← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 214 OF 227

Sashe 214

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowa cikin room ɗin V ta yi, tana ɗan ɗingisa kafa, ba jimawa ta farka daga barci ta yi wanka, tana sanye da kaya marasa nauyi. Kallo suka bita da shi, suna shirin yin magana sai gani suka yi ta ɗauki wayanta ta nufi waje, bayanta suka bi da kallo. Kusan a tare suka miƙe Manassa rike da cup na drink ɗin suka biyo bayan V dan su ji meyasameta, sun ga idanunta sun yi jajir sun kumbura tamkar ta sha kuka, ga shi tana ɗingisa kafa, abinku da shagwaɓɓaɓiya sai shagwaɓe fuska take yi.

A bakin tantinsu suka isko V tsaye tana ƙoƙarin kara waya a kunne, Arya rike da hannun Jehan, Manassa ta zauna a wannan dutse dake bakin tantin nasu tana kora drink ɗinta, Angelina ta tsaya gefen Manassa ɗin, suka tsaya jiran ta kammala waya.

A natse murya can ƙasa ta ce. "Hello friend". Ta faɗa tana ɗan matsawa daga kusa da su Angelina, taga miss call ɗinsa sama da 20 ne daga daren jiya zuwa yau, shi ne ta ce bari ta kira ta ji menene, wannan causin ɗin nata ne.

Daga can ɓangaren ya ce. "Ina kika shiga ne beb, tin jiya ban jiki ba, dik na damu, na yi kawarki sosai, na yi kewar daddaɗar muryar nan taki"........ "Sorry friend, nima ai na yi kewarka kuma na yi kewar daddaɗar muryanka ɗin, aiki ne ya sha kaina, ya su Aunty Bee?".

"Suna lafiya to ya aiki?"....... Ɗan juyawa ta yi zata amsa da lafiya idanunta suka sauƙa a kan Noor dake tsaye ta bayan tantinsu, ya yi folding hands ɗinsa a kirji, kallonta kawai yake yi, fuskanta a tamke tamau, dik ya canza. Ya shiga cikin tantinsa ne yaga bata ciki, to sanin bata jin daɗi yasa ya ce bari ya dubota, sai ya bi ta bayan tantin nasa zai shigo nasu kenan ya ji tana cewa ta ki kewar daddaɗardl muryan friend, shi ne ya tsaya a wajen.

Ai jikinta take ya hau rawa, ta wani irin mugun shan jinin jikinta, da sauri ta zare wayar daga kunnenta, tana ƙoƙarin yi mashi magana ya matso cikin zafa ya kwace wayar, wancan karon ma da ya raga mata dan bai san me mata yake nufi gabaɗaya ba, aikuwa yanzu ya sani, dan haka bai ga dalilin da zai sa wani ya nemi shiga harkarsa ba, yanzu auren sunnah ma suka yi bana zobe ba, kuma ya je duniyar sama jiya ai sai shiru.

Jikinta na rawa ta sake mashi wayar tana kallonsa. Bin kan screen ɗinta da kallo ya yi, sai ya kara wayan a kunnensa, a daidai lokacin Friend yake ce mata. "Da gaske voice ɗina na maki daɗi beb?"........ Wani irin tsananin takaici ne ya turnuƙe zuciyansa, a fusace ya ce. "Who the hell are you?!".

Zuba mashi idanu su Manassa suka yi, zallar kishi ne malam a kan fuskansa, har idanunsa sun ƙaɗa sun yi jajir. Kit Friend ya katse kiran, dan a tinaninsa oganta ne a wajen aiki. Bin kiran Noor ya yi, amma ba'a ɗauka ba, cikin zafa ya ɗago da kallonsa a kanta.

Hannu É—aya ya zura cikin aljihun combat trouser dake jikinsa, ji ya yi tactical tshirts dake jikinsa ma zafi take haÉ—a mashi tsabar ya fusata, abin takaicin yai mata warning a farko ranar, amma yau ta sake yi.

Cike da zafin kishi ya ce. "His voice is so sweet, and you missed him so much, who's he?!". In a harsh way ya faɗa, hakan ya ja hankalin sauran sojojinsu dake sansanin, amma dik sai suka yi ƙasa da kai tin da ogansu ne a wajen.

Gagara bashi amsa V ta yi, idanunta suka ciko da kwallah, hannunta sai kerma suke yi........ "Okey you love his voice, you missed him? You love him right? You want to marry him?". Cikin zafin kishi ya faÉ—i maganar, bai ma san me yake faÉ—e sosai ba.

"Please stop it, stop saying that, It's not what you're thing......". Tamkar zata sanya kuka ta yi maganar..... Wani irin mugun kallon da ya dallah mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar. Cikin fushi yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta ya maka wayar tata da ƙasa, take ta tarwatse raga-raga. Hannu bibbiyu ta sanya ta toshe bakinta jikinta na tsananta kerma, hawayen da take ƙoƙarin rikewa ne ya fara zuba tamkar an buɗe tap, da kyar ta iya ɗagowa ta kalli rikitatcen face ɗinsa da gabaɗaya ya canza, har ja fuskar tasa ta yi tsabar fushi. Sai ma in ya tina ta ce i missed you and i missed your sweet voice, ya rabb, sai ya ji tamkar zai haɗiye zuciya.

Muryarta na rawa ta fara ƙoƙarin sake yi mashi magana ko zata dace. Cikin zafa ya ɗaga mata hannu game da cewa. "Don't say anything here!!". Ya faɗa yana pointining ɗinta da hannunsa. Ba shiri ta haɗiye abin da take son faɗe, jikinta ya tsananta kerma sosai wanda yasa ta gagara iya rike kanta dama ba lafiya ba, sai kawai ta durkushe ƙasa a wajen, wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi.

Da gudu Angelina ta kariso in da take, durkushewa ta yi ta rungumi V a jikinta tana satar kallon Noor dake ta uban huci tamkar zai kama da wuta. Gabaɗaya takaicinsu ya gama cika Arya, ji take tamkar ta shake V da ta zubar masu da mutunci take baiwa namiji hakuri a kan laifin da bata aikata ba, yaushe ta ce tana son friend?. Ita dai Manassa abin da kowa ya sani ne, watau komai normal, bata wani damu ba, dan faɗa tsakanin V da Noor ai ba sabon abu bane, zama su shirya ne babu wanda ya sani, ranar da suka yi wancan uban faɗa waye ya taɓa zatan zasu shirya? Ba sai ga shi ko kwana ɗaya ba'ayi ba har sun shirya! Dan haka su rataye kansu idan sun ga dama ita babu ruwanta.

Noor ne ya cika baƙin kishi, ga ɗan banzan saurin fushi, ya koyi saurin fusatar Leo, in ban da haka yanzu me abin fasa mata waya daga jin tana magana da wani? Ko damar yin magana yaki bata, shi sarkin zuciya.

Siririn tsaki Arya ta ja tare da juyawa da sauri ta bar wajen, dan zata iya kai duka idan ta cigaba da tsayawa. Manassa dai hannu ta miƙa ta ɗauko drink ɗinta dake ƙasa ta cigaba da sipping, dan ita faɗar ma sugar yake mata, ai in basa faɗar basu cika masoya ba. Juyawa Noor ya yi cikin fushi zai bar wajen. Da sauri muryarta na rawa ta ce. "Please, my heartbeat, just listen to me, give me one chance to tell you who I truly am, don't be upset with me for a mistake I never made, let me hold your trust close to my heart".

Ai ko kallon in da take bai sake yi ba, da sauri ya wuce gudun kada ya kai mata duka, dan wlh ya rike kansa ne, ba dan haka ba time ɗin da take cewa friend voice ɗinka da daɗi da sai dai ta ji hakwaranta a ƙasa ya zubar mata saboda balain kishi. Ita ma bata ji, gata mai aboki, ai taga aboki yau kam.

Wucewa ya yi ya barta a wajen, ta rungume Angelina tana wani irin kuka mai ban tausayi, dama ga ciwon da ya ji mata. Shi kuwa cikin tantinsa ya koma, ya zauna a gefen mattress yana huci. After like 5 mins ya miƙe cikin zafa ya fito. Suna nan in da ya barsu, Arya da Jehan ne kawai suka koma ciki.

Su ya nufo gadan-gadan, yana zuwa ya É—auki V cak sai saman buÉ—aÉ—É—iyar kirjinsa, cikin zafin jini ya wuce cikin tantinsa da ita, ba zai iya barinta tana kukan nan ba dan yasan bata da lafiya, kada wani ciwon kuma ya kamata.

A saman mattress ya kwantar da ita, a tsawace ya ce. "Ki mun shiru, idan na sake jin koda tarinki ne sai kin gane kuranki". Babu wasa a tattare da shi ya faɗa. Hannu tasa ta toshe bakinta game da haɗiye kukan nata, tana kallonsa cikin ido, ya dallar mata harara kafin ya miƙe ya fice ya barta kwance, sai shessheƙar kuka take yi.

Lamarin Noor da V sai su wlh, ga balain kaunar juna ga zafin kishi, ga kuma faÉ—a, kai suna bani ciwon kai.

After some hours.

Bayan sun yi sallar mangrib da ishai, sojojin dake sansanin suna hakin wuta, har team one suna tare a bakin wuta except Leo dake cikin ɗakinsa, V tana ɗakin Noor kwance zazzaɓi ya rufeta saboda kukan da ta sha ga ciwon da angon nata ya bata jiya, sai zazzaɓi ya rufeta, har yanzu kuma Noor yana kan dokin zuciya, yaki sauraranta, da ya kawo mata abincin dare ma tana son yi mashi magana ta faɗa mashi tana jin zazzaɓi sai ya dakatar da ita, ya wuce ya fita ba tare da ya ji me take son ce mashi ba.

Su Angelina suna tare da Arya a cikin É—aki suna hira, shiryawa Arya ta yi cikin normal kayan gida kamar yadda Leo yai mata message, wandon jeans baki da top ash, ta É—auki karamin pistol da ake basu dan kare kai, sannan ta É—auki laptop É—inta cikin rucksack É—inta, bata yi wa su Angelina magana ba ta wuce ta fita.

Da sauri Jehan ta taso tana nuna mata alamar zata bita. Riko hannunta ta yi, ta miƙawa Angelina ita tare da cewa. "Zan je wajen sir Nirash ne, akwai aikin da zamu yi, ki kula da ita". Ta kai karshe game da rage tsawonta ta sumbaci goshin Jehan, sannan ta saketa ta juya.

Da sauri ta nufi tantin Leo, tsaye ta iskosa ya kammala shirinsa cikin combat trouser ɗinsa da normal tshirt, yana kokarin sanya wuƙaƙensu na sojoji a mazaunansu a jiƙinsa. Kamewa ta yi game da sara mashi kafin ta ce gata nan. Bai yi magana ba ya wuce gaba, bayansa ta bi, suka fita ta baya babu wanda ya sani, ko su Noor basu sani ba.
Chapter 214 · 0% Book details