Sashe 301
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dare daya Allah ke nashi ikon idan ya tashi ba wani mahalukin daya isa ya hana wanan faruwa a duniya saishi daya bayar ya isa ya karbe abinsa duk lokacin dayaga daman hakan ga bawa kamar yadda ya bayar din. Wanan tafiyan da yaya yayi sati biyu kacal ta daukeshi ya dawo a cikin tarin dukiya mai dinbin yawa tare da abin arziki ga yan uwa da masoya don tafiyace data zamo wace ba za a manta a cikin tarihi ba. Wani lokaci Allah kan jerabi bawansa ya dora mai jerabawa a rayuwansa wace zata zamo mai alheri a gaba matukar bawan nan ya iya juriya ga hakan ya samu ikon cun jerabawansa da hannu biyu a karshe sai Allah ya juya hakan ya zama mai alheri a rayuwansa. Don kuwa zance da ciwon yaya da shiga fatarsa da ganin wasu halaiyan da bai zata ba ga yan uwa duk hakan jerabawane daga ubangijinsa Allah. Don sanadiyan wanan ciwon da yaya J ya kwanta abubuwa da dama Allah ya jerabeshi dashi yaga duniya sanadin hakan dukiya ya salwanta lafiya ta kubce masa yan uwa sun gujeshi don baida iyali sun nuna nasu halin a gareshi abokai ba kowa ke saurarenshi ba duk da halarcinsa garesu a baya. Sai gashi Allah ya dawo mai da dukiyansa inda ubangiji yayi ikonsa kayan sun ninka kudinsu sama da lissafin mai lissafi abin baiko faduwa. Wani saurayin Maibe dake can ya adana kayan a wajensa kamar yadda ta bukata yayi daga baya da suka samu labarin jin saukinsa aka baiyana mashi inda kayan suke yabi kuma suka shiga a cikin lokaci aka samu alherin daba,a taba tsamanin hakan ba gareshi. Ruwa aketa shega muna a garin hakan yasa bamu tsaya wani dogon hira ba duk da ba matsalan mu da ruwan muna cikin rufin asirin Allah mu bamu ganinsa balle ya tabemu. Amma yanayi yasa mun kwanta da wuri a ranan nagama shirya Amir nima na kimtsa kaina zan kwanta naga wayana yana haske na dauka. Yaya nagani yana kirana lokacin na dauka yaron kuma yana min kukan nono na fara daukan wayan nakara a kunnena kafin nakai hannu na dauki yaron ina mashi sallama naji yana fadin kun rufe gidane nace ehh yaya ki bude min gani nan zuwa ya fada. Na amsa da to cikin mamakin yadda ya iya tafiya a cikin wanan ruwa ga dare haka duk da shadaya ake nema a lokacin amma gari yayi tsit a lokacin. Na saba yaron a kafada na fita zuwa falo na bude kofan a daidai lokacin maigadin mu ya bude get din gidan motoci ukku suka shigo a jere lokaci guda haraban gidan. Dawowa nayi na zauna don Amir daketa tsala min ihu hakan kuma ba halisa bane shi yarone mai hakkuri yana da wuya kiji kukansa sai can ba a rasa ba amma akwai zuciya gareshi mama kance ya gado na fulanin a gareni watau zuciya. Haka ya shigo ya sameni zaune na fara ba yaron nono yana tambaya ina key din dakunan boys quaters suke na mike na dauko mashi ya fita na zauna nacigaba dabawa Amir nono a falon. Ya dan jima ina falon zaune ina tunane a cikin raina Aminu ya dinga shigo da wasu manyan jakkuna shida mai gadin gidan kusan biyar kafin shiya shigo daga baya don ruwan ya dan tsagaita a lokacin. Tun kafin yakai zaune yake tambayana mama fa tayi barcine nace ta kwanta tun dazun nima wanan ya hani barci yau da sauri yake tambayan meya sameshi kuma ? Nace dashi yau dai kuka yakeyi tun yamma mama tace kila cikinsa ke ciwo anbashi balma kuma bai bari ba. Ya mika hannu ya karbi yaron nace abinci fa yace bar zancen abincin nan yanzu bamu da yunwa hankalinshi na kan yaron yana dan dube dube a jikinsa yake ban amsa. Yakai zaune yana fadin ko zamu kaishi asibitine a dubashi da sauri nace da daren nan a dai bari da safe mugani yanzu ko mun fita a cikin ruwan nan wa zamu samu a can ? Baki da tausayi don ciwon ba a jikinki yake ba zakice har saida safe idan bai bar kukan nan ba dole mukaishi asibiti nayi sa,a yarin yabar kukan shima ya mike zuwa dakinshi yana gyara kayan da suka shigo dashi din ciki. Yaron na goye a bayana na shiga na sameshi ina fadin yaya bafa gidan nan zaka zo ba naga kazo muna a cikin daren nan baiyi magana ba saida ya gama dora kayan ya juyo yace Allah ko ? Ina ya kamata in tafi nayi shiru tunda nasan tambaya dai kawai yakeyi saida yakai zaune nace saura kwana ashirin da biyu muyi arba,infa yanzu. Sai akace kada inzo sai kinyi arba,in ko banda wanan koda kikaga ban zama saboda mamace kuma aiki akai maki kina son hutu yasa nabarki ki huta don nasan innazo zaki wahal da kanki da aiyuka yasa na daure har wanan lokacin. Kamar ince yanzu ko kagaji da hakkuri da zamanta ka dawo ko karanta zakayi daga gidan iya dai tunda mukaje suna bata dawo ba tayi zamanta gida tace na samu sauki ai saidai. Banyi magana ba na shiga bandaki na hada mashi ruwan wanka amma saida na koma daki na dauko ruwa a cikin flask don ba ruwan zafi gashi ana sanyi a ranan balle ya watsa ruwan sanyi. Ya shiga wanka na koma dakina muka kwanta da Amir ban falka ba sai Asuba na tashi nayi sallah kitchen naje na hada muna ruwan zafi don yin wanka har lokacin ba wuta a garin gashi engine din gidan ya baci ba a gyara ba har lokacin duk da ban jona mashi kayan nauyi dama. Na juye ruwan na fara hada breakfast don bakin dayazo dasu mama najin motsina ta fito daga daki tana fada nace aina sa biba ta kwashe min ruwan takai min. Lafiyayyen breakfast na hada nayi wanka na gyara kaina lokacin mama ta fito tayiwa Amir wanka ta kimtsashi ta miko min shi in bashi nono Biba ta shigo tana fadin Anty naga wasu motoci a wajen gidan nan fa ? Da maisu a gidan ai motocin me kuma kinkan fara maganan ki ke nan mara ma,ana nace ta ganine mama yaya ya dawo jiya da dare kuna barci. Cikin mamaki mamake fadin lalai munyi barci jiya ban kayi dogon zance mai tsawo da ita saidai ita ta dinga min hira ina murmushi ba ita kadai ba kusan hakan dabi,atace rashin dogon magana mai tsayi da kowa hakan nake. Shine ya fito yana muna sallama mama ke fadin yanzun nan take fada muna ka dawo jiya da dare ina tunda iska ya taso aka fara hada hadari muka shige daki ai suka gaisa dashi tayi mai yaya hanya ? Bayan sun gama gaisawa ya juyo yana fadin mutanen nan zasu kama hanya yanzu gashi na makara ba ayi masu abin karyawa ba kuma ? Nayi na fada a sanyayye kinyi fa eeh na soya dankali da kwai sai dan ferfesun dana hada da sauran kayan cikin daya rage muna a fredge amma kin kyauta wai da nafitone in kaisu su karya su kama hanya. Biba ta fito da kayan zuwa wajensu ya jima a can din kafin ya dawo bayan ya saukesu inda zasu shiga mota na na hada mai ruwa yayi wanka sanan ya fito karyawa . Bayan ya zauna yake tambayan mama nake fada mai tana daki yace nayi mashi magana da ita nashiga na kira mama din tazo. Mama din tafito tana fadin ka dawo ashe bakin sun tafi ko yace sun tafi mama daga can nazo dasu sun jawo min motocine zuwa nan yan kamfanine aikinsu ke nan idan ka sayi mota a wajensu zasu jama sukai maka duk inda kake so. Tana mamaki tace su kuma ta haka sukeci da iyalinsu Allah ka rufawa bayin ka asiri ya amsa da amin tafiya ai tayi kyau sosai mama addu,anku yana aiki sosai a garemu kullum sai kara ganin haske a rayuwa mukeyi mama . Addu,an mu da alherin ka ga mutane malam da zamu samu irinka biyu zuwa ukku a cikin mu da yanzu an gama saninku a ko ina fadin kasan nan hannu daya akace baya daukan jinka. Anyi ma yawa akai malam dole jiki yayi tsami ko a hakan mama Alhamdullahi don tafiya anyita a sa,a sosai wana karo ban taba tafiya mai sa,a kamar wanan ba a rayuwana ba. Mama ta gyara zama tana fadin Alhamdullahi haka muke son ji ko yaushe gareku muji kuna samu karuwa tako ina shine addu,an mu gareku ai. In sha Allahu mama bana ina son ku taka arfa gaba dayan ku da yardan Allah cikin mamaki tace gaba dayan mufa kace yace insha Allahu hakan nake fata mama. Allah yace malam Allah yace daga gefe na amsa da amin a cikin murna tace dadina dake yar nan hankali yau da watace ya fadi hakan saita nuna bakin ciki a fili wasu matan basu da lissafi a rayuwa ko kadan wallahi ni dai nayi murmushi ina fadin mama aikoni keda hali haka zan iya kaiku insha Allahu. Haka shike yata nasam zaki iya hakan idan Allah ya hore aka kwashe da dariya suna ta hiransu yana karyawa har ta dauko mai zancen yadda saiba taje tayi hauka da kuma zancen zuwan saratu gida. Nan ya tsayar da cin abincin yake fadin me kuma saratu tazoyi gida yanzu ko haka akeyi kazo gida daga kaika gidan miji wai ? Towa zai sani malam uwarta ta boye zancen ga yan uwanku nasan kai ake jira ka dawo yanzu daka dawo ai dole a nemesu ai yaja tsuki da alama abincin ya fita mai rai yace Allah mama naje gida banji wani abu mai karfi ba yau din nan tana konawa dakin mijinta. Basu san ka dawo ba ke nan tace shigowa na gari na yo nan gidan don bakin nan dana zo dasu nasan idan na kaisu can karsheta inji kunya don haka nayo dasu nan gidan ai. Bai wani jima ba dai yabar gidan muka zauna hira da mama tana kara ban tarihin rayuwansu lokacin mijinsu yana raye kafin ya rasu. Gidan Asmau ya fara biyawa a lokacin ya samu suna karyawa ta dan fara kame