← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 227

Sashe 4

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jami'an sun samu sun shiga tsakiyar harabar gidan, amma babu hanyar kutsawa ciki, saboda door É—in parlo ya fi ko'ina kamawa da wuta, su Eagle sun san za'ayi yunkurin kawo taimako shiyasa yaransa suka fi zubawa jikin door fetur sosai, sun kware a iya aiki over shiyasa.

Dik yadda waÉ—an nan jami'ai da jama'ar unguwa suka so cetar Dr Hushaima da yarta abin ya faskara, domin babu hanya, suna ji suna gani suka ja da baya dan wutar ta zarce yadda suke tinani. Tin karfe 5 na asuba ake abu É—aya sai karfe 12 na rana suka samu damar iya kashe wutar, amma ya ci gidaje almost 10 zuwa sama. Gidan Dr Hushaima ko tsinke ba'a iya fitarwa ba, komai ya kone kurmus, gwara ma sauran gidajen akwai abubuwan da suka É—an ragu, amma nata gidan abin ya munana sosai. Jama'a sai jimami suke yi, sunga balai yau.

Bayan lafawar gobar fire investigation, ATF sun halacci wajen domin binciken menene ya jawo wanna gobara mai karfi haka?. Sai dai iya bincikensu ya nuna masu cewa gas ce ta fashe, bayan ita basu samu wata makama ba. Jama'ar unguwa faÉ—i suke Dr Hushaima tana da balain kula, ya aka yi aka samu wanna matsala, amsar da mutane suka rasa kenan.

TO FARKO KENAN DAGA LITTAFIN ZAKUNA BIYAR, SHIN YAZATA KAYA? INA YAR DR? SHIN HAR DA ITA TA RASA RANTA NE? INA WANDA DR TA CETA? MEYASA DR TA ZAƁI TA RASA RANTA A KAN TA BUƊI BAKI TA FAƊI IN DA YAKE? MENENE ZAI BIYO BAYA BAYAN MUTUWA DR DA YARTA? MUJE ZUWA AKWAI KALLO NAN GABA KAƊAN.

SHIN MUTANE NE ZAKUNA BIYAR ƊIN? DABBOBI NE? WHY ZAKUNA BIYAR? BA ZAKI TAƁA SANIN ZAKUNA BIYAR BA HAR SAI KIN BIBIYI WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSA HAR KARSHE, KAMAR YADDA NA CE A FARKO, BA ZAN CE KOMAI BA, NA BARKU DA ALKALANCI.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA STAR LADY TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

2-11-2025.🔥

E_____________2.

NEW YORK.🔥

Jami'an sun yi iya bincikensu amma ba su iya gano menene ya haddasa wannan gobara a cikin gidan ba, iya abunda suka sani kawai shine gas ne ya fashe.

Haka suka kwashi jiki suka bar gidan jama'a cike da jimami kowa ya koma bakin aikinsa. A gaskiya jama'a sunyi babbar rashi, domin dr mace ce wace kowa ya shaida tana da kyawawan É—abi'u da kyawawan halaye, duk anguwan kowa yana alfahari da ita kuma kowa yana son kasancewa tare da ita, ko me dare in baka da lafiya ka kirata zata fita ta duba maka, bugu da kari abin hanunta bai rufe mata ido ba, kome ka tambaye ta zata baka kyauta in dai bai fi karfin ta ba, gaskiya jama'a sun ji babu daÉ—i sosai.

Haka unguwar yau ta kasance shiru, dik da dama suna kasancewa a cikin shirun babu hayaniya, amma na yau daban ne saboda mutuwar doctor da Æ´arta.

9:00PM.

Agogon birnin new york ya sake bugawa, kasancewar unguwar ta manyan mutane ne sai ya zama kowa ya shiga gida, ga kuma mutuwar da ya faru sai ya kara sanyawa ko'ina yai tsit sosai, then akwai alamar ruwan sama a sararin samaniya, hadari bakin kiri, shi ya kara kora kowa gida........ A hankali sauti na wasu irin jiga-jigan motoci da suka amsa sunansu motoci ya fara ratsowa cikin unguwar, tun daga kan yanayin sautin kukansu zaka san motoci ne na manyan kai, ajere suka keto titin wannan unguwa suna tafiya a wani irin slow montion. Motoci ne guda biyar cip.

Kai tsaye a ƙofar gate ɗin gidan dr suka paka, suna parking a tare aka buɗe kofofin motocin, kan ka ce me wasu irin jiga-jiga mutane madaka katti sun danno waje, dikkansu sanye suke da baƙar wando da kuma farar t-shirt a jikinsu, while sun ɗaura tail coat a saman T-shirt ɗin wacce ta kai masu har gwiwa. Da ka gansu ko ba a faɗa maka ba kasan wasu tawaga ne na daban, imma jami'ai ko kuma gangsters, mutane biyar ne suka fito a cikin motoci biyar, kowane daga nashi motan daban-daban.

Bawai iya su biyar ba ne a cikin motoci, a'a, akwai wasu sannan da drivers daban, dan dukansu daga back seat suka fito, cikin gidan dr suka wuce, a tare suke tafiya, in short a tare suke É—aga kafa su kuma sauke, yadda kuka san kwararru kuma shahararrun gangster's, a haka suka shiga cikin gida.

GabaÉ—aya mutanen unguwa suna cikin gida babu wanda ya san meke faruwa, saboda motocinsu ba irin motoci masu karan nan ba ne, mota ce da saita matsa kusa da kai zaka san tana zuwa, asali irin wannan motocin jami'an sirri sun fi amfani da ita ko kuma manyan gangsters da suka shahara a duniya, mota ce bata kowa ba.

Sun ɗauki a kalla minti 10 a cikin gidan dr kafin su fito a jere, ɗaya daga cikinsu hannunsa ɗauke da wata ƙatuwar abu kamar kwali aka nannaɗe, dikka sauran huɗu akwai abubuwan da suka rike a hannunsu, da alama daga cikin kayan doctor wa inda basu ƙone ba suka tattaro ko dai wani abin, dik yadda aka yi suna da alaka da ita ko makamancin haka. Cikin motocinsu suka koma, a jere suka bar unguwar kamar da suka shigo TO FA, TAFIYAR YANZU TA FARA FA WACECE DR? ME KUKE TINANIN ZAI FARU? SU WANENE WAƊAN NAN MUTANE? MU JE ZUWA DAI.

-------------------------------🔥

KASAR AVARIS.

Avaris kasa ce dake makotaka da Us a kudu ta tsakiya. Kasa ce wacce take da tarin tattalin arziki, kama daga kan man fetur, gold, red diamond, har da su uranion suna da shi, suna da tattalin arziki daga albarkatun kasa da ruwa fiye da yadda mutum yake zata. Kasa ce dake cin gashin kanta, kasa ce dake da karfin siyasa da soji, sai dai gabaɗaya mafiya yawa daga cikin states na kasan a lalace suke, ga fama da yunwa da talauci, dik da wannan tarin arziki da suke da shi, ƴan ta'addan sun hana wasu daga cikin yankunan kasan zaman lafiya, kidnappers, da ɓarayin fili dana ɓoye, cin hanci da rashawa, gurɓatattun shuwagabanni, a wasu yankunan ma ƴan'ta'addan sun fi gwamnati karfi, su ke juya gari har da karɓar haraji da sauransu, abu kamar shirin film, amma zallar gaskiya ce!! Amma mu kutsa cikin labarin zamu fahimci daga ina matsalar Avaris ta samo asali.

Eldoria State. Nan ne babban birnin kasar Avaris wanda suke ji da ita, birnine da ta ƙawatu matuƙa, domin a nan Diamon palace take, wato fadar shugaban kasar Avaris, birni ne na manyan alhazai mai ɗauke da dogayen gine-gine na alfarma, benayen da aka yi su high rise building masu design daban-daban, ga manya-manyan estate na gani na faɗa masu tsarin ginin turai, da su urban complex, glass towers, residential towers da dai sauransu. Wannan kasa tana da kyakkyawar alaƙa da turawan yamma, akan kasuwancin fili dana ɓoye, kai akwai fa abubuwa sosai sai mun kutsa ciki zaku gane karatun.

-----------------------🔥

AZURE BARRACK. Babban barikin soji na birnin Eldoria.

Shinfidaɗɗen ginine wanda aka shinfiɗa tamkar ba za'a mutu ba, ka kai iya kallonka baka iya ganin karshen wannan gini saboda girmansa, gini ne dake ɗauke da Academys kala biyu bayan sansanin soja, sannan gini ne da sai mun kutsa ciki kawai zaku iya ganeta. Dik wasu manyan jami'an da suka shahara a manyan kasashe duniya ta sansu, to AZURE BARRACK ne ta kyankyashesu, daga ƙasashe da dama ana kawo manyan gifted jami'ai dan a horar da su, dik manyan jami'an manyan kasashen dake ji da kansu a nan ake horasu cikin sirri ba tare da sanin duniya ba!.

Katafaren gate ɗin farko na shiga. Gate ɗin dakakkiyar ƙarfe ce mai ƙarfi tare da tsarin tsaro na zamani mai matukar ban mamaki, akwai kamar CCTV mai karfin gani daga nesa kilomita 5, da na'urorin tantance mutane wato biometric scanner wanda in dai zaka gifta wannan gate ɗin to sai ta yi scanning ɗinka ta turawa ɗakin da jami'ai na musamman ke kallon shige da fice na Barrack ɗin. Akwai katafaren office a bakin gate ta ciki dan karin masu gadin da zasu tarbi masu shigowa!.

Mu kutsa ciki ta shinfiɗaɗɗiyar titin da ta miƙe tin daga gate na farko har izuwa can cikin Barrack ɗin, ta ko'ina ka juya a cikin barikin nan dakakkun jiga-jigan jami'ai ne ke shawagi, ga fuskokinsu sam babu kyan gani saboda yadda suka ɗaure tamau, suna wani muzurai tamkar ba mutane ba!.

Manya-manyan gine-gine ne masu balain kyau a cikin wannan bariki, har da upstairs masu matukar tsayi dan manyan jiga-jigan sojoji. Akwai babban parade ground, babban fili mai ɗaukar mutane da yawa dan horo da taruka. Filin ya kasance da tsananin kyau tare da alamomi dan sauƙaƙa atisaye. Ga abubuwan training daban-daban a cikin wannan waje.

Yankin da offices na jiga-jigan soja yake watau headquarters yana gefe guda cikin tsari da tsaruwa. Office ɗin The General Of The Army, watau shugaban dikkan sojoji kenan, daga kansa babu wata muƙami a soji, office ɗinsa babban gini ne mai ɗauke da offisoshi daban-daban dan manyan Generals na soji kamarsu Brigadier General, Lieutenant General, Major General, General, Colonel, Captain da dai sauransu. Kowani office cike yake da kayan more rayuwa dan jin daɗisu suma. Dik wanda bai san ya barikin soja take ba to yau zai sani.

Akwai katafaren Training Academy, watau makarantar horarwa. Babban gini mai cike da É—akunan karatu, laboratories, da É—akunan nazarin makamai. A gefe ga filin horar da dabarun yaki da training na jiki. Ga tsarin dijital dan koyarwa, akwai allunan zamani irinsu smartboards da na'urorin koyarwa ta yanar gizo kai tsaye.

Gefe guda akwai katafaren masaukin sojoji watau Barracks. Ƙayatattun ɗakuna masu tsabta da kyau, tare da kwanciyar kula ga sojoji ko ɗalibai na musamman masu bincike tamkar aljanu, yadda kuka san hostel haka Academy ɗinsu yake, ɓangaren mata daban ɓangaren maza daban, ga tsari mai kyau. Gidan kowane soja mai muƙami ba wai ɗalibai ba ya kasance tare da wutar lantarki, ruwan famfo, da tsarin ɗumama ko sanyaya wuri.
Chapter 4 · 0% Book details