Sashe 66
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Watau kun san me mutane? Su Lion karshe in dai a ɓangaren tinani da hangen nesa ne, ga karfin hasashen dake tabbata, wlh dik hasashen da suka yi tabbatacce ne. Ni dai a jikina ina jin Avaris exactly Nigeria tamu ta gargajiya, ku me kuke jinta? Amma mu je zuwa, alkalami ya fi tokobi! Kumun addu'ar in samu cikar burina na warware gaskiya a cikin wannan labari kamar yadda na so, wlh complete storyn nan ina ɗaukarsa tamkar gaske ne sai abin da ba'a rasa ba, tamkar yadda kwakwalwar su Lion take da kaifin hangen nesa da hasashe game da tinani haka ƙwaƙwalwata take, dikkan abin da zai faru da idon basira nike kallonsa, ina fatan dik wacce zata karanta littafin nan daga yanzu ba za'a sake raina mata wayau ba!.
Shiru Lion ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce. "Wannan abu ne mai sauƙi, manyan ƙasar sun zauna meeting na sirri da manyan ƴan kasuwa dake shigo da kaya, sun umarcesu da ɗaga farashin kayan abinci ta yadda talaka ba zai iya sayan foreign food ba, daga nan su kirkiro fitinar ƴan ta'adda suna shigowa sai a rufe wasu bodojin ƙasar". Ya ɗan nisa kafin ya cigaba da cewa.
"Idan suka ɗaga kayan abinci suka kuma rufe boda sai su ƙarawa takin noma kuɗi ta yadda takala dole ya ci bashi a lokacin yin nomansa, dan kuɗin da ya lissafa zai kashe a farko yanzu komai ya tashi ya ninka kuɗinsa, kuma dole ya saya dan yana buƙata, kafin ya gama noma bashi tai mashi yawa ta yadda yana cire amfanin gona dole ya biya mutane bashinsu, idan ya noma buhu goma ne, to buhu 6 zai tafi a biyan bashi, saura huɗun ba zasu ishesa ya ci a gida da iyali ba bare har a je ga lissafin ajiye wani kuɗin dan noman shekara mai zuwa, kaga kafin wata shekara ta zago ya sake cin bashi dan ciyar da iyalinsa, lokacin noma ya sake cin bashi dan nomawa, idan last year ya samu ragowar buhu 4 to this year in ya biya bashi da kyar ya tsira da buhu 2, a haka ake haifarwa da ƙasa mugun yunwa da wahala, shiyasa zaka ga kaya a wajen Avaris da mugun arha, amma a cikin ƙasan ya ninka kansa sau biyar".
"Kaga buhu biyu bai wuci ya ci na ƴan kwanaki ba, sun kare, kaga bashin da zai sake ci wannan shekara da ta fi ta wancan shekara kenan, idan ya ci ya gama noma abincin da ya noma ba zata isa ya biya bashi bama bare ya rage na ci, daga nan zai fara gudun biyan bashi, ya ci ba zai biya ba saboda babu yadda zai yi, idan ya biya bashi da abincin da zai ci a gida, yunwa ta mamaye ƴaƴa da ƴan uwansa, daga nan yunwar take farawa har ta mamayesu ta ko'ina, ga bashi da rashin madogara, makarantun yara ya tsaya, rashin sana'a, abubuwa su caƙuɗe, yunwa tasa dole yara su fara ɗauke-ɗauke, daga nan shaye-shaye". Lion ya dakata hankalinsa a kan computersa.
Champion ne ya ce. "Wannan ma naga ba zanga-zanga rashin tsaro suke yi ba bayin ALLAH, zanga-zangan yawan faɗuwar tamkoki mai da ake samu ne a kwanakin nan yana masu ɓarna, yana kashe masu al'umma sosai, shi ne suke zanga-zanga kan gwamnati ta biyasu gidajensu da wata tankar mai ta ƙona".
Guru ne ya kalli Champion da ya ajiye wayar dake hannunsa yanzu, dama tin É—azun da kuka ga ya yi shirun nan sauraren wayar da Seraphina take yi da Rimsha a yanzu yake yi, yanzu ta sake kiran Rimsha tana faÉ—a mata tana tsoron gidan, kuma ita kaÉ—ai ce, tana kuka tana faÉ—a mata. GabaÉ—aya sai ya ji hankalinsa ya tafi kan ya je ya ganta, yanzu da suka gama wayar ne shi ma ya ajiye wayan nasa ya mai da hankali kan aikin da suke yi.
Bai san dik abin da yake yi Lion na sane da shi ba, su fa mata haramum ne a wajensu, sun haramtawa kansu, kada ku É—auka da wasa ake yi! Da gaske suke yi, yanzu idan har Lion ya kama Champion kan macece take É—auke mashi hankali zai rabasu ne, saboda ba zasu tsayar da aikin da suka fara ba, kuma ga shi kunga zancen Lion ya fara tabbata, mata suna da É—aukewa mutum hankali, kunga tin É—azun maganar arziki ake yi shi kuma Champion ya tafi jin gulma na hirar su Rimsha, sun É—auke mashi hankali.
Guru ne ya ce. "Gaskiya kwana biyun nan ana samun fashewar tankar mai a Avaris sosai, kuma tana sanadin rayuƙa da dama, to motocin man ne dik sun mutu, amma manyan ƙasar sun kasa sayan sabbi". Champion ya ce. "Kuma kansu zasu yi wa idan sun sayi sabbin ma, amma ba zasu saya ba".
Nisawa Lion ya yi tare da ɗaukar cube ya fara murɗawa, ya koma baya ya jingina da jikin chair da yake kai a zaune, sannan in cool way ya ce. "Da balain son kuɗin nan nasu kuna tinanin zasu taɓa yarda su karɓi asara ne? Kada ku manta fa idan man ya zube asararsu ce, to zasu yarda haka kawai su yi asara ne?".
Shiru su Champion suka yi suna nazarin kalamansa. Katse masu shirun ya yi da cewa. "Shi kansa faɗuwar tankan man plan ne ga ƴan ƙasa"...... Champion ya ce. "Confirm, suna sake tankar ne saboda abubuwa biyu, na farko ko su juya akalar tinanin al'umma zuwa kan wannan case ɗin su aikata wani babba laifi, ko kuma su faɗar da ita domin kashe mutanen dake yankin, da gayya suke faɗar da ita, ko direbobinsu basu sani ba, dik shiri ne, in ba haka ba ba ta yadda za'ayi su dinga tabka asara haka, yadda suke mugun son kuɗin nan".
Guru ne ya ce. "Na fi tinani suna yin hakan ne domin su ɗauke hankalin ƴan ƙasa su aikata wani babban laifi".
"Dalilai uku yasa suke hakan, na farko dan ɗauke hankalin ƙasa, ko zasu fitar da dukiyar ƙasa kamar su gold zuwa wani waje, ko zasu shigo da wasu manyan mutane cikin ƙasar, ko kuma zasu fitar da ƴan matan da suke sacewa ana kaisu waje dan kasuwanci da su ta hanyar karuwanci". Cewar Lion.
Jan numfashi Lion ya yi tare da sauƙewa a hankali kafin ya cigaba da cewa. "Idan sun shirya jefar da tankar mai, akwai wata chemical da ake cewa hydrochloric Acid, suna saita daidai in da suke son tankar ta fashe ne, sai su yi diluting ɗinsa da ruwa, su zuba ruwan da zai daidata chemical ɗin ya kuma ɗauki tsawon lokacin da zai isa wajen can ɗin, sai su zubawa tankar mai ɗin ta daidai in da suke son ya fashe, idan drivernsu ya ɗauki motar lafiya lou zai tafi da ita, wannan chemical ɗin tana cin wajen da aka zuba ɗin a hankali, sai ya isa in da suka tsara unexpected zai ga tankar ta fashe mai ya fara zuba, za'ayi duban duniyar nan a rasa dalilin fashewar tankar, dan chemical ɗin sam bata nuna alama, haɗewa sa ruwa take". Ya dakata yana sauke ajiyar zuciya.
"Yanzu me mafita?". A cewar guru. Champion ne ya amsa da. "Yakamata mu tsaya tsayin daka dan tsabtace Avaris, gurɓacewarta ta yi yawa over, ga cin hanci ta yawaita"........ Guru ne ya amsa da. "To jami'an Avaris ai dole ake tilasta masu cin hanci, shi ma wannan shiri ne domin jami'an su zama karnukan farautarsu, dole suke tikasta jami'an Avaris da su yi masu biyayya ta hanyar azabatar da su da karamin albashi, idan suka basu albashin da ba zai iya ciyar da su ko na sati biyu ba, kunga yunwa zata sanya dole su fara karɓar cin hanci dan ciyar da family ɗinsu, dole a wannan lokaci zasu karɓi dik wani aiki da na sama da su ya basu dan su samu abin da zasu baiwa ahali, yunwa ita ce babban makamin da shuwagaban Avaris suka rike wajen sanya kowa ya bautawa buƙatunsu, talaka na fama da yunwa an kawo mashi aiki da zai samu 10k dole zai karɓa ko dan yaran da ya baro a gida suna jiran baba ya dawo ya kawo aci abinci". Ya kai karshe cikin tsananin takaicin abubuwan dake faruwa a duniyar yau.
Nisawa Lion ya yi tare da cewa. "Ba laifin shuwagabannin Avaris bane, suma umarni ake basu ta yadda idan basu yi ba za'a kashesu, WORLD SYSTEM ita ce matsalar duniya gabaÉ—aya, kowani shugaba ya hau mulki dole zai bi umarninsu ne in har yana son ransa".
Guru ne ya ce. "Wai to su ɗin su waye ne?". Champion ya ce. "Mutane ne kamar kai"....... Lion ya amsa da. "Haɗarinsu kuma ya fi nuclear, su ɗin ba mulki suke yi ba, ba shugabanci ba, hasalima basu a siyasa ko sarauta, su akewa laƙabi da masu naɗa mai mulki, su suke zaɓar shugaban da suke so ya yi mulki a kowace ƙasa, kuma dole ya yi masu biyayya ya aikata dik abin da suka sanya shi, idan ba haka ba, su kashesa ko su ɓatar da shi, su ɗin su ne ke juya duniya a yau, sai abin da suka so mutane su sani suke sani". Ya ɗan dakata yana fito da bayanai a kansu a cikin computer dake a gabansa, bayanai ne da ya sha wahala, ya shafe tsawon lokaci yana haɗasu, dan shirya mission na musamman a kansu.
Champion ne ya ce. "Suke juya sojoji ta sigar da babu wanda zai sani har su kansu sojojin, suke juya manyan da suka amsa sunansu manya, suke juya harta talaƙawa, dik wata ƙasa a duniya da kuke ganin kamar suna da power ko su ke juya duniya to ku sani suma umarni suke karɓa daga wannan team na WORLD SYSTEM ɗin, wannan WORLD SYSTEM ɗin su ke tsara komai da suke son ya gudana a kowacce ƙasa, baku ji sunansu ba? WORLD SYSTEM, su biyar ne, amma mutum ɗaya ya fi dikkan shuwagabannin manyan kasashe girma da karfin iko game da haɗari, kowa a karkashinsu yake ba tare da kowa ya sani ba".