Sashe 177
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A sanyayye na amsa mashi murmushi naji yayi sabanin fadan dana zata zai min a lokacin yana fadin ashe yar kokawa na aje agida ban sani ba ? Abinda ya fada din yasa na sauke murmushi lokaci guda yace baki kyauta min ba Rahama with your condition zakije kina fada haka idan wani abu ya sameki fa baki tausaya min ne don Allah ? Kayi hakkuri don Allah ya daurone idan ban rama ba a lokacin sai su dauka ina tsorone shiyasa na rama dukan da sukayi niyar yi min din. Nasani amma kinsan illan hakan ai ina daukanki mai hankali sai gashi kuma kina son kifi Saiba hauka agaban kowa kuka dinga fada kuna zubar da mutuncin ku why zaki biye masu kuyi hakan don Allah. Na sake fadin kayi hakkuri yaya muryata tana nuna alaman karya a lokacin is ok amma don Allah kada a maimaita hakan naji komai nasan ba laifinki bane zuwa gidan kuma har in zai kawo matsala idan ban nan don Allah Rahama ki daina. Katseshi nayi da fadin saboda su ba zanyi zumunci da yar uwata ba ke nan banje donsu ba kuma ban takalesu ba sune suka kirkiro abinda zamuyi fitina har haka ai. Nasani amma itama Maria din dole subar gidan ai tunda har haka ya fara faruwa yanzu haka mun gama magana da habu zai gyara gidansa su koma ciki zuwa next week in sha Allahu . Bance kicewa kowa komai ba duk da ance mama da kawu sun sameki a gida saidai banda fargaban hakan tunda iya tana gidan a tare dake yasa wanan bai dameni ba amma ki kula don Allah hakan ba mutuncin ku bane please ? Nagode na fada sai nayi shiru shima dan shirun yayi ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya a bangareshi kafin yace ina dai baki ji ciwo ba kema ? Banji ba na fada a takaice yace sure nace umm,umm Allah ya tsare ya jikin ita maria din duk da ance kun dai fasa mata kaya amma ba a tabeta ba kinga illan fada ke nan bakyau don Allah. Tausayi ya bani yadda yake maganan sai naji ba dadi a raina karon farko da nayi nadaman faruwan abin kenan a kasan zuciyana wanda hakan ya ja na rage irin zafin da nakeji kasan zuciyana nasu. Washegari saiga maria a gidana ita da yaya Habu sukazo nan muka zauna falo dasu da iya nan naji yadda ransa ya baci ya fada ya kara zai bar gidan tunda mama bataga laifinsu ba sai na matarshi da yar uwarta. Habu kuyi hakkuri akwai abinda ku baku sani ba game da uwarku ina nan ina mata addua Allah ya kwatota daga kaidin da take ciki a yanzu duk wani abinda za a fada a yanzu banzane don bai tasiri azuciyarta don tana ganin ita daidai take. Amma kaga Dauda da matarsa hansatu ka barsu nan inda ka gansu su dade sunawa uwarku bandan kasa. Yanzune abin yake yawo akanta haka kuma yar nan matar Jafaru itama da akwai wani shu,umancin datayiwa Dubu a zatona wanan abin shine duk ya rikita kanta a yanzu din. Kaga kuwa wanan abune dake son addu,a don ba yarda da hakan zatayi ba koda an fito mata fili an lurar da ita zata iya mussan hakan mutum abin tsorone. Ni kaina a lokacin ai hafsatu bata barni ba nasan komai ido na zubawa gudunsu tunda yadda suka so dai bai samu ba. Sunyi hakane don ku da yan uwanka ya kasance duk wani nema naku yana a hannusu sai yadda sukayi daku da uwarku din sai gashi ku ba a kama kuba ita abin yafi shiga jikinta. Nina sani iya don ko kowa bai yarda ba nina yarda kawu zai iya hakan fiyema da hakan sai yayi don irin yadda yake muna wani lokaci sai mutum yakai zuciyarsa nisa don azauna lafiya. Yanzu dai zan bargidan ba zan zauna ina gudun zuciyarsu ba ninawa yana baci a kullum don haka zan kwashe kawai na bargidan ina ganin shine mafita a wajen mu baki daya. Ita kuma saratu kai salima na fadawa yaya su fito da maza a daura masu aure kowa ta kama gabanta zaman ya isa hakana musanman ma saratu da duk wani fitina itace ke kawoshi a gidan nan kuma mama bata yarda da hakan . Yanzu da safen nan saida muka kwasa da ita wai mun kadarwa saratu bamu kaunarta abu kadan ace saratune har tana batun yi min kuka fa iya wai akan saratu. Sai naji iyan tace kafadawa uwar taku zancen tashin naka yace ehh to cikin fada na fadi amma ina ganin bata dauka da gaske nakeyi ba. Don kyata da bala,i irin nata wai a falona Nusaiba zataje fada duk sun fasa min kayan falo amma duk mama bataga laifin hakan ba sai fada rakeyi wai Rahama tazo har gida tayi masu rashin mutunci. Me yaranan suka tarewa mama haka don Allah iya ta nisa tana fadin habu kayi hakkuri na fada maka inda matsalan yake don haka addua zamu bita dashi a yanzu. Ya juyo wurina yana fadin ke kuma baki da hankaline da kika biyewa haukansu Rahama idan suka illataki fa badon Allah ya doraki akansu ba yadda ake fadi sun tarar maki ai saisu nakasaki a banza tunda ba wajen hukuma za a kaisu ba a daukar maki fansa. Don haka daga yau ki kama mutuncin ki dama ita abinda take nema ke nan abinda za ayi ta bata maki record a idon mutane ba haka kikaga yar uwarki tana zama dasu ba. Bayan haka ke kinsan yadda akai auren ku da J dole haka ya faru tsakanin ki dasu don ma ita Asmau a yanzu ta daina saka kanta cikin iskancin Nusaiba don na kula ita a yanzu bata irin abubuwan nan don haka kada nakara jin hakan daga gareki. Duk abinda zatayi ai yanzu tunda ta gwada ba sa,a a wajenta aiba zata kara bari su hada jiki ba kuma da dai ace ta samu sa,antace bata da sauran numfashi kuma a gidan nan yanzu. Sai Allah ya kawo saukin abin kika rijayesu don haka yanzu iskancin zai rage akanki saidai ta fito wani hanyar kuma nan gaba. Ai tasha fadancewa saita wullakantani dake a gaban kowa amma ban taba tsayawa na kulata ba ina jiran ranan da zata kawo iskancin ta akaina ta gane kurenta bata san naki dan maline ba don nafiki hauka kyalesu kawai nakeyi. Maria data karbi zancen iya take fadin hakan sai iyan tace gara dai kada akai ga hakan ai yanzu na fada maku zasu shiga hankalinsu sosai tunda basu sha da dadi ba. Na daiyi fama da tsamin jiki tunda jikin a yanzu ba wahala irin da can baya inda gadan gadan ya Habu ya shiga gyaran gidanshi da zai koma da iyalinshi. Unguwa dayane amma akwai dan nisa da inda nake saida yayi wani dawowan ya samu mama da zancen tarewansu gidan akan ga gobe. Me kake fada Habu zaka kwashe ka koma gidanka watau ban isa da kaiba yanzu saida yaran nan sukai nasaran raba min kanku a gidan nan ? Wasu yara kuma mama ta kalloshi a yatsune tana fadin wasu yara banda shu,uman yaran nan da kuka dauko min a gida ? Dama gurinsu kenan su raba min kan yayana gashi ko sunyi nasara na farko a gareni shigowan yaran nan cikin ahalina bai haifar min da komai ba sai tarin bakin ciki da takaici . Kowa yasan asalin nono dama daga ruga yake ashe gaskiya ake fada akan fulani ba a fadi karya ba duk wanda ya auri yar filo sai yabar kowa nasa gashi kuwa nagani a kaina. Saita fashe mashi da kuka ya mike ya fice daga dakin bata kara ganinsa ba saida yammane saratu ke fada mata da gaskiya yakeyi fa tafiya zasuyi don ashe har sun kwashe duk wani abin amfani nasu sunkai wancan gidan. Ranta ya baci ta mike tsaye da sauri saratun ta tareta tana fadin mama kada ki fita don yaya ya ganeni zaice nice na fada maki. Yace mana idan yace fa shi har ya isa ince ban yarda da hakan ba yace min don me koshi jafar daya dauki wanan yarinyar ya kaita can tunda abin ya zamo iskanci ai nan zai dawo da ita dole yanzu. Tunda tana ganin hakan da yai mata kamar tafi kowane a yanzu har take iya ganin zata tako har cikin gidan nan taciwa mutane fuska jiransa nakeyi ya dawo garin nan ai,,, Sallaman ya Habu dake shigowa dauke da dansa a hannunsa sai maria dake bayanshi sabe da jakarta na hannu shiya saka suka juya suna kallonsu. Zama yayi yana gaida ita ta amsa a dakile kafin yace yaune zamu tafi wancan gidan mama na fada maki zamu koma gidana to yaune komawar tamu insha Allahu. Kai habu saboda ka auro yar gwal mai takobin raba zumunci zaka ture dokana kace zaka bar gida don ra,ayinta tunda su da manufa suka shigo cikin mu dama ? Meye laifin Maria anan mama tunda ba itace ta gina min gida ba ninayi ra,ayin hakan don haka a barni da shawarana don haka nake son tsarina. To ba zaku ko ina ba kaji na fada maka wace zata iya zama a nan ta zauna wace bata iyawa kuma hanya a bude yake ta fice ta kama gabanta. Ashe gaskiya da ake fadin dangin filo dangin bala,i yanzu don matarka har zaka iya kyatare dokana don kada ranka ya baci. Mama ba ra,ayinki nazo nema ba a yanzu don na riga dana gama shirina ba zan bar iyalina gidan nan kina kallo ana ci mata mutunci ba tare da daukan mataki ba. Yanzu zanyi abinda ya dace a zauna lafiya kuma zakice ban isa ba a zatona hakan abin farin cikine a wajenki ai mama tunda har Allah ubangiji ya hore muna muhalin kanmu haka da taimakon dan uwanmu dake son cigaban mu a rayuwa. Ashe hakan ke a wajenki ba abin godiya bane yau don danki ya samu farin ciki mama kinfi bukatan ganin rayuwan mu ko yaushe a tauye ? Habu ni kake musayan harshe dani yau haka kan wani tsari da aka doraka sama yace ba wanda ya dorani na fada