← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 227

Sashe 98

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin sauyawar numfashinta ne ya sanya shi É—ago kai, sai ya ga kuka take yi sosai, nisawa ya yi tare da zuro tongue É—insa waje, hawayen nata ya fara lashewa wanda ya sanya ta dakatar da kukan cak. Da sauri ta waro idanunta waje, kai tsaye sai a cikin nasa idanin very close to her haka. ÆŠan zabura ta yi, lokaci guda kuma ta ji tsoro ya shigeta, bata san tsoron me ba, kawai ta ji tsoro ne.

Cigaba da lashe hawayen nata ya yi bai damu da tana zazzare mashi idanu ba. ÆŠan lasar lips É—inta ya yi da ya gama lashe hawayen, sannan ya dawo da kallonsa gabaÉ—aya a kan idanunta, suna fuskantar juna, suna shakar numfashin juna. Saura kaÉ—an ta saki mashi fitsari a wando, take jikinta ya soma kerma, zazzare idanu ta cigaba da yi a kansa.

"Baby, watau ni ne baki yarda dani ba ko? Ban isa in hanaki abu ba ko? Bincike kike yi a kaina? Baki tinanin hakan zai iya affecting rayuwata ne? Baki san dik abin da ake ɓoyewa yana da haɗari bane? Baki yarda da daddynki ba? Ke fa yakamata ki rufe asirin daddynki, amma kece kike ƙoƙarin ɗaukana hoto dan ki turawa duniya ko?". Ya ɗan dakata yana jinjina kai.

Gagara motsawa ta yi, jikinta dik a mace, ba zata iya yin magana ba. Kara matso da face ɗinsa dab ita sosai ya yi, kara zaro mashi ido ta yi, shi kuma ya ɗaure fuska tamau tare da cewa. "Ban yi zaton zan ce ga abin da nike so ki yi gaban kanki ba, idan kina son sanin waye ni why ba zaki yi facing ɗina ki tambayeni ba? Meyasa zaki tambayi wata bare? Good!". Ya faɗa tare da saketa, a hanzarce ya miƙe, jefa yai da wayarta a saman bed.

"Ki nuna hotona a koma ina ne ki tambayi waye ni idan kin yi ra'ayi, amma ki sani ko mutuwa na yi a kan hakan kece sila". Yana kai karshe ya nufi hanyar fita da sauri tamkar zai tashi sama...... Shiru ta yi tamkar mara lafiya, ta zuba mashi ido har ya fice. Yana fita ne ta samu damar fashewa da kuka, a ranta take jin bata kyauta ba, meyasa zata nemi dole sai ta binciko waye shi tin da ba zaluntarta yake yi ba? Meyasa idan tana son sani ma ba zata tambaye shi ba kamar yadda ya ce ba?.

Da sauri ta miƙe ta ɗauko wayar tata. Jikinta har yana rawa wajen laluɓo number ɗinsa. Kira ta fara danna mashi tana ruwan hawaye. Na farko ta kira har ta katse ba'a ɗaga ba, na biyu kuma yana shiga ya katse kiran, na uku ma haka, da ta takura mashi sai ya kashe wayar gabaɗaya, ta kira ta ji switch off.

Take jikinta ya kara mutuwa, ta yi nadamar ɓata mashi rai har ya yi fushi da ita. Da gudu ta fito ta nufi room na Madam tana kwala mata kira. A lokacin Madam tana cikin toilet, hakan yasa ta zauna a gefen gadonta tana jiranta.

Tana zama sai ga wata mata ta shigo room É—in bisa jagorancin Aisha, matar ma tare take da wata budurwa wacce a kallah zata kai 23 haka. Cike da mamaki Seraphina ta bisu da kallo kafin ta ce. "Aisha who are those people?".

Kallon tsab matar ta yi wa Seraphina kafin ta ce. "Wannan ita ce yarinyar kenan?". Da alamar walaƙanci da ƙasƙanci a maganar matar. Jinjina mata kai Aisha ta yi kafin ta ce. "Ita ce mai gidan". Taɓe baki matar ta yi tare da cewa. "Ina Aunty Rohisha ɗin ne?".

Aisha ta amsa da. "Tana toilet"...... Ganin yadda matar ta kalleta ya sa Seraphina ta É—an sha jinin jininta, a sanyaye ta ce. "Good morning".

Matar ta amsa a takaice tare da wucewa ta haye saman bed ɗin Madam ta yi kane-kane har da miƙe kafafu tamkar wata ballagaza ta zauna a kasuwa. Matashiyar yarinyar dake tare da ita ce ta kariso wajen Seraph, sai da ta dallah mata wani irin harara kafin ta ce. "Give me a way to pass".

Cike da mamaki Seraph ta kalli filin dake gadon, dik bai isheta hanyar wucewa ta haye saman gadon ba sai in da take? To amma da yake ba bakuwar zafi bace sai an taɓota sosai sai ta miƙe ta basu waje, ta koma saman sofa ta zauna, ita ba don tana son faɗawa Madam halin da take a ciki bama da ta bar room ɗin.

Aisha ma waje ta samu saman sofa kusa da Seraphina zata zauna kenan muryan matar ta katseta da cewa. "Ke wuce ki fita a nan"........ ALLAH sarki, suna nunawa Aisha kyara ne dan marainiya ce Madam ta É—auko take reko, abu ba abu ba sai su ce mata maganar family ake yi.

Wannan mata kanwar Madam ce uwarsu É—aya ubansu, wannan budurwar Æ´ar kuma Æ´arta ce, basu da mutunci ga shegen son duniya, sun ji Madam ta samu matsugunni a CRYSTAL PALACE ne shiyasa suka ce suma dole su zo aci arziki da su, yanzu dai wai sun dawo gidan da zama.

Miƙewa Aisha ta yi zata fita fita jiki ba kwari Seraphina ta riketa tare da cewa. "For what reason zata fita? Is it your room? Su waye ku nema da zaku zo ku samemu a ɗakin mom ɗinmu ku ce ta fita? Is it your room?". A kule ta faɗa tana kallon matar, jinin IRON FIST basa ɗaukar rainin wayau, da farko ta ɗauka bakin arziki ne shigasa tai masu shiru, amma da ta ga basu san arziki ba shi ne ta gwada masu jinin IRON FIST take.

Budurwar ce ta amsa da. "Ke baki da tarbiya ko? Babban mata zaki faÉ—awa haka? Bata haifeki bane? Ko a gidanku babu manya ne?"..... Wani irin mugun harara Seraphina ta dallah mata kafin ta ce. "Keda gidanku suke da manyan ai naga basu baki tarbiyar adalci ba, kuma basu koya maki yadda ake magana ba". Ta faÉ—a tana zazzare mata ido, irin ta san bafa tsoronta take ji ba.

Kallon juna yarinyar da mamanta suka yi, sun gano Seraphina ba wacce ake takawa ta taku bane. Daidai lokacin Madam ta fito daga toilet, ta yi wanka har ta shirya a ciki dan da kayanta ta shiga, cikin arabian dress ta shirya.

Ganin suna musayar yawu yasa Madam ta yi saurin cewa. "Safiyya me haka? Daga zuwanki? Ke ba zaki canza hali bane wai?".

Wannan budurwar ce mai suna Suhana ta ce. "Mommy Ummina bata da laifi, wannan yarinyar ce ta zageta"...... "Ya isa haka Suhana, babyn daddy me yakefaruwa ne?"...... Sake hannun Aisha Seraph ta yi tare da miƙewa ta isa gaban Madam, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Mommy daddy yana fushi dani, ya tafi cikin fushi, kuma ina ta kiransa baya ɗauka, daga karshe ma ya katse kiran".

Riko shoulders É—inta Madam ta yi. "Jeki room É—inki ina zuwa sai ki faÉ—a mun me kika yi mashi ya yi fushin dan mu san daga in da zamu fara gyara, Aisha ku je da ita". Ta kai karshe tare da saketa. Da sauri ta juya ta nufi waje ba tare da ta sake kallon in da suke ba, Aisha ta rufa mata baya.

Suna fita Madam ta kalli Safiyya tare da cewa. "Ke baki da hankali ko? Sai kin ɓata mana dik wani shirinmu a kansu kin sa asirinmu ya tonu ko? Yanzu idan kuka fara nuna mata kiyayya kuka ja aka koremu ba shikenan komai ya lalace burinmu ba zai cika ba ko! Meyasa baku da tinani ne?".

A taƙaice Aunty Safiyya ta ce. "Kai Aunty Rohisha, ni fa yarinyar ne take bani haushi, na tsaneta daga kallon farko, na kasa ɓoye tsanar ne yasa na nuna halin"...... Nufosu Madam ta yi tana faɗin. "Gara ki koyi danne abu, dan wlh a kan wannan yarinyar babu irin matakin da ba zasu ɗauka ba, zai ma koremu a gidan nan, kada ki manta saboda ita ya ɗaukomu dan ta yi farinciki, dan haka dik abin da kake son cimmawa a hankali zaka bi da shi har ka cinma, bugu da ƙari ina son ki san cewa gidan nan gabaɗaya kewaye yake da camarori, cikin bedrooms ɗinmu ne kawai babu camera, amma bedroom na Seraphina akwai ɓoyayyen Camera, ranar da na shiga unexpected ina ɗaga kai jikin bulb na wuta ta ƙasa naga karamar camera, da alama basa son Seraphina tasan da camerar ne a wajen yasa ya ɓoye, amma sauran ɗakunan gidan babu, su parlo, kitchen har balcony dik akwai Camera, dan haka ku yi taƙa tsantsan, ku kuji shiga harkar Seraphina a gaban camera".

Kai suka jinjina alamar gansuwa, sannan Suhana ta ce. "Mom gaskiya CRYSTAL PALACE duniya ne kuma karshe ne, amma kuma gaskiya suna ji da yarinyar nan sosai, dubi irin daular da aka zuba mata, sannan Camera ta ko'ina dan kula da dik wani motsinta, tsaro sai ka ce zasu iya hana mala'ikan mutuwa É—aukar ranta in ya zo?". Tana É—aure fuska alamar hasada dan bata samu irin hakan ba ta faÉ—a.

Madam zata yi magana Aunty Safiyya ta rigata da cewa. "Gaskiya Aunty Rohi kin iya ɓadda kama, ni ba dan na ji muryanki bama ba zan gane ke bace, kin iya sanya fuskar boge wlh, kuma kowa ya ɗauka fuskanki ce fa". Ta kai karshen magana suna murmushin dake kama dana mugunta. Madam ta ce. "To ya zan yi, biyan buƙata yafi kwana masallaci, dole in yi basaja, dole in ɓadda kama in shiga jikin Seraphina dan cikar burina".

Shiru Aunty Safiyya ta yi tana tinanin makudan dalolin da ta karɓa kan ta fito masu da Seraphina daga CRYSTAL PALACE, a ranta ta fara tsara yadda zata shawo kan lamarin, ta samu ta ja Seraph wajen CP ɗin. Watau sun san a cikin CP dai kam basu isa shiga su ɗauketa ba, dole sai an fito da ita waje, lallai kuwa akwai gagarumin matsala, meyasa suke neman Seraphina? Su waye su? Madam Rohisha da ɓadda kama for what? Meyasa ta shiga rayuwar Seraph? Me manufar su Safiyya? Zasu yi nasara ko kuwa?. Uhm mu leƙa WS-HOSPITAL mu dawo.

---------------------------🔥

WS-HOSPITAL.

Bayan wani lokaci, zan yi skipping na labarin ne kaÉ—an saboda wani dalili da a gaba zaku gane!.
Chapter 98 · 0% Book details