← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 227

Sashe 88

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daidai lokacin Aryan ya tashi tsaye, zuciyansa na tafarfasa ya nufi Lion gadan-gadan, glass table ɗinsu ya ɗauka ya makawa Lion a gadon baya yana faɗin. "Baka son gaskiya, saboda ka tsani mata shi ne a kansu baka taɓa kyautata masu zato, ba zaka yi tunanin kirki a kan wannan al'amari ba, ko bata da ƴan uwa za'a iya tura mata kuɗi". Ya faɗa ne kawai amma shi kansa yasan ba haka bane, lallai kuɗin da aka tura account na Dr daga babban account mai tsaro ya fito, shi kansa Aryan ɗin yasan da kamshin gaskiya a batun Lion, amma soyayyar Seraphina yasa lallai sai ya wanketa a gaban Lion.

Da karfi Lion ya juya ya shakesa, ya ɗagasa sama, sannan ya buga shi da ƙasa kafin ya ce. "Ba zan yi tinanin alkhairi ba in dai akan mata ne! I hate them and also you now, i don't want to see your face!!"........ Wani irin azaba Aryan ya ji, hakan yasa ya ɗan rintse idanu, da kyar ya iya miƙewa, cikin fushi ya sake ɗaukar flower decoration ɗinsu ya bugawa Lion a kai ta baya, nan Lion ya juyo suka fara gwabza faɗa tamkar mayunwatan zakuna.

Shi dai guru rungumo hannayensa a kirji ya yi yana kallonsu, saboda yasan bafa zasu rabu ba, shi kaɗai bai isa ya rabasu faɗa ba, idan suna yi sai sun jigata dan kansu sun hakura, amma batun rabasu ma bata taso ba. Cikin ƙanƙanin lokacin suka wargaza ɗakin kaca-kaca, suka fashe dik wasu glass dake wajen, suka lalata komai, sun jiwa kansu ciwo sai jini suke zubarwa, Aryan yaki yarda da maganar Lion shi me Lion yaki yarda da maganarsa, kowa gani yake shi ne mai gaskiya.

Yau sun jima suna faɗa saboda magana ce kan abin da ya shafi zuciya, sai da guru ya ga Lion ya ɓaɓɓako Tv ɗinsu daga jikin bango zai bugawa Aryan dake baje a kasa yana numfashi sama-sama ne ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar dannawa da gudu ya rike Tv, suna cikin fushin nan zasu iya kashe junansu ne ma basu sani ba, kun san zuciya bata da hankali wani lokacin.

Ƙoƙarin kwacewa Lion ya fara yi dan har yanzu zuciyansa tafarfasa yake yi, sanya karfi guru yai, suka fafata, da kyar ya kwaci Tv ɗin saboda Lion ɗin ma ya jigata babu karfi sosai a jikinsa, so ya samu damar kwacewa kafin ya yi ta mazan shigar da Lion cikin wajen balcony ya rufe glass door ɗin. Da gudu ya zo ya ɗauki Aryan cak ya saɓa a saman shoulder ɗinsa ya fita waje. Yana fita ya rufe kofar har da sanya key, a daidai lokacin Lion ya rugurguza glass door na wajen balconyn ya dawo cikin ɗakin, sai huci yake yi, kun san ance idan rai ta ɓaci sai hankali ya gushe to haka ne.

Ɗayan room dake kusa da nasu guru ya kai Aryan, ya kwantar da shi saman gado tare da shiga cikin drugs room ɗinsu, cikin gaggawa ya ɗauki wata allura, jikinsa har yana rawa wajen fara ƙoƙarin haɗa alluran nan, yana jiyo Lion na ƙoƙarin ruguje door room ɗinsu, dama su biyun nan zuƙatansu na da wuyar sarrafuwa idan ta kwaɓe masu, shi ma Aryan ɗin dan Lion ya dakesa da laptop ɗinsu a kai ne yasa ya shiga wani irin yanayi tamkar ya suma, kun san duka a kai akwai wahalar iya jurewa, ban da haka da yana cikin hayyacinsa wlh ba zai hakura ba shi ma, zai ce sai dai a yarda shi ne mai gaskiya, to thank god ya shiga coma mood.

Yana gama haɗa alluran ya fito da gudun gaske, kai tsaye room ɗinsu ya koma, yana zuwa daidai door Lion ya ruguje kofar zai fito. Cikin zafin nama guru ya shammacesa ya dankara mashi wannan allurar a gefen wuya, da sauri Lion ya dafe wajen tare da juyo da kallonsa a kan guru, ɗayan hannunsa yasa ya damki wuyar guru, ya shakesa da karfi, yana ƙoƙarin yin magana amma ya gagara, take idanunsa suka fara rufewa a hankali, ya fara ganin abubuwa bibbiyu, kan kace me wata yana ta fara rufe mashi gani.

Jim kaɗan ya saki jikinsa gabaɗaya zai faɗi ƙasa tare da zame hannunsa daga wuyan guru. Jifa guru ya yi da kwankon alluran hannunsa, cikin zafin nama ya tare Lion ɗin, sannan ya zare alluran dake wuyan nasa ya jefar kafin ya gyara shi da kyau, ya ɗaukesa cak sai saman shoulder ɗinsa, ya fito da shi zuwa ɗayan ɗakin dake gefe ba wanda Aryan yake ciki ba, ɗakinsu da suke kwana su uku kam yau ma sun fashe komai kamar yadda in ta kwaɓe masu dama suke ruguje komai, sai sun huce ake sayan sabbin kaya, amma idan suka yi faɗa, oooooo kai kace abokan gaba ne ƴan duniya.

Room da Aryan yake a ciki guru ya koma dan ya duba ba dai ya samu matsala a kan nasa bane. Yana shigowa room ɗin daidai Aryan na dirowa kasan bed ɗin, da alama ya dawo normal. Fuskan nan tasa tamkar wanda aka bawa bakar labarin cewa wuta zai shiga, yana wani irin huci ya ce. "Ina Zayra'an?"....... Hannu guru ya harɗe a saman kirji kafin ya ce. "Aryan kada ace idan rai ya ɓaci sai hankali ya gushe mana! Ka sani cewa Zayra'an ba zai taɓa saurarenka ba, ba zai yarda da abin da zaka faɗa ba, kuma kai da kanka kasan kan batun case na Dr Lion ya fika gaskiya, mun san bata da ƴan uwa a nan, sannan ƴan uwanta na can a daji suke, ta ina ta samu kuɗi daga irin wannan shahararren account da sai manyan gangster's ko terrorists or manyan ƴan siyasa suke amfani da shi? Mun yi iya yinmu mun gagara bin diddigin mai wannan account ɗin, ka yi lissafi mana".

Hannu Aryan ya É—aga mashi. "Is enough, koma dai menene Seraphina bata cancanci ya mata hakan ba"..... Kallon tuhuma guru ya wurga mashi kafin ya ce. "Aryan anya kuwa? Meyasa ka damu da Seraphina haka?"....... "Because she's my daughter!". Cikin tsawa ya faÉ—a. Gyara tsayuwa guru yai yare da É—an karkata kansa, ya É—an É—aga mashi gera guda kafin ya ce. "After that kuma fa?".

Wani irin kallo Aryan ya wurga mashi kafin ya ce. "Get out of my room!!". Cikin fushi ya faÉ—a.

Kun san wani abu? A daidai wannan lokaci da suke ta faÉ—ar su kuma Abba da Ammie suna can zaune suna shirin zuwa gidan makota tambayawa su Aryan auren yaransu, da Aryan, da Faryan and Harleen, Abba ya ce sun girma dik aurar da su zai yi, dan haka ya ga wasu Æ´an mata uku a makwabta, É—aya ma Æ´ar siyasa ce, yana ganin tana da kyawawan halaye, zata dace da Aryan, kun san su waye yake magana a kai? Su Aunty Luna Aunty's É—in Noor, su Abba ya gani, ya yaba da hankalinsu, kun ga shi ba'a auren soyayya a gidansa, dan haka gobe zai je nemanwa su Aryan aure, dama so yake su tsayar da magana da Ammie gobe ya kira Aryan maza su zo su shirya su tafi aje a kaisu Æ´an'matan su gansu idan sun yi masu.

Bafa idan ƴan matan sun yi wa su Aryan ɗin ba, a'a, idan dai su Aryan ɗin sun yi wa ƴan matan, shi Abba ba ruwansa da su Aryan basa so ko yaran basu yi masu ba, shi dai yardan ƴan matan kawai yake so, to jama'a wacece zata ga Champion namu na amana ta ce bata ciki? Ai kowacce makale mashi zata yi, akwai dai dirama, wai kaman Champion ɗin namu ne za'a kai mace ta gani ta zaɓa, lallai su Aunty Lusi anyi kasuwa mai tsadar gaske. Watau idan na hango cakwakiyar dake gaba a cikin littafin nan har wani ɗan juya mun kaina yake yi.

Sanin cewa suna cikin fushi ne hasa guru ya juya ya fita, bai sake magana ba. Cikin fushi Aryan ya wuce toilet zuciyansa cike da tunanin Seraphina baiwar ALLAH kuma marainiyar ALLAH. Ni kam na ce daddy Aryan ko dai ko dai? Ka faÉ—i gaskiya fa!.

----------------------------🔥

WS-HOSPITAL.

Safiyar yau ta fara masu ne da yanayi na musamman, sun tashi cike da farincikin da basu san dalili ba saɓanin yadda suka yi barci jiya da takaicin sister Lazy. Shiryawa suka yi tsab cikin kayan aikinsu, suka fito zuwa wajen aiki, sun mance ma da batun sister Lazy na jiya, saboda su mutane ne da sam basa rike abu a ransu, da sun yi barci sun tashi zasu mance komai abinsu.

Daidai zasu shiga side É—insu watau side C sai ga su Dr James a jere su ukun kamar yadda suka saba tafiya. Jikinsu na rawa suka sussunkuya suka gaishesu, dik in da zasu wuce sai an sunkuya an kaishesu saboda su ne manyan kwararrun likitocin.

Ko kallon in da suke basu yi ba suka wuce suka shiga section D. Da kallon su sister Maya suka bisu har suka shige ciki, ajiyar zuciya sister Zinta ta sauke kafin ta ce. "Kwanaki biyun nan Dr James suna yawan zuwa section D, ko dai wani project suke yi ne? Kullum da safe sai sun shiga wajen, suna kuma É—aukar awanni kafin su fito".

Maya ce ta amsa da. "A tinaninki menene a section D and section E?".......... Shiru ta É—an yi kafin ta ce. "I think akwai babban aiki a wajen, dan kinga su uku ne suke shiga wajen, project ne babba a wajen, musamman section E É—in nan da yake killace a gefe guda, ga tsananin matakan tsaro har da kofofi masu amfani da lantarki a wajen, kai ina son sanin me a cikin wajen?".
Chapter 88 · 0% Book details