← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 306

Sashe 148

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin dare muna barci ya bugo min waya saidai wayan tana a silent ban samu dagawa ba lokacin sai washegari ya sake kira har na shirya lokacin naga kiranshi na dauka a zatona zai tambaya ko mun tashi ko kuma yai min ina kwana ? Sai gashi bayan mun gaisa yake min albishir din haihuwar matarshi Asmau data haifi da namiji a cikin dare . Da murnata nake fadin cikin farin ciki lah anty Asmau ta haihu Allah ya raya Allah yasa albarka ga yaron yasa mai akidar addini a zuciyar shi ita kuma uwa Allah ya bata lafiyan shayar dashi sai faman fadin amin amin nagode Rahama yakeyi. Nace a shafa min kan baby kafin nazo ganinsa yace zan shafo maki baki ganshi ba bouncing baby dashi kamana wallahi . Na kwashe da dariyan yake zakice yana gabana a lokacin sai bayan mun gama wayan nake fadawa Habiba zancen haihuwa tayi wani dunkunkun tana fadin Allah ya raya. Abinda su a kullum sukaga mutane sai su nuna basu sanka ba sai ka tsaya kana ta masu dogon kwantance karshe suce owooo ba zasu ba mutum ko ruwan sha ba. Kai habiba kowa da irin halinsa haka suke su halinsune hakana ai tace Allah anty shiyasa muka bar zuwa gidan gaidasu amma da ko wani sallah muna zuwa ai mu gaishesu muka daina. Shiyasa da akace zan zauna a wajenki na zata halinku daya dasu ai nayi ta kuka ina fadin ban zuwa maman mu tace in taimaka inzo kada ran uncle ya baci saida nazo naga ba haka kike ba ashe anty ? Da farko nazone in kwana biyu in koma sai naga ke kina son mutane kina kallon kowa da mutunci kai biba watau daba ba zama kikazo yi ba ashe tayi dariya tana fadin zan zauna ai anty ba inda zanje yanzu. Shigowan ya Ibrahim yasa muka mike gaba dayan mu muka fita ya sauke kowan mu ya juyo kamar yadda ya saba muna a kullum. Yar uwa na taushi zuciyana sosai akan yaya J da matansa ina kuma rokon Allah daya sassauta min zafin kishi irin namu na mata game da zaman takewan mu. Alhamdullahi kuma don ance Allah maji rokon bawane duk da abin dai sai a hankali idan ya kwanto zuciyana ina danjin wani abin lokacin da sauri kuma Allah zai tamakeni abin ya gushe min a kasan raina. Don haka tunane na farayi da me zanje idan zani barka don dole dai inje mata barka kuma zai kasance zuwana na farko tunda na auri ya J wanan zuwan zanga irin tarbon da zan samu daga kowa dake gidan. Bayan mun dawo gida na bude akwatin turamena na dauko wani zani daya dan burgini a ciki na aje saman gado niyata na kara bude na kayan kamshi in hada mata dashi inkai masu . Muna kitchen nida biba ne ya shigo har kitchen da ya same mu muka shiga gaidashi da wuni yana amsawa nake tambayashi maijego yace suna lafiya. Na karayi mashi barka da arziki yayi godiya ya juya zuwa falo ya zauna a nan na sameshi nakai zaune a kusa dashi yace a gajiye nake sosai yau banjin zan kara fita a yau da sauri na juya na kalloshi don nasan ba gidana yake ba da zaice hakan ? Ban gama mamaki ba ya kara fadin hada min ruwan wanka masu zafi in gasa jikina dana dawo sallah naci abinci inbdan kwanta in huta. Sam jiya bam samu barci ba muna asibiti saida ta haihune kusan asuba na samu na dawo gida ban kuma yi barci ba aka kira sallah na fito haka mutane ke shigowa suna muna barka da arziki. Tsam na mike zuwa hada mashi ruwan wankan dayace sai dai zuciyata a cunkushe don na kasa fahintar manufan hakan. Saidai ban sani ba ko zai kintsa daga nan gidanne ya wuce can din zuwa anjima kada in mai mumunan zato yasa na kawar da zancen kasan zuciyata. Har yaje yayi wanka bai kara magana ba nikan na fito naje maci gaba da aiyu kana naji lokacin dayake fadin shiya fita massalaci. Sai bayan isha,i yashigo gidan ina daki zaune a inda nayi sallah ina duba sakonnin wayata ya shigo ya sameni da sallama dauke a bakinsa. Na amsa tare da dago kai ina gaidashi yake fadin abinci zaki ban na dan kwanta kada in fadi a gajiye nake sosai yau wallahi. Na dai mike tare da taimakonshi daya miko min hannu muka nufi falon Biba nasawa kira ta fito daga dakin da take ta sameni a kitchen ina hada abincin abincin ta na bata don yarinyar nada wata dabi,a idan ban bata abinci ba komai yunwar da take ji bata taba diba taci sai lokacin dana bata din. Na fito na jera mashi lokacin har yakai kishingide a wajen yana waya saida na hada komai nayi mai nuni daya fara ci din yaja ruwa ya dauraye hannunsa ya soma ci ina gefe zaune ya kalloni da alaman tambaya inci mana na kada mai kai alaman a,a don na fahinci wayan da yakeyi yana da muhin manci a gareshi lokacin . Zance na miliyoyin kudi yakeyi don haka nayi gudun nayi interrupts dinsa a lokacin har ya kusa gamawa yana kan wayab ina jin maishi na tambayanshi abinci yake cine halan naji yace ehh new wife dina ta hada min delicious nake ci yana dariya yake fadin ko mai nata na bam mamakine ita kamar yadda take ai. Banyi aune ba naga ya haskowa wace yake wayan da itani yana fadin kinganta nan yana nuna mata fuskana nayi kasa da kaina cikin kunya. Yake fadin ku gaisa mana amma bata jin hausa fa turanci zaki mata zance ranan ya fara jin kalman turanci a bakina da abin ya bashi mamaki matuka. Har yake tunane wai ko da gaskene munyi zaman rugga da ake fadin munyi kuwa shifa al,amarin mu yana matukar daure mashi kai sosai wallahi. Kafirace na gane hakan ta yanayin shigarta da nagani suman dokin dake kanta daya zubo sai yanayin rigan jikinta kuma dana kara fahintan ba musilunci a tare da ita. Muka gaisa da ita take fadin gaskiya ina da kyau matuka dole handsome ya rude a kaina ashe a yanzu baida zance sai nawa a bakinsa meye sirin abin ne wai ? Koda yake ga sirin ta gani da idonta ai kurciyata yake diba da yake kara mai karfi take fadin in kara kula da shi sosai don Allah nayi dariya ina mata godiya ya juya da wayan yana cin nama sukaci gaba da magana dashi duk a kaina daine har sukayi sallama suka kashe wayan tasu. Ni kan harna mike ina tattara kayan abincin zuwa kitchen na dawo ya mike yana fadin a ina yarinyar nan take kwancine da cewa habiba yake tambaya ? Tare muke kwana da ita a dakina na bashi amsa yace to a dakina ke nan zamu kwanta ko mu bar mata waje ? Anan zaka kwana ke nan ya kalloni cikin mamakin da ni yakamata ace nayi mashi tunda nasan bai gama kwanakin da zaiwa matanshi a can ba tunda na fahinci two two days ne kwanan namu kamar yadda akasarin musulman hausawa sukeyi a gidajensu wajen raba kwana a tsakanin matayesu. Shi da kansa ya koma ban amsa da anan zan kwana tunda kikaji na fada ai ko akwai matsala da hakan ne ? Nayi lau da idanu ina rausaya kai nace gani nayi dai baka idda kwanakin ka bane a can ai tunda kwana biyu kawai kayi a wajensu ? To anan din da baki son in kwana zan kwana din ya mike ya nufi dakinshi kai tsaye yana barina wajen dana bishi da kallo marata dake dan yankawa ya kara yankawa alaman dai period yana gab da zubo min don haka yake min idan na kusa period akarshen wata. Daki na koma na kimtsa duk da dare baiyi ba sosai a lokacin saida na gama na nufi wajen biba dake takure daki kasancewar shi a gidan na samu har ta soma barci da littafi a hannunta. Dan bugun ta nayi ta tashi nake fadin tashi kije dakina ki kwanta uncle fa ya tafine anty naji ta tambayeni ? Sai nayi dan murmushi nace ba a nan zai kwanta ba yana dakinsa jin hakan yasa ta mike sai kuma tace da dai kin barni nan din in kwana anty ? Bazaki kwana a can din ba shiya kwanta tun dazun ai yana dakinsa hakan yasa muka fito tare zuwa dakin nawa da ban fita ba saida naga ta kwanta na rufo mata kofan bayan na kashe wuta. Dakinsa kodana shiga har ya kwanta kamar yadda yace barci ya soma dibansa na kashe wuta na rufo dakin na kwanta a gefen shi . Na zata barcin nasa yayi nisa sosai yasa nake komai a hankali don kada in tasheshi amma me banfi minti biyu da kwanciya ba naji ya mirgino guna yana rugumana tare da ajiyan zuciya. Saida ya shaki suman kaina dake a daure don ko kitso ban samu yi ba niyata sai zai dawo gidana zanyi kitso din da dan gyare gyare sai gashi abin ya zamo min bambarakwai ban fahinci meke gudana ba a yanzu gidansa. A yadda daina fahinta shine dole akwai matsala tsakaninshi da saiba har ya kawo haka kuma dole wanan matsalan babbane duk da ko suna hakan a da can ba fahinta zanyi ba irin yanzu dana shigo cikinsu dole a yanzu in fahinci hakan a tsakaninsu duk daba hiransu mukeyi dasu ba dashi. Kiss yakaiwa wuyana yana fadin I love you Rahama ina son kamshin nan naki sosai yana min dadi a raina nakan ji kamar bani bane idan na kasance dake haka a yanzu ? Cabdi jam watau gaskiyane anty salma da malam mu na vocatinal center da sukace wasu mazajen kamshi tsabta da iya girki ko iya magana yana sa su kasance da mace har a dauka kamar asiri macen take masu suke rikicewa haka akansu. Anty Salima da saratu sun taba hira mai kama da gulmanshi a gabana ita saratu take fadin takan rasa yaya yake kasancewa da matansa yadda yake dan gaye din nan su kuma san gasu kazamai tun dai Asmau dako wanka yake zama
Chapter 148 · 0% Book details