← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 240 OF 306

Sashe 240

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

isa ba wanan karon. Tafiyan maman tudu yasa hankalin yaya Jafar komawa gareni ko yaushe zai zauna zugun yana tunane ta inda zai bullowa zancen tafiyan nawa gida. Don ya kulla da mama sam bata son wanan maganan haka shima habu yayi shiru da alama yayi fushi akan rashin dawowana gidan tare dasu lokacin. A lokacin mama ta shigo dakin ta sameshi hakana a cikin halin tunane ta soma fadin Jafaru na horeka da zama haka kana faman tunane ? Kasan jikinka ba lafiya gareka bafa ka daina tunanen yaran nan dukkansu yan banzane don jinyar kane duk suka gujeka da kuma fitinan su ya koresu idan wani abu ya sake samunka a yanzu ba hasaransu bane. Haba mama ki daina zagin yaya mutane haka ita Nusaiba ai kowa yasan abinda ya hadani da ita gidan nan harta fita haka kuma ita Rahama saboda matsinki da saratu akantane ai yasa ta tafi. Amma ba don jinyana ba ko za a fadi hakan kuma banda Rahama yarinyar da tayi tsaye a kaina har Allah yaban lafiya. Yanzu kuma ace don kada tayi jinyana ko ta gaji da jinyata yasa tabar gidan nan kawai dai irin maganan da kuke fadi a kantane yasata fushin zuciya ta tafi amma ba,,,, Wai Jafar kanka daya kuwa yau kake fadin wanan maganan haka kamar wanda wani abu ya sama shima jafar din katseta yayi da fadin a,a mama maganan Allah udan yazo a yishi don kina gani a gabanki saratu da Nusaiba suka matsawa yarinyar nan amma ba a tsawata masu ba . Lalai anyi gaskiya da akace macen bafulatana hatsarice ga mutum don basu shiga gida ba su hada kan kowa a gidan ba idan basu sami hakan ba kuma sai suyi yadda zasuyi suga sun halaka duk wani wanda ke gidan ,,,,,, Wayanta dai daya dauki kara shiyanata karasa zancen datakeyi din ta tsaya daukan wayan a cikin mamakin dan nata datakewa kallon tababe a ranan kan bafulatanan matarshi din data tafi yasashi gigicewa hakan. Ganin layi kawu daya matsa kiranta yasa ta dakatar da zancen ta dauki wayan da sallama tana karawa a kunnenta ya amsa. Gaisuwa ta fara mai ya amsa a gagauce ya soma fadin Dubu kina da masaniyar zuwan yaron nan gidana kuwa ? Ta mayar mai da tambaya itama da wani yaro ke nan kuma ya amsa da yaron nan Yazid mana wai yazo tambayana kudinsa da akace suna hammunsa. Kudinshi kuma shi yazid din yazo tambayanka kudi yaya ya amsa da kwarai yazo shekaran jiya nace bari dai in kiraki in tambayeki ko kina da masaniya ga hakan ? Wallahi summa tallahi yaya banda masaniya ga zuwanshi wajeka shi yazid din yaje gidan ka yaya yana tambayan kudi kuma bayan na fada mai kada yayi wanan maganan a wajenka . Kwarai kuwa yazo min nan a fitsare wai yazo karban kudinshi a wajena nace yaje sai munyi magana dake Dubu dama abinda nakewa gudu kenan gashi ko ya faru tun yanzu ? Har yaushe aka bada kudin nan don Allah dubu da za a dinga matsawa da a bayar dasu bayan an juya kudin zuwa kaddara yanzu. Yaya kayi hakkuri dan Allah zan mashi magana sai faman fada yakeyi Jafar yana zaune gefe yana kallon ikon Allah a tsakaninsu. Saida ta gama wayan ta dago tana fadin kaji min kuma wai yazid ya samu kawunku yana mashi zancen kudinshi . Ok kawune kuke waya dashi yanzu ta juyo a cikin damuwa tana fadin yanzu haka kawai yaron nan muna zaune lafiya da dan uwana yana son hada tsakanin mu. A,a mama ku natsu ku bincika kuji meye dalilishi nayin hakan dole yana da dalilin dayasa yayi hakan ai ba zai tashi haka yaje wajen kawu kai tsaye zancen kudi ba. Jin abinda Jafar ya fada yasa uwar kallonsa tana fadin barshi ya dawo ai zai sameni bai yarda dani ba ke nan danace kudin suna hannun yaya yaje da kanshi ya bincikeshi ? Fada sosai mama din keyi ga yazid din ya fita tun safe bai shigo ba har mama dubu ta fito zuwa part din don diba jikin jikannata nan ta samu mama din tana fada saidai tana ganin iya taja bakinta tayi shiru. Don da jafar da yazid suna dasawa sosai da tsohuwar habune kadai suke yawan fada dashi lokaci lokaci wanan yasa ko yanzuma da yazid ya dawo da iyalinsa suke kadaici itace mai zama dasu tana debe masu kewa. Sai bayan la,asar ya dawo gidan part dinsa ya nufa inda ya dan zauna da iyalinsa yaci abinci kafin ya fito don tun safe bai leka dan uwansa ba. Ya shigo da yaronshi a hannusa cikin fara,a yana fadin yaya ka ganni sai yanzu na tafi duban masu aikine can nake tun safe don kada su sake maimaita shirmen da sukayi a baya. Ya dan rankwafa yana fadin ya karfin jikin naka brother badai matsalan komai ko yake tambayan dan uwan ? Ya juyo wajen mahaifiyar tasu a sake yana fadin mama barka da gida yaya gidan kuma da iyali ? Suna lafiya Yazid yaushe kaje gidan kawun ku tambayansa kudi don dazun ya bugo min waya yana tambayana ko ina da masaniyar zuwanka wajenshi ? Ya samu bugo maki kenan naje ina son kudina dake hannunsa akwai abinda zanyi dasu a yanzu don ba zan tsaya ace sai kawu ya juya min kudina ba mama ? Yazid ni kake fadawa hakan kai tsaye ko kana son nuna min cewa mu bamu isa rikema abinka ba ke nan ko ? A take ya daure fuska yana fadin da karfina mama zan tsaya kawu yana juya min dukiya aban abinna yadda akabawa kowa nasa in rika don ina da abinda zanyi dasu yanzu . Yazid kafita min a ido akan kudi kada ka tsaya kana min rashin kunya a gabana yanzu da sauri yazid din ya katseta yana fadin . Mama kudina fa nake zance ba wani abu ba ya ban ina da bukatansu tunda hakkinane anbawa kowa nasa nima ina bukatan nawa a yanzu. Kudi a yanzu kaddara aka mayar dasu don haka banson jin zancen kudin nan a yanzu ka bari sai ranan da ya sayar da kaddarorin daya saya ya baku kudin ku. Ba zai yuyu ba mama kudin nan fa kudinane bance aban na wani nayi amfani dashi ba don haka a ban abinna don Allah ki fada mashi. Yana fadan hakan ya juya a fusace ya bar dakin da danshi a hannunsa yana shiga part dinsa ya zauna yana fada yana fadawa iya abinda ke faruwa . Karshema ya dauki waya ya dannawa kawu waya yana fadin kawu zancen kudina nake maka ina bukatansu nan da kwana biyu in Allah ya kaimu yana fadan hakan ya kashe wayar tashi rai bace. Shima a bangaren kawu bin wayar shi yayi da kallo yana mamaki yadda dan nasa ya kirashi babu ko sallama yana mashi zancen kudinshi. Yasan akwai matsala ke nan akan hakan don dole yakai kanshi gidan su zauna a gaban mahsifiyarsu ta takawa yaron burki don yasan ita kadaice zata iya takawa yaran a yanzu.
Chapter 240 · 0% Book details