← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 227

Sashe 200

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har zata juya kuma sai ta fahimci ashe macece kuma sister Maya ce. Ajiyar zuciya ta sauke game da karisawa wajen da sister Maya ke kwance, tattaɓata ta fara yi tana ambatar sunanta. A hankali Maya ta buɗe idanunta, ganin Zinta ce yasa ta miƙe zaune tana faɗin. "Sister lafiya?".

Zinta ta amsa da. "Sis babu kowa fa a gidan nan yanzu, ina suke to?"..... "Ban gane babu kowa a gidan nan ba?". Ta faɗa tana zare idanu. Shaida mata da kyau sister Zinta ta yi lallai babu kowa a gidan nan, zabura ta yi ta sauƙo ƙasan gadon tana tambayar ina suka je?.

Sister Zinta ta ce. "Ke, ki natsu, ina ganin wani abin suka je yi, ko sun je cikin hospital ne? Mu je mu dubasu"..... Na'am da wannan zance Maya ta yi, sai ta haɗe natsuwarta waje guda, ta miƙe suka fice a tare.

A bakin gate suka isko guards masu gadin gidan suna zazzaune babu alamar barci a idanunsu, zasu fita guards É—in É—aya ya ce. "Ina zaku je Madam?"....... "Cikin hospital". Sister Zinta ta basu amsa.

"Sorry Madam ba'a ce mana zaku fita ba, dan haka ku koma"...... Kallon juna suka yi, sister Maya ta juya da nufin su koma, ita kuma sister Zinta da yanzu ta daina jin tsoro da shakkar kowa tin da ta amarce da Dr James sai cewa ta yi. "To idan na zo fita ka hanani in gani". Ta faÉ—a tana riko hannun sister Maya.

Miƙewa tsaye guard ɗin ya yi game da cewa. "Sorry Madam, ba'a bamu izinin cewa akwai wacce zata fita mu buɗe mata kofa ba". ..... Sosai sister Zinta ta tsorata da ya miƙe tsaye, wani kato da shi a murɗe. Amma saboda yanzu bata jin magana sam-sam, bata shakkar kowa bare tsoro sai ta ce. "Wannan kai ya shafa, ni dai hanya zaku bani in wuce ko kuma in buɗe da kaina in wuce".

Rikota sister Maya ta yi tana faÉ—in. "Sis please ki kyalesu mu koma ciki"..... "Ba zan kyalesu ba sis, sai na je na duba mijina, kika sani ne ko yana tare da sister Lazy!". Cikin masifa ta faÉ—a, yanzu ta fara iya harda masifa yarinyar nan, da shiru-shiru abinta.

Mamaki ne ya kama Maya ganin yadda take masifar, har da É—aure fuska tamau. Shi kuwa wannan bodyguard É—in ya tsaya tsayin daka kan ba zata wuce ba, domin kuwa a bakin aikinsa yake. Da ta matsa mashi ma sai ya yi mata É—aukar amarya, cak ya dagata, bai direta a ko'ina ba sai a tsakiyar parlonsu, ya juya ya fito.

Zata bi bayansa sister Maya da ta shigo yanzu ta riketa tana faÉ—in ta yi hakuri koma menene ai Dr James É—in zai dawo, ba sai ta titseye shi ba idan ya dawo, kin aminta ta yi, ta kwace kanta zata sake fita Maya ta riketa tana sake bata hakuri. Shi kuwa bodyguard tini ya koma bakin aikinsa.

A daidai wannan lokaci kuma 3D suna tsakiyar hospital ɗin, dan SECTION E a tsakiyar gabaɗaya ginin yake, amma ba zaka taɓa zaton shi ne a tsakiya ba har sai in ka san taswirar ginin da kyau, a yadda aka tsara haka ne, amma jama'ar cikin asibitin suna ganin kamar SECTION E a karshe yake.

Da ace sister Zinta ta fito a wannan lokaci, to hakika da zata haÉ—u da 3D rike da jariran da suka É—auko daga SECTION D, saboda sun fito zasu shiga SECTION E, a daidai saitin hanyar da zai kaisu gidansu suka tsaya Dr James yana duba wani baby da hancinsa ke bleeding, sun É—auko five babys kamar yadda suka saba, suna tsaka da tafiya ne Dr James ya ji jini na zuba a hannunsa, shi ne suka tsaya duba menene matsalar, to daidai wannan lokaci su sister Zinta suka so fitowa guard É—in can ya taresu.

Sosai hancin jaririn yake zubar da jini, wannan jaririn ne da sister Maya take É—auka a lokacin da aka É—auke mata darling, sai ta maye gurbin darling da shi, to shi suka É—auka dama. Ganin kamar akwai matsala ne yasa Dr James ya ce su Dr Kamal su yi gaba yana zuwa, bari ya duba babyn, in bashi da lafiya ne sai ya ajiyesa ya É—auki wani, da safe zasu duba lafiyansa.

SECTION D ya dawo da babyn, su kuma suka wuce SECTION E da sauran na hannayensu dake ta faman barci. A saman gadon yaron ya kwantar da shi yana duba lafiyan jikinsa. Jikin yaron ya yi zafi sosai alamar bashi da lafiya, tin da yaga haka sai ya kyalesa, dan na faɗa maku basa amfani da jini mai rauni, idan jariri bashi da lafiya komai na jikinsa yana raunata, so jikinsa ba zai baiwa jininsa wannan sinadarin da suke da buƙata ba, ko sun razana shi sinadarin da suke so ba zai fita ba, sun yi asarar kashesa a banza kenan.

Matsawa gaba Dr James ya yi, a gadon wani jariri ya tsaya, yaron idanunsa biyu yana wasa da Æ´an kafafu da hannayensa, ya ALLAH, wlh ALLAH ya yi halitta a kan wannan yaro, da shi dana kusa da gadonsa, kamanninsu É—aya sak, ya rabb, kyawawan gaske ne sosai, jajir da su, É—ayan babyn yana harci, while É—ayan idanunsa biyu.

Yaron nan ya haÉ—u jama'a, idanunsa dara-dara farare kal a waje, kwayar idanunsa sky blue irin mai hasken nan, da yake dare ne ga idanun nasa a buÉ—e har wani kyalli yake yi, lips É—insa dark purple tamkar an sanya purple lipstick, yana ta zaro idanu waje yana wasa abinsa, tamkar a baka shi ka je ka ajiye ka yi ta kallo.

Hannu Dr James ya sanya ya É—auki babyn, ya kalli fuskansa da kyau kafin ya juya ya kalli fuskan babyn dake gadon kusa da wannan, tamkar an tsaga kara a kamanni, dik yadda aka yi da sperm na mutum É—aya aka kyankyashi yaran, kuma yaran alama ya nuna sperm na ainahin European ne, dan turawa ne yaran, gashin kansu golden brown mai shegen kyau haka.

Saɓa shi a saman shoulder Dr James ya yi, dama ɗaya zai ɗauka, su Dr Kamal sun tafi da huɗu. Bayansu ya bi yana ɗan jijjiga baby, dan yana ji an ɗaukesa ya fara ƙoƙarin kuka, da alama yunwa yake ji.

A SECTION E ya isko su Dr Kamal suna tsaye da babys a hannu suna jiransa, yana zuwa suka kwantar da yaran a wannan gado na lantarkin. Suka kunna masu shocking ɗin. Take suka fara wani irin jijjiga, ya rabb, wannan baby ya zaro blue eyes ɗinsa waje tamkar kwayar zasu faɗi ƙasa, ya jisa a wani irin duniyar da bai taɓa ji ba, ya gagara gane menene ma a wajen.

Ko gezau 3D basu yi ba, suna tsaye har sai da jikin yaran ya saki waÉ—an nan sinadaran, sannan ne Dr James ya matsa ya kashe shocking É—in. Ai yana kashewa wannan baby mai blue eyes É—in ya fashe da wani irin kuka har muryarsa tana wani irin garrrr-garrrr-garrr saboda tashin hankalin da gangar jikinsa ya shiga.

Babu tausayu babu imani Dr James ya jefasu cikin ɗayar injin, yana jin yaron nan yana ihu, ko kyan yaron nan bai duba ya ce ya mashi kyau bari ya barshi ba, haka ya dannasu cikin wannan ball ɗin, suka mayar da marfi suka rufe. Suna rufewa kuka ɗaya mai ƙara yaron ya yi daga nan bai sake ba, injuna sun murɗe mashi wuya. Allahumma ajirni fi musibatin.

Shiru 3D suka tsaya har lokacin tarar jini da ɓargo game da garin ƙashi da tsoƙa ya yi, suka ɗauki bokitansu suka zo suka tari komai kamar yadda suka saba, sannan suka wuce izuwa freezers room dan adana jinin......... Nasan jama'a kun ƙosa ku ji me suke yi da ɓargo da garin ƙashin babys ɗin ko? Tin da kun ji me suke yi da jini kam. Ni kaina na ƙosa in sanar daku amma a aikace ba'a labarce ba, na ƙosa ku sani dan irin abubuwan da dayawanku kuke amfani da shi ne, amma mu je zuwa, lokaci zai kaimu da ku ji komai!.

Bayan sun adana su ɓargon yadda yakamata sai suka nufi SECTION D dan duba dashen da suka yi na eggs and sperms ɗin nan. Kewaye suka fara yi a cikin wajen suna dubawa, komai na tafiya yadda suke so. Sai dai abu ɗaya da basu yi tsammani ba, eggs da suka cire a jikin matattun yaran can sun fi kowani eggs a wajen karfi da kwari, sun fita daban da saura, da alama sun fi lafiya.

A cewar Dr James jariran zasu fi kwari da lafiya, da alama zasu samu maƙudan kuɗaɗɗe da su. Fitowa suka yi bayan sun tabbatar da komai lafiya, suka nufi gidansu bayan sun je office ɗinsu sun cire kayan aikata ɓarnar nasu kenan, suka mayar da kayansu.

Suna hanyar komawa gida ne Dr Kamal ya ce. "WaÉ—an nan eggs É—in suna da karfi sosai"...... Dr James ya ce. "Sosai, nima na lura da hakan"....... Dr Mark ya amsa da. "Ina ganin mu sayar da babys É—in kawai kada mu yi drugs dasu".

Shiru Dr James ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Dama waɗan nan yadda suke da karfin nan manya ƙasashe zamu sayarwa, dama akwai ƙasar da ta nemi jarirai masu karfi a hannuna dan ta renesu ta mayar da su sojojinta, sai dai su jarirai dubu uku suke so"..... Dr Kamal ya ce. "Suna shirya yaki ta karkashin ƙasa kenan?".

Dr Mark ya amsa da. "Zaka gane masu ne? Ai kasan haka suke, sai su reni jarirai a yadda suke son su kasance, su jefasu hukumar soja dan kawai kasashen duniya su razana da karfin sojansu, kaga yanzu akwai ƙasashen da idan aka ambaci sunansu to sai ka ji ana faɗin sojojinsu tamkar ba mutane ba, basu tsoron mutuwa, yaki kawai suka sani".
Chapter 200 · 0% Book details