← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 227

Sashe 158

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"My gentle chaos yau ka kwana a nan kawai". A shagwaɓe ta faɗa. Raba jikinsu ya yi, ya sauƙa ya koma saman sofa, wayarsa dake ƙara ya fitar yana faɗin. "Jeki kawo lunch in ciyar dake"........ Da okey ta amsa tana sauƙowa ƙasa ita ma.

Picking call ɗin ya yi tare da sanya mata yatsa ɗaya a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru, kai ta jinjina, a natse ya ce. "Hello"....... Daga ɗayan ɓangaren Lion ya amsa da. "Ina kake?"...... "Ina zuwa". Ya faɗa a takaice. Guru ne ya karɓi wayar daga hannun Lion, fitowa balcony ya yi, dan dama suna ɗakin Lion ɗin, cikin zolaya ya ce. "Na baka 1 min ka dawo ko in tona maka asiri, kuma a matsayina na uban yarinyar nan ko I love you ban yarda ka ce ba".

"Kai gauro yakamata ka nemo mata in maka aure, dan ka san me duniya take ciki, naga ka zaƙe dayawa kana son shiga tsakanin mata da mijinta". Aryan ya faɗa yana miƙewa tsaye, daidai lokacin Seraphina ta dawo hannunta rike da plate na jolof rice, a gabansa ta tsaya, cikin shagwaɓa ta ce. "My gentle chaos yau nima zan yi feeding ɗinka a baki". Ta faɗa tana ajiye plate ɗin a ƙasa, ta riko hannunsa ɗaya.

Dik abin da ta faɗa guru ya jita, sai ya ji abin ya burgesa, dan shagwaɓarta da yadda ta ce zata baiwa Aryan abinci a baki sai ya ji bayan soyayyar ƴan uwansa su Lion lallai yana buƙatar irin wannan soyayyar ma, wannan na daban ne. Muryan Aryan ne ta katse mashi tinani da cewa. "Ka samu mata in maka aure, wannan shi ne soyayyar mace, daban yake da kowanne, ba zaka gane hakan ba har sai ka ɗanɗa". Ya faɗa mashi hakan ne dan yasan confirm ya ji me Seraphina ta ce.

A shagwaɓe ta sake cewa. "My gentle chaos ɗan uwanka ne? Dama kana da ƴan uwa?"....... Kai ya jinjina mata alamar e, sai ya ɗan riko waist ɗinta ta baya, ya jawota jikinsa tare da kara mata wayar a kunne yana faɗin. "Ki gaishesa".......... Ɗan gyara murya ta yi game da cewa. "Ɗan uwan daddy good afternoon".

"Afternoon Seraphina, how's your day?"....... "Fine what of you?"....... "Cool". Ya amsa da shi kafin ya sake cewa. "I'm your dad also, ki ce mun daddy not É—an uwan daddy"...... Murmushi ta fara yi kafin ta ce. "To daddy yaushe kai kuma zaka zo in ganka?"...... Lokaci guda ya tina time da take gidan nasu zakinsu ya biyota ta shigo room É—insu, dai gata ta sume.

"Soon". Ya amsa mata..... Zata yi magana Aryan ya karɓe wayansa, dan in ya biyewa Seraphina ba zai tafi ba. "Scorpion ina zuwa yanzu". Ya faɗa tare da katse kiran, ya ɗan sassauta riƙon da yai mata kafin ya ce. "Zauna ki yi lunch, zan dawo anjuma da daddare"...... Tana turo baki ta amsa da ka dawo da wuri.

Sumbatar forehead ɗinta ya yi game da ce mata bye-bye, ya saketa ya nufi waje. Da kallo ta bisa har ya fice, zama ta yi a ƙasa saman carpet ɗin tare da jawo plate na abincin nata, a fili ta ce. "Daddy kenan, nasan kaima kana son sex sai ka ce mun ba haka ba, wai zaka gwada mun kai ba ruwan kan nan, nasan maganinka ne ai"..….......🤯

Ta faÉ—a tare da fara cin abincinta, ta É—auki wayarta ta kira Rimsha, nan ta fara bata labarin yadda suka yi da daddy, ke Rimsha da iya yi har da cewa. "Gaskiya daddyn nan naki anyi É—an duniya, watau ke zai rainawa wayau ko?"...... Tana kai abinci bakinta ta ce. "Bai san kar nike kallonsa ba, ki kyalesa ne zan yi maganinsa ai".

Dariya Rimsha ta yi kafin ta ce. "Ki goge mashi hadda".….... Dariya ita ma ta yi kafin ta ce. "Ke ai har yau ba ƙinƙi amfani da shawarar da na baki ba?"........... Tana kwance kan gadon Faryan ta ce. "Wani shawara kenan?".

Nisawa Seraphina ta ɗan yi kafin ta ce. "Da na ce ki bugawa uncle Aryan ɗin nan naki wood a kai, ba ya ce shi mugu bane, ki daina jin tsaronsa na ce maki"..... Zazzaro idanu ta yi, a zabure ta miƙe zaune. "Seraphina baki da hankali, yanzu uncle ɗin zan bugawa wood? Kina son ki daina ganina a duniya kenan ko? Kin gaji da ganina! Uncle Aryan fa? Mutumin da duk family ɗinmu tsoronsa suke ji ɗin? Ke baki son a zauna lafiya na lura, ai da hanya ta haɗani da uncle Aryan gara na bi ta saman wuta in wuce, ke na lura kin fara zama muguwa, yanzu kin daina sona".

Wani irin dariya Seraphina ta fara yi har da riƙe ciki, ta dinga cewa Rimsha matsoraciya malalaciya, Rimsha ta ce e ta yarda su je a hakan in dai a kan shiga harkar uncle Aryan ne ta kirata da koma menene idan tana so. Suna tsaka da wayar katin Seraphina ya ƙare, turo baki ta yi game da ajiye wayar.

Tana ajiyewa sai ga kiran Rimsha ya biyo baya, cike da murna ta É—auka suka cigaba da hira har ta kammala cin abinci, ta tashi ta shiga wanka rike da wayar a hannunta bata katse kiran ba.

----------------------🔥

WS-HOSPITAL.

Suna shiga cikin hospital ɗin kai tsaye suka nufi SECTION D. Sai da suka je suka duba lafiyar babys ɗin nan, sannan suka nufi in da darling yake, nan ma suka duba shi, izuwa yanzu ko motsi darling baya yi, sai idanunsa ne kawai ke motsawa, jikinsa ya yi wani irin fari sosai tamkar dattin haihuwa, fuskansa da hannayensa zuwa kafafunsa sun kumbura sosai wanda hakan yasa ya zama ƙato tamkar jariri ɗan wata 7, alhalin satinsa 4 yanzu a duniya.

Ganin aikinsu a wajen yana tafiya daidai ne yasa suka fita izuwa É—akin tiyata. To ALLAH ya sake dawo damu wannan rana ta tiyata a cire eggs. Wanna É—akin ma mun bashi sunan ÆŠAKIN CIRE EGGS

Ƴan matan gabaɗaya suna kwakkwance a saman gadajen jinyarsu, kamar ranar dik suna barci, dan sun sha alluran barci, babu sabbin fuska a cikin mata, dik na da ɗin ne....... Dik da yaran nan a kwance suke, da kunga jikinsu zaku ga alamar rauni, alluran da ake danƙara masu ya fara kashe dik wasu garkuwa na jikinsu, skin ɗinsu ya canzawa, sun yi wani irin haske sosai, kuma abin takaici dikkansu babu wacce ta haura 20 years, ga su kyawawan gaske, amma a haka su Dr James suke son salwantar da rayuwar yaran nan, sun zo duniya ta hanyar kyankyasa, basu da uwa bare uba, sannan zasu bar duniya ta hanyar cire eggs ɗinsu, dan waɗan nan shegun alluran da ake masu ba karamin ɓarna yake masu a jiki ba, an mayar da rayuwarsu tamkar ATM na ciran kuɗi, dik lokacin da ka ga dama zaka je ka cire kuɗi a bank ɗinka, to suma haka 3D ke masu, dik lokacin da suka ga dama zasu ciro eggs ɗinsu. Ya rabb.

Nurses dake wannan asibitin sun shirya komai yadda ake buƙata, a gaban wani bed Dr James ya tsaya, wata na'ura ya ɗauko, ya ɗaura a kan cikin yarinyar dake kwance bayan ya ɗage rigar dake jikinta sama. Yarinyar ma fuskanta a kumbure kamar bata da lafiya haka.

Idanunsa a kan computer dake jikin gadon, ya zuba yana kallon yadda cikin nata yake motsawa, a daidai mararta ya tsayar da na'urar, ya zubawa ovaries ɗinta idanu, can kuma ya ɗan yi ƙasa da na'urar izuwa saitin follicle ɗinta. Ya ɗan yi mamakin ganin ruwan cikin follicle ɗin bashi da yawa.

Ɗago eyes ɗinsa a kan fuskarta ya yi, shiru ya ɗan zuba mata idanu na ƴan sakanni, sai kuma ya kai hannunsa ɗayan ya taɓa tsakiyar wuyarta daidai in da maƙogwaronta yake, kun san jijiyoyin wajen suna harbawa ai, suna amsawa daga bugun da zuciya take yi.

Yatsunsa biyu ya ɗaura a kan maƙogwaron nata, ya kasa kunne sosai yana son ya ji yanayin harbawar ƙananan jijiyoyin dake wajen. After like 30 seconds ya ɗauke hannunsa daga wajen ya mayar saman forehead ɗinta, ya sanya yatsansa ya janye fatar idanunta sama, ya gwalo kwayar idanun nata waje.

Can ya saki idanun tare da dawo da hannunsa saman kirjinsa, ya zame rigar ya É—aura yatsunsa biyu a saitin zuciyarta. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Da gaske yarinyar babu ita, babu rai a jikinta, komai na jikinta ya tsaya cak ya daina aiki, da alama daga alluran barci ta zarce lahira, rai ya yi halinsa.

Fahimtar da ya yi cewa ta mutu da gaske ne yasa ya ɗan nisa tare da ɗauko siririn bututun da suke tiyatar, ya ɗauko audiga tare da wani oil a cikin roba, zuba oil ɗin yai a jikin audigan, ya goggoga mata a gabanta, ya cusa har can ciki kafin ya sake fitarwa, ta rigada ta mutu, komai na jikinta ba zai motsa ba, bai isa ya cusa mata wannan karfe a gabanta ba, saboda jikinta ya daina sakin ruwa, shiyasa ya saka mata wannan mai ɗin dan ya samu hanyar wucewa ciki. Ya rabb, ta mutum ma ba zai hakura ba, dan suna bala'in buƙatar alot of eggs sosai, so ba zai iya yafe mata ba, kai wannan wace iriyar musifa ce?

Bayan ya gama shafe gabanta da mai har can ciki ne ya ɗauko bututun ƙarfen tiyatar tare da gyara na'urar dake kan cikinta, ya ƙara yin ƙasa da shi zuwa ta gabanta, dan yasan zai sha wahalar shigarta tin da babu ruwa a jikinta ta rigada ta mutu, so dole ya duba hanya da kyau kada ya fasa jikinta ya shiga wani waje.
Chapter 158 · 0% Book details