Sashe 203
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ÆŠan zazzaro idanu a kanta suka yi, sister Maya ta ce. "Ina kika samu wannan suna mai shegen daÉ—in kuma, Haiza'an, sunan ya yi daÉ—i"...... Tana É—an murmushi ta ce. "A laptop na my Dr na ga wani folder an rubuta Haiza'an shi ne kawai na ji sunan ya kwanta mun har cikin raina".
"To waye ya ce maki suna ne? Kika sani ko wani abin ne?". Sister Maya ta faɗa.. tana saɓa babyn a saman shoulder ɗinta ta ce. "Koma dai menene sunan ya shiga raina sosai, koma ba sunan mutum bane, ko sunan wani abin ne ni dai ya mun, in na kira sunan daɗi nike ji, dan haka sunan babyn nan Haiza'an".
Maya tana murmushi ta ce. "Kin san nima sunan ya kwanta mun a rai ya burgeni?"....... "Ai sunan yana da daÉ—i ne, daga yau sunan wannan baby Haiza'an, haka zaki dinga ce mashi"..... Suna murmushi gwanin sha'awa suka fara cire kayan jariran suna yi masu wanka.
Bayan sun kammala suka sanya masu kayan sanyi saboda weather ta ruwan sama, a nan suka zauna zaman hira, sister Zinta ta sanar da sister Maya cewa ai sun kai babys ɗin ɗakin kula da su ne dan sun kamu da cuta, Maya ma ta gamsu da bayanin, sai suka hau addu'ar yaran su samu sauƙi.
A can gefe kuwa 3D na zaune office ne Dr James suna tsara yadda zasu haɗa rigakafin cutar NEXAPOX-31 kafin su haɗa ainahin maganin cutar, Dr James ya fito masu da tsarin aikin da kuma jerin abubuwan da zasu buƙata domin haɗa wannan magani da kuma rigakafin.
Suna ta faman karanta abubuwan buƙatar. Yau basu yi wani aiki sosai ba, around 1 suka je suka zuba jikin darling Dr James ya sake ɗaukansa video ya turawa World System, hakika bakina ya yi kaɗan iya zayyana maku bala'in da darling yake a ciki, ya rabb, ALLAH ya saka maka, ya bi maka hakkinka bawan ALLAH.
Bayan sun duba shi suka wuce cikin ɗakin haɗa cutar NEXAPOX-31 ɗin, suka shirya kwalaben dake ɗauke da sinadarin cutar a cikin manya-manyan kwalaye, sannan suka shirya a wani ɗakin duhu dake kusa da wajen, daga nan suka fito suka nufi ɗakin kirkire-kirkiren halittunsu da ƙaƙale-ƙaƙalensu....... In Sha ALLAH a wannan kirkire-kirkiren zaku kirkirowa kanku bala'i shehu la'anannu kawai!.
Wasu mugayen kwari dake cikin wasu glass suka sanya guard biyar majiya karfi suka ɗauka suka fitar masu da shi, kai tsaye a bayan motar da ake shirya jariran da Dr Mark yake fitarwa suka sanya katuwar glass ɗin. Kamar kullum Dr Mark ya ja motar ya fita da shi ta cikin wannan hanya da ta ɓulla cikin dokar dajin.
Su kuma suka koma cikin asibiti, da alama an kammala wannan project na kwarin, za'a miƙawa masu shi. Ko wacce ƙasa za'a sakarwa waɗan nan kwari kuma? To koma wace ƙasa ce ALLAH ya kareku daga sharrin WS, dan waɗan nan kwari suka cijeka sai ka kwanta jinya na zazzaɓa mai mugun zafi ga ciwon kai, idan kana da rabo sai ka sha jinya ka warke, idan kuma ba saura kwana mutuwa zaka yi bayan shan azaba.
Wunin wannan rana dai haka suka kasance, around 5:30 Dr Kamal and Dr James suka zo suka É—auki sister Maya and Zinta. Yaran nan sam basa son tafiya su bar babys É—insu, amma ba yadda suka iya, sun gama yi masu wankar yamma suna wasanni dasu kawai 3D suka zo suka É—aukesu, Maya har da guntun hawayenta wai bata son barin boy, ta ce zata tafi da shi Dr Kamal yaki yarda, ya yaudareta da kalamai har ta aminta ta biyosa suka tafi.
Around 1 na dare Dr Kamal and Dr James suka sake fitowa suka baro ƴan matan nasu a cikin gida. Yau ranar haɗa drugs ne na jini da suka riƙa jariran jiya. Dan haka ba sai na sake yi maku bayani kan yadda suke haɗa magani da jinin ba, already kun sani, na ɓargo da ƙashi ne baku sani ba, idan na zo nan dallah-dallah zan maku. Amma yanzu dai sun haɗa maganin kamar yadda suka saba, suka shiryasu cikin sachet kamar ko yaushe.
Sannan suka sa aka fitar masu zuwa É—akin shiryasu a cikin kwalaye, sannan suka fitar zuwa General Hospital É—in. Around 4 suka kammala, suka koma gidansu, sun isko su Zinta na barci, dan yau shayar da su maganin barci suna yi a cikin lemu da suka je yin lunch ba tare da su Zinta sun sani ba.
Hankalin 3D ya fara tashi tin daren jiya da su Maya suka nemi titseyesu kan ina suka je, daga nan suka yanke shawarar rinƙa masu maganin barci cikin dare, dan basu son suga hankalin ƴan matan nasu a tashe, kuma ba zasu iya faɗa masu abin da suke yi ba.
Bayan sun dawo wanka suka yi, suka shirya cikin wasu sleeping dress ɗin, a gefen matan nasu dik suka kwakkwanta tare da jawosu jikinsu, ba jimawa barci ya yi awon gaba da su. While shi kuma Dr Mark yana can yana kwasan hanya zai fitar da kaya daga cikin ƙasan ta ɓarauniyar hanya.
D-------O-------L🔥
Ita kuwa Angelina tana zaune kusa da Zaynish tana aikin satar kallonsa, Unays kuma yana satar kallonta, yana ta ALLAH ALLAH Zaynish ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna.
Kiran Ummie ne ya shigo wayar Zaynish. Ciro wayar ya yi daga aljihunsa. Kashe kiran ya yi game da kiranta. Bugu É—aya ta É—auka, kara wayar a kunne ya yi game da cewa. "Assalamu alaikum". A yadda ya yi magana ko Angelina dake kusa da shi bata ji me ya ce ba.
Daga ɗayan ɓangaren Ummie dake zaune saman sabbin sofa set ɗinta da ta yi wa kanta ne ta amsa da. "Waalaikumussalam ɗan uwana"....... "Ina wuni Aunty Ummie?"........ "Lafiya lou Alhamdllh ya aiki da abokan aikin naka?"....... "Suna nan lafiya, ya gida da Yaya Faisal? Ya dawo ne?".
Kai ta ɗan girgiza kafin ta ce. "A'a bai dawo ba, ya dai turo mana saƙo jiya, ina su Noor? Kwana biyu ban jisu ba?"..... Kallon in da Noor yake ya ɗan yi kafin ya ce. "Suna nan lafiya, Aunty Ummie kina mana addu'a sosai ko? Kin san yanzu addu'a kawai muke da buƙata".
"Sosaima, kullum sai na yi maku, ALLAH ya kare mun kai, yaushe zaka dawo ka fara aiki a nan dan ka ɗauka mana fansa? Ka kore mana ƴan ta'addan nan?"......... Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Sai mun kammala wannan FIVE MISSION ɗin, a wannan lokacin ne muke da zaɓi, ko mu zauna a Avaris mu yi aiki ko kuma mu yi applying Nigeria or Niger dik wanda kika zaɓa mun, so in mun gama FIVE MISSION muna dan ƴancin zaɓar ƙasar da muke son yin aiki".
Shiru ta É—an yi, sai kuma ta ce. "Zan yi tinanin in da zaka yi aiki, amma yanzu dai yaushe zaku gama?"...... "Very soon In Sha ALLAH, ke dai ki cigaba da yi mana addu'a".
"In Sha ALLAH addu'a kam ba fashi, yanzu dik ajiye wannan magana, batun aure na kiraka mu yi"...... Kada ku manta ita bata san sun tafi mission ba, ya ɓoye mata dan kada ya ɗaga mata hankali, yanzu ta ɗauka suna barrack ne shiyasa ta ɗauko mashi batun aure.
Ƙasa ya ƙara yi da murya wajen cewa. "Kai Aunty Ummie, na faɗa maki bani da zaɓi a kan mace, kawai ki bani dik wacce tai maki, ki zaɓota, na baki wuƙa da nama, ko wacece kika kawo zan aureta, na yi alkawari, amma ki kawo wacce zata girmamaki fiye da yadda zata girmamani, wacce zata soki kamar yadda nike sonki, wacce zata maki biyayya tamkar yacce zata mun, wacce zata kula dake tamkar yacce zata kula dani, idan ba mai wannan ɗabi'u ba bana so kada ki kawota!"...…. Murmushi ne ya kubce mata, cike da farincikin irin yadda ya bata muhimmanci a rayuwansa ta ce. "Ina wacce ka ce ka taɓa gani? Wacce ka fara jin sonta a ranka? Bana son ka rasa soyayyarka ta farko".
Nisawa ya ɗan yi game da cewa. "Ban san in da take ba, na faɗa maki tin daga ranar ban sake ganinta ba, dan haka ni nama mance da ita, kawai ki nemo mun taki"......... "To shikenan zan kuwa nemo maka haɗaɗɗiya, kana zuwa hutu sai aure kawai"........ Kai ya ɗan jinjina kafin ya ce. "A'a, mu ai muna da lokacin yin aure, sai mun samu umarni daga sama, idan kin samo matar ki sanar dani sai in shigar da buƙatar auren a tsare, idan manyanmu sun yarda shikenan in na dawo sai ayi komai".
Da to ta amsa kafin ta ce. "To ka kula da kanka, ka ci abinci ka yi ibada mai kyau, a dik in da kake ka sani ALLAH yana ganinka, kada ka cutar da kowa, ka zauna da kowa da zuciya ɗaya, hakance zai sanya ba zasu iya cutar da kai ba, a dik in da kake ka tausayawa mace, kaga mai raunice, ka tausayawa kanka, ka tina kai maraya ne, baka da kowa sai ni, ba zan iya jurar rashinka ba, ka tina hakan, ka rinƙa addu'a da alwala kafin kwanciya barci, ALLAH ya yi maka albarka".
Hakika kunnuwansa sun yi mugun sabo da jin kalaman Aunty Ummie na nasiha kullum, har ya haddace, dan haka da In Sha ALLAH ya amsa mata. Sai ta sake cewa. "Ina sonka sosai rabin raina".
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, bai san daɗin iyaye ba, amma a kanta yasan ainahin menene soyayya, ta sadaukar da komai saboda shi, lallai soyayyarta ce ake cewa true love........ "Nima ina sonki sosai Aunty Ummina, ba zan taɓa son wani abu rabin son da nike yi maki ba, ki kula da kanki, dik abin da yake damunki ki yi gaggawar sanar dani kin ji?".