Sashe 209
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
kowa hakan yasa uwar take dauke dashi ko yaushe mikewa nayi dashi ina jijigashi a cikin kafin naji yana badaniya da nufin na mika mata dan ta karba mana kukansa ya isheshi ke nan yake nufi. Ni kaina karfin hali nakeyi a lokacin don warin abincin nan ya isheni a hancina ina jin kaina wani iri a lokacin. A wurin karbansane na shaki turaren dake jikinta kuma wani irin amai ne naji yazo min lokaci guda karo na biyu ke nan a yanzu dana ji abu mai kamshi zanji zuciyana yana tashi . Da sauri na mika mata na nufi bandakin nayi mamakin irin aman da nayi a lokacin duk dan abinda naci a lokacin saida na amayeshi a wajen haka na fito a galabaice ina share fuskana . Idon su a kaina yake na samu waje na zauna a gefe tana min sannu kamahin ne ya kara dakan hancina na mike da sauri na koma bandakin idonshi yana kaina har na shige ina kakarin aman da ba abinda ya fito min a wanan karon.