← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 227

Sashe 80

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗago idanu a kansa Aryan ya yi tare da cewa. "Nothing, ka gama magana dasu ne?"...... Kai ya jinjina alamar yeah, sannan ya ce. "Bro akwai gagarumin matsala a arewacin Avaris, musamman da muka je barrack na arewacin ƙasan, wai menene banbancin arewaci da gudancin ƙasar? Meyasa commond hukuncinsu daban-daban, kundin dokoki jahohinsu da hukuncinsu daban-daban, meyasa? Horon sojojinsu daban-daban, a barrack na gudancin nan ka duba yadda suka hora su Nirash! Komai a wadace, ga tsari da muhalli mai kyau, meyasa barrack na arewaci da yunwa ma ake hora sojojin? Abinci kaɗan za'a basu sai dai su kira iyayensu daga gida su tura masu in suna son ci su ƙoshi, ga wahalar horo, ga rashin muhalli mai kyau, gabaɗaya barrack ɗin sai a hankali bare kuma ɓangaren wajen kwanan ƙananan sojoji, makamansu tsofaffi matattu, horon ma ba cikakken horo ake basu ba face azabtar da gangar jikinsu, meyasa komai ya banbanta? Ko kuɗin da ake baiwa sojojinsu ya banbanta, salarinsu ɗaya, but why allowance ɗinsu yake banbanta sosai? Meyasa danger allowance, ration allowance, operation bonus na sojojin kudancin ƙasa ya banbanta dana arewacin Avaris? Barrack na kudancin ƙasar ka kalli yadda su Nirash suka rayu a ciki, cikin gata da kulawa, wasu sashe har AC ne da su, wajen kwana mai kyau, sojoji su rayu da kwargo da samun kula, ga natsuwa da sanin aiki, suna samu horo matuƙa, amma barrack na arewacin Avaris komai a lalace, dubi irin gadon da su Nirash suke kwana a kai a nan, to dubi irin gadajen dake barikin arewacin ƙasar! Komai a lalace cikin wahala da ƙunci. Hankalina ya yi mugun tashi sosai bro, kuma a haka ƴan arewacin suke rayuwa?".

Shiru Aryan ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya ce. "Gudanci basa tsoron mutuwa! Basu yarda a takasu ba! Sun san ƴancin kansu! Ba dai a cikin mission na su Nirash uku a kudancin ƙasan ɗaya a arewaci bane? Ga jira lokacin a nan ne zaka gane menene dalilin dikka wannan banbanci"....... Cike da mamaki guru ya ce. "Me haɗin mission na su Leo da banbancin dake tsakanin Arewacin Avaris da kudancin ƙasar?".

Ciro wayarsa Aryan yai tare da yin playing na voice ɗin Seraphina dake waya da Rimsha a yanzu kafin ya amsa. "A cikin wannan mission ɗin zaka gane ainahin gaskiya, a nan zaka fahimci daga ina matsalar arewacin ƙasar ta fara ta kuma samo asali, yanzu dai ba sun je yaki da ƴan ta'addan dake haurowa kudancin ƙasar suna samu mafaka ba? To ka jira su juya mission kan arewaci zaka gano komai, dalilin kenan dayasa Lion ya ce kada mu sanya baki a mission ɗin, dan akwai abin da yake dubawa a mission ɗin".

Shiru guru yai yana nazarin kalaman Aryan, lallai kuwa yanzu ba zai gane komai ba, sai su Leo sun juya Mission a kan arewacin Avaris. Nima na ce a yanzu ba zaku gane komai ba, amma mu je zuwa zaku gane.

Miƙewa Aryan ya yi tare da nufar kofar fita yana cigaba da sauraren su Seraphina, yaran nan sai shirin ALLAH, hira suke yi sosai kan SSO, Rimsha ma ta ce ai ita babbar fan ɗinsu ce, musamman Admiral wanda ni da ku readers muka san shi da Lion kuma Zayra'an, sun mutu a kan SSO yaran nan, sai bawa Seraphina labari Rimsha take yi kan ranar ma SSO sun yi live da jami'an Paris, ta bibiyi live ɗin, har da cewa zallar ilimi da jarumta ce kawai yake magana a wajen.

Seraphina ta ce. "Ni dai bana banbantasu tin da kullum da fuskokinsu a rufe, kawai dai nasan ina son SSO gabaÉ—ayansu".... Rimsha ta amsa da. "Nima bana banbantasu, kawai dai nasan su uku ne, kuma dik ina kaunarsu, kin san dama jami'ai irinsu basa nuna fuskokinsu ga duniya saboda sun fiye yin aikin sirri, shiyasa suke nufewa, dan suna shiga ko'ina yin aiki, idan al'umma ta shaida kamanninsu ai kinga akwai matsala ko?".

Seraphina ta amsa da. "Haka ne, suna da hujja ɓoye kamanninsu wa duniya, amma ina fatan ganin face ɗin ko ɗaya daga cikinsu ne ko sau ɗaya a rayuwata"...... Dariya Rimsha ta yi kafin ta amsa da. "Baki da hankali my star lady, a ina zaki samu damar ganinsu? Ki dai cigaba da yi masu addu'ar ALLAH ya cigaba da karesu yana dafa masu a dik in da suke".

My people wai na ce ya kuke tinanin Seraphina zata yi a ranar da zata gane cewa daddy Aryan É—inta ne É—aya daga cikin SSO? Ya Rimsha zata ji idan ta gane uncle Aryan É—insu SSO member ne? Ya zasu ji ranar? A gefe guda kuma sun tsani IRON FIST, kai akwai cakwakiya fa, ku dai mu je zuwa.

Ba ƙaramin daɗin sauraran hiransu Aryan yake ji ba, sai ma idan Seraphina ta yi magana tana ɗan shagwaɓe muryan nan, dik rasa kansa yake yi, sai ya ji tamkar ba'a duniya yake ba, tsabar daɗin hirarsu da yake ji har ya fito daga hotel ɗin bai sani ba, yana ta tafiya kawai abinsa. Da Seraphina ta ce. "Rimsha do you know something?". Rimsha ta amsa da aa. Seraphina ta ce. "Ina jin daddyna a raina sosai, tin shekaran jiya bai zo wajena ba, ina kewansa sosai, and bana son in ce ya zo saboda mom ta ce in daina takura mashi da yawan cewa ya zo zai daina sona sosai, amma ina cikin damuwa sosai, shi kuma yaki zuwa ban san meyasa ba". A shagwaɓe sosai ta karisa maganar.

Ai sai ga malam Aryan ya É—aura hannunsa É—aya a saman hair É—insa yana watsawa, yana jin wani irin nishaÉ—i na musamman, kai shi kansa ba zai iya faÉ—a maku a wace duniya yake ba, ga shi sai tafiya yake ta yi ba tare da yasan in da ya dosa ba....... Rimsha ta amsa mata da. "Kawai ki kirasa ki ce kina kewansa, ai tin shekaran jiya ne bai zo ba, kinga ko mom É—in ce nasan in kika faÉ—a mata ba zata hanaki kiransa ba tin da an jima, kawai ki kirasa". Ta amsa mata cike da son sanin tarihin Seraphina, ta san dai Madam ta ce mata marainiya ce bata da iyaye, to waye wannan daddyn? Gara mom da take cewa Seraph ta faÉ—a mata Madam Rohisha ce, amma dik da haka tana son sanin tarihinta, amma ta gagara tambayarta.

Da sauri Seraphina ta ce. "I remembered something Rimsha, kin san da cewa daddyna yana kama dake? Your eyes and lips iri É—aya da nasa, kuma skin É—insa up white ne irin naki"....... Ai da jin wannan magana Aryan bai san time da ya dawo cikin hankalinsa ba, É—an zare idanu yai tare da kara natsuwa yana sauraronsu. A ransa ya ce lallai kin cika jinin IRON FIST, na kara shaidawa jininmu ce ke, kaga yarinya da basira, tab!.

Ita kuwa Rimsha ta ce. "Kai anya kuwa kin gansa da kyau? Ko dan kina kewata ne yasa kike yi wa kowa kallon kama dani?"....... Da sauri ta ce. "No Rimsha, for sure yana kama dake, kinga É—an bakinsa? Like yours, sai ma idan yana magana, dimple É—inku iri É—aya, his big-big eyes, kai kuna kama sosai.

Shiru Rimsha ta É—an yi kafin ta ce. "Kai anya ba uncle Aryan bane to? Dan dik cikin uncles É—ina mun fi kama da shi, dani da shi and Yah Vash dik da Ammie muke kama, su uncle Faryan kuma da Abba suke kama"........ "In kuwa haka ne to ina ga shi ne, but zan É—auka maki pic É—insa idan ya zo, sai in tura maki ki gani idan shi ne". Seraph ta faÉ—a cike da mamaki.

Tsayawa jikin wata karanta Aryan yai tare da gyara nose mask É—insa yana mamakin yaran nan, watau Rimsha har ta samu damar kallon fuskansa tasan da waye yake kama ko? Dole ya kara taka mata birki daga zuwa kusa da shi, ita kuma Seraph yasan maganinta ne, wayar ma zai kwace ya huta da bala'in da suke son jefasa, ka ji yara, shi yanzu idan su Ammie suka san shi ne Champion na IRON FIST Ina zai sanya kansa wai?.

Yayi nisa cikin tinani bai san time da suka yi ending na call ɗin ba, sai jinsu shiru ya yi, katse kiran ya yi yana ƙoƙarin tura wayar a aljihu kenan guru ya iso wajen yana faɗin. "What brought you here bro? Ka sani dogon walking". Sai a lokacin ya ɗago kai ya fara kallon hanya, yayi nisa da hotel nasu, lallai jin gulma tai daɗi. Ɗan shafa kansa ya yi zai yi magana kenan daga gefensu suka fara jiyo hayaniya da ihun jama'a.

Kallon juna suka yi, sai kuma suka sake kallon wajen, a natse suka fara takawa a tare suka nufi wajen dan su duba menene. Suna yin kwana suka isko wata matsakaiciyar kasuwa a wajen. A bakin gate É—in suka tsaya tare kallon juna. Guru ne ya ce. "I think something bad is happening inside"........ "What am I thinking kenan". Aryan ya faÉ—a.

Magana suka yi da ido ta hanyar cewa su shiga su duba. A natse suka fara takawa izuwa ciki. Tin daga nesa suke hango jama'a a kwakkwance a ƙasa kamar ba lafiya ba, kafin su farga sai ganin wasu tsageru suka yi a tsakiyar kasuwar suna gilmawa izuwa cikin shaguna hannunsu rike da bindigu zasu kai su goma, dikkansu fuskokinsu nannaɗe da rawani, sai jajayen idanu zaka gani.

Kallon juna suka sake yi, Aryan ya ce. "I think they are armed robbers"..... Guru ya amsa da. "Dama waÉ—an nan ai daga gani ba tambaya Æ´an fashi da makami ne".......... A daidai wajen wani shago suka tsaya, shagon irin na uztazan nan ne masu sai da su dabino, zamzam, bakaruwa ta makka, jallabiyoyi da rawani dayawa. Masu shagon din sun kwanta a kasan tebur dake cikin shagon, sun natsu tsit saboda harbin bindigun da armed robbers É—in suke yi.

Kusan a tare suka miƙa hannu suka zari rawani ɗai-ɗai, dik da nose mask dake fuskokinsu hakan bai hana sun kara naɗe fuskokinsu da kyau ba, kai tsaye suka nufi in da armed robbers ɗin suke. Sai faman fashi suke yi suna kwashe kayan al'umma suna wani irin muzurai tamkar kwarto a gidan General na soja.
Chapter 80 · 0% Book details