← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 227

Sashe 149

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da jin ya rungumeta ba karamar daɗi ta ji ba, ta ƙara shigewa jikinsa sosai. Shiru suka yi, shessheƙar kukan shagwaɓarta na tashi a hankali-hankali, yasa hannu yana ɗan shafa kanta izuwa kan bayanta. Gabaɗaya ya shige love mood, har ya manta cewa Campaion na IRON FIST yake!.

Sun É—auki 10 mins a haka, slowly ya saketa, ya raba jikinsu, saman sofa ya koma ya zauna, ya jingina kansa shiru tamkar mai tinanin wani abin, ya É—an lumshe idanunsa soyayyarta na kara ratsa shi sosai. Ganin haka yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da zuwa ta zauna a kusa da shi saman bed, tana kallon kyakkyawan face É—insa.

Ni kam na ce daddy fa ya yi mugun nisa a soyayyar Cherry bloom ɗin nan nasa, sai abin da muka gani, yanzu ita ke rike da ragamar zuciyansa, amma yarinta yasa ba zata gane cewa zata iya juya shi ba, ko Abba ba zai iya juya shi cikin sauƙi ba, amma ita zata iya a sauƙaƙe cikin kwanciyar hankali ma kuwa, amma ba zata gane hakan ba. To me kuke tinanin zai biyo baya? Ga su dai zaune shiru Cherry ta zuba mashi ido, idan ya wastsake ya dawo daga duniyar da ta jefasa me kuke tinani zai faru? Ƴar yarinya da ita tana son fin karfinmu, tasan komai, to thank God dai da bata fara aikata komai ɗin ba daddy ya farga!.

Tin da sun zauna shiru bari mu leƙa wani ɓangare, watakila kafin mu dawo shi ma daddy ya dawo daidai ya wastsake.

--------------------------

Zaune Abba yake a main parlo, yana rike da littafin The Franklin Scandal yana karantawa, hannunsa rike da gold scepter ɗinsa, ya miƙe kafafunsa saman lallausan throw pillow ɗin dake a gabansa, hankalinsa ya karkata kan littafin.

Cikin natsuwa Ammie ta sauƙo ƙasa, tana tafiya tana wuwwurga idanu in da zata gano Rimsha ya jikin Abba, dan tasan lokacin dawowarta daga school ya yi. A gefen Abba ta zauna tare da cewa. "Barka da hutawa ranka ya dade".

Abba gwani a izza da isa, kai tattijon nan akwai taƙama da nuna karfin iko game da fadanci, anya Abba ba jinin sarauta bane ba kuwa?....... Sai da ya ɗauki mintuna kafin ya rufe littafin hannunsa, a natse ya ce da Ammie. "Yauwa sannu da fitowa".

"Ban ga Rimsha ba". Ammie ta faɗa tana miƙa hannu ta karɓi sandar hannunsa, ta kwantar a ƙasa...... "Basu shigo ba ai".... Shiru Ammie ta ɗan yi, can kuma ta ce. "Nasan dik abin da ka yanke abu ne mai kyau, baka yanke abin da bai dace ba, kuma dik abin da ka yanke muna biyayya da kuma mubaya'a a garesa, amma a wannan karon ina neman alfarma dan ALLAH! ALLAH ya kara maka nisan kwana da lafiya".

Bai amsa ba, ya dai zuba mata idanu yana kallonta, tasan halinsa sarai, shirunsa ma magana ce, dan haka sai ta cigaba da cewa. "Dan ALLAH ka bar batun haɗa wannan aure na su Aryan da waɗan can yaran.....". Gagara karisawa ta yi saboda ɗan waro idanunsa a kanta da ya yi, mamaki ne ya kamasa jin yau karo na farko a gidansa ya yanke hukunci ake neman yi mashi katsalandan, abin da ba'a taɓa yi ba kenan.

"ALLAH ya baka hakuri, tuba nike". Ammie mace mai biyayya ta faÉ—a, sam ita bata son ai wa É—anta auren dolen nan ne, dan ya ce mata baya so, sun yi waya jiya, ya faÉ—a mata muddin Abba yai wannan aure to ta sani kome ya biyo baya su suka ja, shi ya gama magana, baya son auren kuma ba zai yi ba! Idan aka matsa mashi ran kowa ba zai yi daÉ—i bane.

Ammie tasan waye Aryan fiye da yadda Abba ya sanshi, tasan baya magana biyu, lallai dik wacce aka aura mashi sai ta gwammaci da bata zo duniya bama, dan billahil lazi mancewa da cewa ita macece zai yi, dama can maza suke yi wa kallon mata, aikuwa yarinya zata ji a jikinta ne!.

Nisawa Abba ya yi, zai yi magana kenan sai suka ji ana knocking na parlo door ɗinsu. Wayansa dake gefensa Abba ya ɗauko, app na door ɗin ya shiga, akwai camera a jikin kofar ta baya, so idan kuka shiga cikin app ɗin zaku iya shiga Camera ku ga wanene yake knocking kuna daga zaune!...... Uhm duniya ta cigaba, ALLAH ka wadatamu da ire-iren waɗan nan cigaban a ƙasarmu.

Yana dubawa ya ga Aunty Luna tsaye a bakin door. Ai da sauri ya danna door control, options suka bayyana, sannan ya danna open. Take dik wasu locks na kofar ta buɗe, ta ɗan motsa ta buɗe kaɗan. Turowa Aunty Luna ta yi ta shigo. Tana shirye cikin shiga ta alfarma, tana shirye cikin black jean, white top and winter jacket wanda ya zo mata har gwiwa a saman kayan, ta yi matuƙar kyau sosai, tana da natsuwa da hankali.

Gaban Abba ta kariso, har ƙasa da durkutsa ta gaida shi cikin girmamawa, sannan ta ɗagawa Ammie ma gaisuwa. Dik da cewa Abba baya dariya, kai face ɗinsa ba zaku taɓa zatan yasan me murmushi ba, amma har cikin ransa ya ji matuƙar daɗin ganin Aunty Luna, a mutunce ya amsa gaisuwarta tare da ce mata ta zauna, ya nuna mata ƙasa saman carpet, dan shi Abba akwai izzar balai, idan yana saman kujera ba'a zama a sama kai tsaye.

Zama ta yi. Shiru ne ya É—an biyo baya, sai kuma can ta ce. "Dama na zo ne in baka hakuri kan abin da ya faru, daddyna ma ya ce in baka hakuri, abin bai yi mana daÉ—i ba, bamu ji daÉ—in abin da grandpa ya yi ba"......... Still dai fuskan Abba babu fara'a ya amsa da. "Kada ki damu surukata, in kin je gida ki sanar da daddyn naki gobe da kaina ina kawo mashi sadaki".

Murmushi ne ya kubce mata, dan ita dai har ga ALLAH tana matuƙar son Harleen, tin da ta kyalla idanu ta ga haɗuwarsa, gabaɗaya ta rasa kanta, kai jinin Abba ba dai haɗuwa ba, ga iya ɗaukar wanka, kai Masha ALLAH kawai zamu ce.

Ta ɗan yi ƙasa da kai bata ce komai ba, ganin haka yasa Abba ya ce mata. "Ki je sama Harleen yana ɗakinsa, ku gaisa kafin ki koma ko?". Tamkar Abba yasan abin dake ranta, tana son ganinsa ne dama, amma ta rasa yadda zata faɗawa Abba, bata san meyasa dik rashin kunya irin nasu na European amma take matukar shakkar Abba, yai mata mugun kwarjini, ganin cikin idanunsa wannan ta gagara yi, to haka Aryan yake, wlh ba kowa yake iya ganin cikin idanunsa ba, bare Lion da Vir, kai IRIN FIST dikka zaku zaci jinin Abba ne su ɗin, akwai su da balain kwarjini, cika ido, sanyawa mutum zarra, izza, isa da taƙama, yadda kuka ga Abba da karfin halin aurar da yara ko ubansu bai so ba, haka IRON FIST suke da shegen nuna iko a koma inane!.

Miƙewa ta yi, ba kunya ta dinga zubawa Abba godiya, sai ta nufi sama. Ammie kam ta saki ido tana kallonsu, watau Ammie bata waye sosai bane, da sauran hijabin kunyarta in faɗa maku, amma Abba, ba dan wani abin ba, ba dan ina tsoron daddy Champion ba, da na ce Abba taƙadarin ɗan duniya ne! Amma ina tsoron Aryan, na yi shiru!.

Har ta haye sai kuma ta tsaya game da juyowa, bata iya kallon face É—in Abba kai tsaye ba, tana facing Ammie ta ce. "Daddy ina ne room É—insa?"...... Abba dake kallonta ne ya amsa da. "Abba zaki kirani, room É—insa na side two daga parlon sama"...... Da okey ta amsa game da cewa thank you Abba tana murmusawan dake kara fito da kyanta.

Ta juya ta karisa cikin second parlo. Kai tsaye ta nufi room É—insa. Yana kwance saman bed, daga shi sai shorts and singlet, hannunsa rike da waya yana dannawa, ya rungumo pillow a kirji, while ya É—aura kafafunsa a kan wasu pillows É—in, da alama yana jin daÉ—in yanayin da yake a ciki.

A natse ta turo kofar ta shigo, sarai ya ji an turo kofa, amma ya zaci Faryan ne sai bai É—ago kai ba, dan yasan kofar É—akinsu ai sai su kaÉ—ai zasu iya buÉ—ewa, dan haka bai zaci wata ce daga waje ba. Ita kuwa Abba ne ya buÉ—e mata kofar daga in da yake zaune a parlo, tin kan ta karisa ya danna open na side two doors, tana zuwa ta ga kofar a É—an ture.

Karisowa ciki ta yi, ko kaɗan bai ɗaga ido ba, abin da ya kara burgeta da shi kenan, wannan miskilanci da izzar tasu! Ga ɗan banzan girman kai wai sun fi karfin cewa sorry, zaku shiga hannun nisau ne dan ubanku Abba Khaiza'an, mu zaku gwadawa iskanci? Yanzu lokacinku ne, ku gama shan kamshinku zamu damƙeku ne, Aunty Luna kada ki kyale ɗan air, ki gyara mashi zama, ki ganar da shi mu fa nisa'u ba'a mana wannan shirmen!.

Har ta iso gaban bed ɗin bai ɗago kai ba, sai da ta zauna a dab da shi, tasa hannu cike da yanga irin namu na mata, ga natsuwa ta karɓi wayan hannun nasa ne ya wani irin ɗawo dara-daran eyes ɗinsa a slow motion. Ai yana sauke idanu kan face ɗin mace bai san time da ya zarosu waje sosai ba, sai ya ɗan miƙe daga kishingiɗar da ya yi, ya zauna da kyau yana kallonta babu ko kyaftawa.

HaÉ—aÉ—É—en murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Good afternoon oga sir".......... Shiru bai amsa ba, sai ma juya idanu da ya yi, ya kalli door É—in shigowa, kafin a natse ya dawo da kallonsa a kanta. ÆŠan É—aure fuska ya yi, a dake ya ce. "What brought you here?"..

Nisawa ta É—an yi kafin in a cool way sosai ta ce. "Coming to see your beautiful face, tin ranar baka sake dawowa ba, ka barni da tinaninka a cikin rai, shin ban maka bane? Baka son haÉ—in Abbanmu ne? Ko akwai abin da baka so a tattare dani ne?". Ta faÉ—a tana É—an jujjuya wayansa dake hannunta.
Chapter 149 · 0% Book details