Sashe 96
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sati biyu da hakan shigan bazata yayi masu don da safe yashigo gidan wanda ke nuna a garin ya kwana ke nan don duk wanda yagashi a zaria karfe takwas na safe haka yasan a cikin garin ya kwana. An kasa samun wanda zai tambayeshi ina ya kwana sai iyace take fadin amma a garin nan ka kwana Jafaru. Ya bata amsa da eh iya cikin gari na kwana nashigi da darene sai kawai na sauka wancan gidan nawa. Kana da wani gidane dama Jafar ban taba sani ba kowama bai sani ba iya idan ba yanzun din da nake fada maki ba amma na dade da ginasa ai komai kuma na saka a cikin gidan. Ina son in kai amaryata can ta zauna ita kadai sai masu tayata aiki kawai a gidan kinga na samu gidan hutu ke nan . Can zai zama Abuja kenan yaya nan kuma gidan kwamacala ya zama lagos ko don lagos shike daukan duk wani kwaram da amma. Salimace take fadin hakan a cikin barkwanci ga dan uwan nata data dauka zolayan iya yakeyi ya fadi hakan. Saiba dake zaune ta tsoma bakiga zancen da fadin babu wata shegiyan da zata shigo muna gida iyamu, mun isheka rayuwa muma din ya aka iya damu balle aje dauko wata. Ta fada tana turo baki dake nuna tana cike dashi har lokacin gashi ya sharesu kusan wata daya ke nan yanzu ya dawo kuma ba wace ya tsaya kulawa a cikinsu. Itako Asmau sai cewa tayi ai lagos din ma ba laifi indai zaka zauna lafiya ko a lagos ai akwai more rayuwa sosai ma don yafi wani wajen sau dubu. Salima tace amma ai kusan cewa Villa shiyafi dadi ko ? Don gaka ga gidan kudi kullum kana jin kamshin bugunsu haka kuma shine headquater da kowa ya sani dai dole yaya ya tare da amaryansa Villar ku kuma kuna nan da yara kuna kwamacalan ku. Dadin abin dai ba a canzawa tuwo suna haka kuma baka zama da miya ba tuwo don shine abokin hadinsa mu din dai mune dai ba wata yar banzan da zata sake shigowa gidan nan da sunan matan aure a part din nan sai dai can gaba kuma . Wayanshi dake kusa dashi ya dauka cikin rashin damuwa da zantukan da sukeyi lokacin can a ka daga yake fadin kai Habu kana inane wai gani gida zaria ? Ina nan kano tun shekaran jiya ana karasa sauke maine har yanzu to idan an gama kazo gida don ba dadewa zanyi ba zan koma . Ina tafe yau din nan in sha Allahu zuwa yamma Habu din ya fada yace Allah ya kawo ka lafiya yana kashe wayar tasa ya aje gefe daya. Sai lokacin iya ke fadin da alama dai wani tafiyan zakayi ke nan kuma Allah ya tsare muna ku Jafar a duk inda kuka nufa din ya amsa da amin iya. Yanzuma akwai abinda nashigo yi a nan zaria don da baku ganni maza ba saboda aiyukan da suka taso sosai a yanzu sai iyan ta karba da madalla haka muke son ji ko yaushe aiki ai alherine. Ta juya ta kalli salima data rakota tana fadin to ke zaki zauna nan ne kuna cika baki ko zaki maidani wajena don naga baku karasa cacan bakin naku ba har yanzu. Ehh lalai ma Iya cacan baki kika dauki zancen mu ashe yanzu akwai wata wace zatayi gigin shigo muna gidan nan da sunan kishiya ? Au kina wasa wuka a gaban doki ne don yaji tsoro ko to jafaru ba raggon maza bane yana da ikon cikawa da biyu a rana daya. Yadda aka auroki kika shigo kika hana wata rawan hantsi kema haka za a dauko wata a kawo bayanki don ba a haifi namiji don mace daya ba dama. Tashi muje yar nan ta dubi Salima bayan ta gama maganan daya harzuka Saiba din data gane nufinta ta zata asirin da take bankawa jikan nata yana tasiri akansane da har bai iya daukan wani kwakwaran mataki akansu. Jafar yasha yiwa iya korafi akan Saiba ko ince ya kawo mata karan sai ba din kan barbade barbade ga abinci ko cusa abu a gabanta bayab sun gama sunna ya ga abin tun yana mata fadan hakan dagashi sai ita har yagane hakan yabi jikinta ba zai iya lamuntan hakan gareta ba yakai karanta wajen iyan akan a tsawata mata ta daina wanan halin. Wanan yasa ciwon sa na farko harda zargin saiba din saida sukayi wanda dama hakane ga mace mai hadawa da surukulle wata rana har abata abinda zai cutawa abokin zamanta cikin rashin sani da sunan taimako a gareta. Ya Habu bai shigo gari ba sai wajajen la,asar ya dan gauta ya iso tun shigowansa gidan ya hango motan dan uwansa a kofan part dinsa. Nasa part din ya tsayar da motarsa ya shiga ciki inda ya samu matarsa da dansa don ita ba ma,abociyar son shiga jama,a bace wanan ya kara mata bakin jini a gidan suka kara tsanarta. Don sun dauka daukan kai take masu don tana ganin kamar ta fisu wanda ba haka bane haline saika zauna da ita na wani lokaci batace dakai kalla ba saika gaji kayi mata magana. A part din iya suka hadu da dan uwan nasa sun dan zauna na lokaci kafin suka mike da sunan zuwa wajen mama dake can tudun wada family house dinsu ita da Saare da Nafisa. Tun zuwa sunan matar yaya sani basu dawo gidan ba suka zauna can din wanda ita Saare bata so hakan ba amma mama Dubu tace ba zata koma gidan yayyun taba sai tare da ita wanan zaman takuran Saare take cikinsa duk kwanakin. Motar Habu sukai amfani dashi suka fice gidan a hanya Habu daya kula da rashin sakin jikin dan uwan nasa yake fadin kace kana son ganina J ? Haka kuma tun shigowana part din iya na kula da dan fadawan da kayi don kayi rama sosai a yadda na barka wani abin ya farune kuma ? Ya dan juyo daga barin kallon titin da yake yana mai dan tsurawa dan uwan nasa idanu na dan lokaci kafin ya mayar a hanya yaci gaba da tukin da yakeyi. Yayi wanan magananne don yadda yaga damuwa karara a fuskan dan uwan nasa don bai saba ganinsa a hakaba ko da yaushe yana a yanayin nishadi da walwala . A hankali J din ya kwantar da kansa jikin kujeran mota yana sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanunsa yace. Bari Habu ina cikin wani dan cakwakiyane a kwanakin nan duk da kaima nasan abin zai shafe ka duk yadda ka kauce kuwa . Subbahanallahi mene wanan abin J jikin nakane ya kara tashi kuma again ya girgiza kai yana fadin ba jikin bane Habu rigima dai na fada a ciki lokaci guda. Habu ya jinjina kanshi yace ina saurareb ka nasan dai duk rigiman da zaka jawo ba wanda zaiyi kasa da martaban mu bane a idon mutane in sha Allahu. In Allah ya yarda ba irin wanan da kake nufi bane habu rigiman soyayya na fada lokaci guda ka kangani a haka na rasa wanda zan fara tunkara da zancen nan saikai habu don nasan zaka sama min mafita in sha Allah. Soyayya kuma J kana da mata biyu fa a gida me zaisa ka fada tarkon wani soyayya kuma a yanzu again ? Nima abinda nake duba ke nan Habu abin mamaki ban taba tunanen zan fada tarkon soyayya irin haka ba lokaci guda sai gashi Allah ya jarebeni da hakan . Lokaci guda habu Allah ya jarabeni da matukar son yarinyar da kowa zaiyi mamakin hakan a gareni amma ubangiji cikin hikimarsa da buwayansa da masifan sonta haka lokaci guda. Guntun tsuki Habu ya saka lokaci guda yana fadin wanan ai baikai na tashin hankali haka ba ni harka firgitani wallahi . Aure a yanzu gareka ai wata mafitace ga wanan matan naka da basu san ciwon kansu ba Allah yasa dai ita wanan din ta kwaraice da zata fiddakai kunyan abokanka. Kaifa Habu dadina da kai ke nan ba sai kajira kaji ko wacece yarinyar ba a yanzu kana zaton zan yarda in kara jefa kaina a duhu irin hakane ? Wa yan nan ka dauka auren kaddara da kurciya nayi dasu yanzu ko aure nake so na kece raini a kaina wai kasan yadda nake zaman kaddara da kazaman matan nan kuwa ? Ankai fa nida part dina habu har gudunsa nake wani lokaci ka dai sanni da kyankyamin tsiya tun farko sai gashi ubangiji yai min wanan jerabawan kazantar akansu. Ankai habu ko ruwa na dauka koda a gora ina jin kyankyaminsa haka inda zan kwanta sain kakabe da kaina in samu in raba in kwanta sabo tarin jakkanci irin nasu. Ni nakance ashe shiyasa suke abokai tun farko haline yazo daya ashe babu wace zata gyara wata a cikinsu ranan ina jin kannen Asmau suna mata fada wai har yanzu ashe tana nan da kazantar ta suna ganin kokarina da nake iya rayuwa cikin wanan bolar dasu haka ka duba fa Habu yan uwanta ma sun shedeta da kazantan tanan ashe haka. Habu yayi kasake yana sauren dan uwan nasa tare da kara tausayawa irin rayuwan daya tsunci kanshi a ciki da matan nasa don zai iya cewa dan uwan nasa sam bai morewa aure ba. Haka kuma wanan zancen da dan uwansa ke son fada mashi a yanzu matsalace babba don abin bai tsaya akan soyayya kadai ba game da yarinyar da yake son ya aura din . Yaji J din yayi huci gumi yana dan tartso mashi saman goshinsa tankar wanda yake cikin mumunan yanayi da sauri ya kara waigo dan uwan nasa yace. J wai meke farune dakai haka nifa gaba daya ka rudani ma ka wani sauya kamar ba kai ba wanan wace yarinyace haka wai take son baka wahala ? Ko kuma ita din ba musulma bace kake tunanen abinda zai biyo bayan zancen ga iyayyen mu ko kuwa sun hana maka itace an samu matsala daga iyayyen yarinyar ne ? Murmushin karfin hali J din yayi yace haba Habu ba wata bace fa yarinyar da sonta ya rikitani min tulin tunane