← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 227

Sashe 184

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Slowly ya saketa game da lumshe idanunsa, kafin wani É—an lokaci ya yi barcin gaske mai daÉ—in da ya jima bai yi irinsa ba. Shiru ta zauna tana ta faman kallonsa, bata son matsawa daga kusa da shi ko kaÉ—an, tana ganin kamar rabasu za'ayi idan ta matsa, har da kwanciyar ruf da ciki, ta É—aura kanta a saman kirjinsa, tana kallon face É—insa, a hankali barci ya É—auketa ita ma.

CRYSTAL PALACE, idan na kira sunan CRYSTAL PALACE a yayin da muke cikin CRYSTAL PALACE ɗin muna labari to ina nufin zuciyar CRYSTAL PALACE gabaɗaya ne, watau gidan MUHAMMAD HAIZA'AN, gidansa ne zuciyar CRYSTAL PALACE, gidan da ya fita daban a tsarin ginin cikin CRYSTAL PALACE ɗin, gidan da aka ware a waje daban, yana gefe can, wani shinfiɗaɗɗen titi da aka shinfiɗa wanda ya miƙe har cikin gidan kawai abin kallo ne, kun san dukiya tai kuka ba kaɗan ba, ya rabb, tin daga farkon titin nan jiga-jigan jami'an SSO ne suke shawagi, ko tsuntsuwa basa bari ta gifta ta sararin samaniyar gidan Haiza'an, lallai na shaida dik wani karfin iko ya kare a wannan waje.

Zaku rantse da ALLAH dik jami'an dake US aka zuba a wannan gidan, wasu irin guards waɗan da ko fuskansu baka iya gani face idanunsu dake rikitar da zuciyar bawa su ke gadin gidan, ya kuke tinanin san da yake raye kenan? Wai a haka ya rasu ne wannan karfin ikon! Ya ALLAH. To mu yi tattaki zuwa cikin gidan dan mu ga meke going a ciki, ya tsarin gidan yake tin da na ce ya fita daban da tsarin sauran gine-ginen dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Jama'a ban taɓa tinanin za'a samu gidan da zai fi Black Tiger empire haɗuwa ba, sai ga CRYSTAL PALACE da kanta, ga kuma uwa uba zuciyar CRYSTAL PALACE watau gidan Haiza'an, ya ALLAH kai mana arziki mai albarka kawai.

Siffar ginin gidan ya kasance irin ginin mediterranean ɗin nan ne ta gefe-gefe, daga ta gaban gidan kuwa zallar glass ne, girman gidan ya fi fili flot 20, saɓanin benayen CRYSTAL PALACE shi wannan gida yana da gate, an kewayesa ne, sai kun wuci gate uku manya-manyan masu cike da tsaro na ban mamaki kafin ku ƙarisa cikin gidan, sannan shi wannan hawa uku ne kawai.

A gefe guda harabar gidan ga tampatsetsen lambu mai ɗauke da ƙananan arche, ƙananan ƙoramu ne da aka yi su dan ƙawata lambun, ga wasu irin fitillu da aka ƙawata lambun wanda ko dare ne zaku zaci rana ne saboda haskensu da ƙawarsu, uwa uba lambun da glass wall aka kewayesa, daga waje kana iya hango haɗuwarsa ta ciki, ya ALLAH, ga wasu kifaye orange and red da aka zuba cikin tampatsetsen glass suna ta yawo cikin ruwa, shi ma ya ƙara ƙawata lambun matuƙa, ga wasu flowers masu mugun kyau da ɗaukar hankali, a bakin kofar lambun daga gefe an yi wasu flower da aka shukasu aka yi siffar sunan HAIZA'AN'S GARDEN da su, jama'a wlh lambun nan ya haɗu fiye da yadda kuke hasashensa a ranku, kuɗin da aka narƙa a wannan waje, kai kuɗin mahaikatan dake gyran lambum nan kawai jarin wani ɗan siyasa ne a Avaris!.

A budget ake cire kuÉ—in masu aikin gyaran gidan Haiza'an, a shekara ake lissafi a cire kuÉ—in masu gyaran gidan, akwai mata akwai maza, kowa da aikinsa, kullum na ALLAH sai sun share ko'ina sun gyara tamkar yana raye............ Jama'a baku tunanin bayan mutuwar daddy Haiza'an akwai abin da ya faru kuwa?.

A tsakiyar tampatsetsen harabar gidan akwai wani waterfall wall, architecture design of gunking zaki ne dake faman fesa ruwa daga bakinsa, ya wage baki sosai ruwa na zuba ta bakin nasa, a ƙasa an yi mashi round tamkar rijiya ruwan da yake zubarwa tana taruwa a wajen, daga can ƙasa akwai hanyar da ruwan yake sake komawa bakin zakin, ba karamin ƙara gyara gidan wannan design ɗin ya yi ba. Ga wasu shuke-shuken flowers a gefe guda da suka ƙarawa gidan haɗuwa.

A gefen dama akwai guest suite, ɗakunan baki guda biyu tare da toilet da kayan more rayuwa a ciki. A gefen lambu akwai tangamemen garage na parkin motocin wanda tsab zai iya ɗauke motoci 30 ciff, gate na shiga garage ɗin automatic ne, da kansa yake buɗewa da rufewa, har yau akwai jiga-jigan motocin daddy guda biyar ciff a fake, tsadaddun motoci ne da suka haɗa da Maserati Levante Trofeo, Rolls-Royce Cullinan, Bugatti Chiron Super Sport, Mercedes-AMG G 63 sai wata mota mai tuƙa ƙanta, motocin dik an rufesu da car cover.

Sannan akwai katafaren swimming pool a ta gefen ginin ba harabar gidan ba, a ɗan gefe aka ƙawata shi, yana ɗauke da sky blue ruwa mai balain kyau da ɗaukar hankali. A gefen pool akwai glass wall na tennis, basketball, filin wasanni na tennis da basketball har ma da football.

A gaban zakin wani tampatsetsen baranda ne a wajen wanda babban parlo door yake kansa. Kai mu haura ground floor dan wlh ƙawartuwar harabar gidan nan ya zarce in iya faɗa maku shi lokaci guda, sai a hankali.

Mu lula grand entrance hall, babban kofar shiga ground floor, kofar ya haɗu, ga kakkafar tsaro da idan ba mamallakan ginin ba babu wanda ya isa ƙetarawa izuwa ciki, ya fi kofofin CRYSTAL PALACE tsaro da amfani da kimiyar zamani.

Kana shiga kofar akwai wani dogon corridor mai kyau wanda yake ɗauke da fitilar chandeliers a tsakiyar corridor ɗin daga sama, duk tsawon corridor din nan sai da chandeliers ɗin nan ya kusa kai ƙasa saboda tsawo da haɗuwarsa.

Idan ka wuce corridor ɗin sai haɗaɗen automatic door, kana buɗesa da wani katafaren living room zaka fara cin karo, haɗuwar parlon nan ba zai faɗu ba, kusan za'a ce five in one ne parlon, dan haɗaɗɗun luntsuma-luntsumar sofa set kala biyar ne a cikin parlon, kowani set ya haɗu matuƙa.

A cikin parlon akwai door da zai sadaku da tamgamemen mediterranean kitchen, kitchen ne mai siffa ra gargajiya, amma su gas na zamani ne a cikinsa, da alama daddy yana son gargajiya, dan a waje harahar gidan cikin wannan lambu akwai hut da aka ƙawata har guda uku, sai dai bukkar ba'a kewayesu da komai ba face glass, samansu kuma exactly bukar da ake yi a ƙauye, cikin bukkokin kuma haɗaɗu kujeru ne na zama dan shaƙatawa, to da alama yana ɗan son gargajiya.

Iya wannan kitchen ɗin ne a ground floor, sai wani haɗaɗɗen butterfly stair case da ya yi sama izuwa first floor, nan ma akwai babban parlo two in one, sai master suite, katafaren ɗaki mai ɗauke da babban balcony da ke kallon wajen harabar gidan da sauran cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Sai katafaren toilet mai ƙunshe da jacuzzi da shower mai ban sha'awa.

Bayan master suite akwai luxury bedrooms guda uku, ɗaya ɗakin yara ne, biyun kuma ɗaya na matar gida, ɗaya kuma babu kowa a ciki sai kayan alatu da aka zuba. Kowanne ɗaki na da toilet haɗaɗɗe da balcony, ga furnitures made in Dubai masu matuƙar kyau da tsada.

Bayansu akwai dining hall, shi ma dik glass wall ne, daga parlon first floor É—in kana hango cikin dining hall É—in, katan table da haÉ—aÉ—É—un chairs guda 24 ne a ciki, sai show glass da ake zuba cups and plates a cikin dining hall É—in, ga haÉ—aÉ—en decorations, and daga cikin dining hall É—in kana iya hango wannan haÉ—aÉ—É—en lambun na waje mai É—aukar hankali.

A gefen É—akin daddy Haiza'an akwai family lounge, wani É—aki ne na taron iyali tare da TV mai faÉ—i da sofas masu taushi.

To mu haura last floor muga me a ciki, ni fa ina son in ga na ɗauko maku abubuwan da cigabansa bai zo mana Naija ba, dan ni a tinanina da yadda na ɗauki rubuta littafi ana rubuce-rubuce ne dan ƙaruwar al'umma da wayar masu da kai game da basu ilmin da ALLAH ya hore maka wanda su basu sani ba........Kazalika kuma makaranta a tinanina kuna karance-karance ne dan ku samu ƙarin ilimi, so bai kamata ace kuna karanta abin da muke da shi a Naija ba, abin da already kun san shi sai dai ayi ta maimaitawa, shiyasa dik rubuce-rubucena yake ketarawa ƙasashe, mu zaƙulo abubuwan da baku sani ba dan ku sani ku kara samun ilmi, kunga ko baku je ƙasashe ba kun san me yake wajen, wannan shi ne kun yi karatu mai riba, kun kara samun ilmi!.

Last floor. Tampatsetsen gym room ne a wajen da aka ƙawata shi dan motsa jiki tare da kayan zamani, sai haɗaɗɗen cinema room dan kallon fina-finai mai ɗauke da fitillun chandelier da kujeru masu taushi dan zaman kallon film da family.

Baya ga shi akwai haɗaɗen roof terrace a saman, wani ƙaramin filin shakatawa ne, tare da barbecue station da kujerun hutawa. And daddy yana da home office na musamman dan aiki, tare da shelves da table na zamani....... A can sama kololuwa wajen sauƙar madaidaiciyar private jet ɗin daddy ne, akwai haɗaɗɗen jirgin da kowa zai yi mafarkin mallaka a wajen an faka shi, jikin jirgin ɗauke yake da sunan MUHAMMAD HAIZA'AN da harafin larabci

To nifa my people wannan lambu na daddy ya tafi dani, dan haka ko aiki ne su Lion su É—aukeni a wannan lambu, dan gaskiya ina son rayuwa a cikinsa, ya haÉ—u ne.

Jama'a ALLAH ya mana arziki mai albarka, ya bamu lahira mai kyau, amma gaskiya zuciyar CRYSTAL PALACE ta haÉ—u, haÉ—uwa fiye da tinani.

------------------------
Chapter 184 · 0% Book details