← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 306

Sashe 157

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin kwana biyu yaya Jafar yayi wani irin rama lokaci guda na kula da hakanne da safe dana sameshi a dakinsa zaune yana shafa mai zaisa kaya. Bandai yi magana ba inda na karbi man ina fadin ya kawo na cika ladana bai kiba ya mika min na shiga shafa mai a cikin sallo da hilla irin ta zolaya yana lumshe idona na gama na zabo mai kayan da zaisa naji yace dani . Rahama da kin bani kaya mara nauyi in saka zaifi don ba ko ina zani ba yau zan daije gida in dubosu don Asmau ta bugo min waya jiya wai idon jaririn yana ciwo kuma. Amma iya tace normal ciwone da akasarin yara keyinsa lokacin haihuwa zan dai je nagani idan zamuje asibiti dashine a dubashi yau. Allah sarki yaro ke nan ya shigo duniya ya fara karo da matsalolin rayuwa ke nan yanzu Allah ya bashi lafiya ai iya zata san hakan tunda sun saba da ganin hakan su. Na taimaka mashi ya zura rigan a jikinshi ya tashi muka fito falo ya zauna muka karya dashi din yau ba zaki fita ba ke nan nace sai zuwa shabiyu zan leka don banda lecture da safe. Zan dawo in kaiki ya fada nace zanbi motan kasuwa ai ka huta da sauri naji yace no don Allah kada ki soma banson hakan ba mutuncina bane aga matata a cikin motar haya. Ya mike tsaye yana fadin dolema in koya maki mota ai don gudun haka koda ibrahim bai gari zaki iya fita ke kadai ina ganin hakan zaifi sauki amma banson zancen shiga motar haya din nan tunda Allah ya hore min abinda zan iya saiwa kowan ku mota a yanzu. Nidai yadda naga ya dauki zancen da zafi yasa bance kalla ba koya min mota kuma na yaushe nidana koya a abuja kuma saidai naja bakina nayi shiru bance komai ba. Yaje can gida din dubasu nan suke magana kan yaron dasu iya yace a dai bari ya kaishi asibiti a dubashi inda abinda zasu bashi. Saidai yadda ya samu maijegon a jagalce ana mata kumshi da kitso yasa rai bace yace da kanwarta ta dauko yaron suje asibitin dashi da salima. An duba yaron an bashi magani suka dawo ya ajesu ya juya ya koma gida lokacin harna shirya ina jiran dawowanshi don har lokaci yaso ya kure min. Gaskiya da ba don irin hakan ana ganin tauyewa bane da sai ince nikan gaskiya haka yayi min daidai a gidan miji don irin zaman nan bakama tuna kana da kishiya sai idan kasawa ranka damuwa da hakan. Hausawa sunce kazantar da baka gani ba sunan shi tsabta to ban gani ba ban kuma damu da in sani ba tsakanin rayuwan can gidan da iyalinshi don haka nake jin kaina kamar banda kishiya duk da ba,a cika baki da zancen namiji da sai ince nidai a yanzu na cika ban sanarwa gaba dai idan zama yai zama a tsakanin mu abinda zai biyo bayan zaman namu nan gaba. Duk haukan saiba hankalina sam bai daga ba da rigimar ta don hakane ma na yanke shawaran ko ranan sunan ba zanje gidan ba duk da naga alaman hakan shima agareshi. Yadda yar uwata take tayar da hankalinta kan aurena da ya J ni a wajena sam abin ba haka bane kila dai don tana cikinsu tana gani kuma tana jin irin barazanan da sukeyi a kaina ne hakan ke daga mata hankali nikan a waje a yanzu da saiba ta gwada min hakan muka zoje da ita ko darrr kuma banji yanzu a kansu kamar farko da nake da tsoron a zuciyana. Dama ance da ka bari a raina ka kayi taba kishiya tsoro da mataki yafi ka fito kana sa,insa da ita a gaban miji irin hakan raini saiya shiga tsakaninku da ita gashi kuma yanzu na gani a kaina hakan gaskiyane. Haka kuma na yarda samun waje ga mace yana fitowa daga matsayin da miji ya daukeka dashine tun farko. Don sai ince yaya J bai bada daman da wani nashi zai kawo raininsa wajena ba don nasan da zuwa yanzu tuni mun gwada hakan da anty Saratunsu din tsakani da Allah dai ita bata kaunanane a zuciyarta don sai ince tafima kishiyoyin nawa daukan zafi dani. Nata sam bai damuna don bankula ta ba balle wani abu ya shiga tsakanina da ita don koda naje gidan banda gaisuwa ba abinda ya hadani da ita ranan . Ina kallonta yadda take bina da kallo mai kama da harara wanda ko wace take tayawan saiba batayi min irinsa ba a fuskanta don ita saiban banda shigan da nayi na samu suna fada a kaina bata yarda mun hadu ba a ranan don haka bancewa tayi min don da mijinta ta tsaya fadan da takeyi din. Karfe hudu ya daukoni zuwa gida inda na koma na samu tarin sayayyan da yayo na abinci nasan don in hakkura da school a ranan. Daki nashiga dan sallah inda na samu period dina yazo min don haka na watsa ruwa na fito na shirya kaina saiga kiran anty salima take fada min gobe zasu shigo nan zasu kwana don aikin da zamuyi din mun dan kai wani lokaci muna waya don ita idan tana waya bata gajiya da surutu koda baka bata amsa kuwa. Haka nake ganin ta daukeni kamar aminiyarta a rayuwa don tun ba zancen auren dan uwanta akaina ni kadai take fadawa damuwata in kuma bata shawara yadda ya dace da zancen. Saidai sam duk da ta girme min a shekaru ban yarda zancen mijina yana hadani da ita ba ko taso bugun cikina akanshi nakanyi dariya kawai in basar da zancen a wajenta. Mun gama na fito falo zaune na sameshi yayi shiru kamar me tunane har saida ya ban tausayi a raina ba karya koda na zargi hakan akwai damuwan yan uwa dana iyali a zuciyar bawan Allah nan saidai baida wanda zai fadawa danuwan nasa yaji sanyine kawai yake bari a zuciyarshi. Har na tako zuwa inda yake na shafa kanshi kamar yadda anty salma take min hira idan D dinta yana cikin damuwa itace takan zauna ta kwantar mai da hankali har ya gamsu ranan kuma biba bata nan don tace zataje gidansu kitso da kumshi daga school don haka ban sa rai da dawowanta ba don haka mu biyune kawai a gidan lokacin dagani saishi a lokacin. Ajiyan zuciya naji ya sauke yana kamo hannuna zuwa jikinshi na biye mashi na zauna saman cinyarshi ina fadin . Tunane yaya na kula tun shekaran jiya baka cikin dadin rai ina fatan dai bani bace nayi ma laifi haka don Allah ? Murmushi yayi yana gyara zamanshi ya dora kanshi a saman jikina yana fadin me zakiyi min Rahama da zai bata min rai kawai dai akan matsalan mu dasu mama kika ganni haka a kwanakin nan. Subbahanallahi na fada na zare jikina daga nashi nakai zaune saman kujera ina fadin har me yayi zafi haka yaya kaida nasan kana kokari akan kowa naka ? Kema da kika shigo rayuwata a yanzu kin fahinci haka tun yanzu balle su da aka haifemu a tare yanzu fissabillah za ace mama kawai yayanta mata ta damu dasu muko mazan ko oho ?. Duk da wani lokaci nakanyi tunanen kamar hakan ba laifinta bane laifin kawune yake kokarin shiga tsakanin ya rabamu da mahaifiyar mu a fakaice amma mama din bata gane hakab ba. Kawu kuma amma gaskiya da bai kyauta mata ba tunda shima aiya haifa kuma shima naga kuna girmama lamarinsa gwargwado. Yanzu ki duba akan yaya barakha ta sani a gaba dazun nan saida na nuna mata raina ya baci duk abinda nayi Rahama wai ace mama bata gansu da hakan ya ake son inyi don Allah ? Matar nan tazo garin nan da cin mutuncu na cinye masu kudin gadonsu dake hannuna ita da saratu suka tada hasumin sai in fito masu da kudinsu in basu suma suna bukata. Na basu kudinsu cikin salama ta dauki kudi takaiwa mijinta ya cinye ya kuma dauki mata kishiya Rahama banyi fushi ba tunda naga ran mama din ya baci na tayar dasu yaya Ai suje suga halinda take ciki ko zataji sanyi da zuwan su din. Bayan sunje din suka bugo suna fada min labari ba dadi na bayar da kudi asaya mata duk abinda ya dace anyi din tun jiyan wai amma kuma mama saita nuna yanzu meyasa na tura su yaya Ai da inna ? Don Allah hakan kuma laifine wai suwa zan tura idan basu ba amma sai mama ta nuna wai nayi hakan don in fallasa asirin sakintane kawai ? Umm,umm gaskiya akwai dai kila wani ya fadi wani abu kan zuwan nasu har bataji dadi ba ta nuna hakan na fada ina kallonshi. Naji tace wa zai fada banda yar banzan nan saratu data bisu nima hankali akanta yaje direct don nasan itacema zata fadawa mama wani abinda ranta zai baci don ban yarda na tura mata kudin sayayyan ta account dinta kona barakha din ba. Amma ba komai idan bakin cikinsu ya kasheni ai kowa zai huta sai su nemi wani kuma su kadarmashi zancena da Saiba nace ta tafi gidansu amma mama tace bata zuwa ko ina Rahama ? Haka zan zauna da mace a kullum ba ranan shiryuwa a gareta sai cin mutunci da tonon asiri ina duban saboda iyayyenta nayi hakkuri na kai wanan lokacin da ita hakana yanzu kuma matakin da nake son dauka mama ta hanani daukanshi akanta ya akeson inyi don Allah ? Nikan gabanane ya fadi da jin furcin mutuwan daya kirawa kansa nasan abu yakai mai ko ina a rayuwansa tunda har ya furta hakan . Cikin dan marairaicewa nake fadin don Allah yaya kabar ambato mutuwa akanka yanzu in ka mutu yanzu nima ai zan mutu ne nasani . Murmushi yayi yana shafo fuskana yace Rahama baki son in mutu ne mutuwa ai dole ayishi tunda munzo duniya ko ? Shiru nayi ina tunane tare da jin wani zafi yana fita min a jikina lokaci guda ni kadai nasan irin tunanen da nayi cikin dan lokacin kafin muryanshi ya dawo dani da yake fadin. Ba lafiya ke jikin
Chapter 157 · 0% Book details