ya shiga kanninsa mata ya fara hangowa a rakube cikin damuwa wucewa yayi zuwa bakin randan ruwan mahaifiyarsu yana diban ruwa a cikin takaici a fili kuma halin ko in kula yaron ya nuna ga abindake faruwa gidan tsakanin iyayyen nasa . A yadda ya fahinta da kishiyar maman tasu da mahaifinsune suka tararwa uwar nasu ake wanan masifan da zage zage a yanzu inda sabo ya saba da ganin hakan dashi da yan uwansa din don zaman lafiya ya kaurace a gidan nasu tun shigowan wanan matar gidansu. Karan dukan da yaji mahaifinsu nakaiwa mahaifiyarsu tana kakarin neman taimako ga yan uwansa na ihun ceto yasa ya yarda mudan ruwan kasa ya nufi wajensu da sauri yana fadin . Baba a,a baba ya haka kuma ka barsu suyi fadansu mana tunda bada kai akeyi ba zaka kamata da duka kuma haka a gaban mu. Uban ya nuna baima san yanayi ba shima haka baisan lokacin daya kai hannu yana banbare hannun mahaifin nasu ba a jikin mahaifiyarsu. Aminu zaka shigarwa uwarkane kome amayar baban nasu ta fada bai kulata ba sai kokarin kwatar mahaifiyar da yakeyi rai bace ganin mahaifin nasu kasheta yake son yi yasa ya nuna mashi karfi ya kwaci uwar yana dagota daga kasa inda uban ya shake ta. Baiyi aune ba yaji an kwala mashi abu a kai hakan baisa ya sake mahaifiyar ba sai juyawa da yayi ya rike tabaryan dake hannun amaryan mahaifin nasu da hannunsa daya yana fadin kika dukeni ? Dan iska zaka ramane kai ga mai karfi kazo ka tureni ka ceci uwarka ko ta kasheka ta kashe banza da iska mai halin uwarsa kawai. Bai kulasu ba yaja uwarsa dake rusa kukan takaici zuwa dakinta rai bace yana fitowa don bai tsaya a dakin ba suka hade da uban nasa ya soma fadin. Kai san iska yau din nan saika barmin gidana ni zaka nunawa ka kawo karfi a yanzy har zaka tureni don kana dan iska ka zabi uwarka dani ko ? To ka fito dakai da uwar naka kubar min gidana bai kula uban ba ya nufi wajen ruwan da yake diba din ransa a bace nan ma uban bai kyaleshi ba yabishi yana fadin . Nafika iskanci dan banza kawai kai har kana ganin kai wata tsiyace ko a yanzu ni zaka daga kan uwarka dan banza kawai. Shi dai yaron bai kula uban ba ganin hakan ran iliyan ya baci ya nufi inda suke aje icce ya rarumo ya nufoshi nan yan uwansa mata suka hau ihu suna fadin ya gudu ga baba nan da icce tafe hankali tashe . Bai gudu din ba ya nufi bayi ai kuwa yakai mai duka da iccen zafin hakan yasa dan dakatawa yana kallon uban dake fadin. Nace ka fice min daga gida mara mutunci wallahi baka zama gidan nan damu dan iska daga kai har uwarku ku barmin gidana gayan tsiya kawai. Uwar ta leko ta hau bakin ta har yaron ya shiga bayi sai kuma ya fito ya nufi hanyar waje ya fice daga gidan cikin bacin rai. Hausawa sunce kowa yace ruwan wani bai tafasa nasa ko dumi baiyi ai.