← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 227

Sashe 5

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga gefe can kuma akwai Military Hospital. Babban asibiti mai É—auke da dukkan kayan aiki tamkar a wajen barrack, É—akunan gwaje-gwaje, É—akunan tiyata, da É—akin kulawa na musamman watau ICU. Likitoci da ma'aikata masu kwarewa amma dikkansu sojojine, kuma su ake yiwa lakabi da surgeon Brigadiers ko surgeon Generals, to su ne likitocin sojoji.

Sannan akwai sports complex, filin wasanni daban-daban kamar na kwallon kafa, kwando, da gudun tsere. Wurin motsa jiki watau gym na zamani tare da kayan zamani.

Sai uwa uba wajen obstacle course, filin ne da aka tsara dan gwaje-gwaje da horaswa na sojoji kamar hawan igiya, gudun duwatsu, da tsallake rami, ko shiga ruwan teku, daga jin wanna abin da na kirga nasan kun gane ya yanayin wajen yake, cike da duwatse, tsaunika, bishiyoyi da kuma teku a gefe, shi a can nesa da barrack É—in yake, dik a ciki ne, amma yana da nisa da wajen da sojoji suke rayuwa.

Kada mu yi tuya mu manta da albasa, akwai mess hall, watau wajen cin abinci kenan. Babban É—akin cin abinci mai iya É—aukar mutane da yawa. Kayan more rayuwa kamar É—akunan girki na zamani masu manya-manyan gas, da tsarin rarraba abinci cikin tsari da natsuwa.

Sannan akwai armory and tech hu, waje ne dan ajiya da gwajin makamai, kamar irin su drones na yaki haka da sauransu, nasan tin daga nan zaku gane girman wanna GIDAN SOJA ya wuci yadda na faɗa a bakina ko? Sannan a cikin armory tech hu akwai gefe da aka tanada dan bincike da kirkire-kirkiren kayan fasaha na soja. Ina daurewa ne in yo maku bayanin komai dan ba zan sake dogon bayani a kan Barrack ɗin ba, Sannan kusan yadda yake da kyau idan ina rubutu kan wani ɓangare ba sai na sake tsayawa dogon bayanin yadda yake ba.

Security control center, wannan ba sai na yi magana ba tin da na ce maku waje ne da ake yaye gifted jami'ai nasan kun san tsaron wajen ai ba'a magana.

Muleƙa senior officers quarters. Gidaje masu kyau tare da kayan more rayuwa ga manya-manyan mukaman soja. Harabar gidan kowani babban jami'i ta kasance mai tsabta da shuke-shuke masu kyau dan morewarsu suma, ba iya yaki kawai aka sansu da shi ba.

Lastly akwai recreation center, wajen nishaɗi a yayin hutun aiki, akwai irinsu sinima, ɗakin wasa na zamani, da wurin zama dan shakatawa a lokacin da ba lokacin aiki ba. Lambunan zamani da shuke-shuke masu kyau dan ƙara kyawun wuri, fitillu masu kyau a kowanne ɓangare dan inganta tsaro da kyau, wutar lantarki 24h ba ɗaukewa. Hanyoyi masu kyau da babu gargada, da alamomi na kwatance watau alamomin nambobi a kan titin. Dik wani barrack na kasashen ƙetare haka suke gwanin ban sha'awa da burgewa. Bari in yi tambaya! Shin ya barrack na kasarku take? Wani tsari aka yi wa sojojinku dan suma su ji daɗi kamar kowani ɗan kasa? Wani irin yanayi ake barinsu a ciki? Suda suka sadaukar da rayukansu saboda kare ƙasa, al'umma da dukiyansu, wani irin sakayya ake yi masu?. ALLAH YA TSARE MANA KU SOJOJINMU YA INGANTA AIKIN NAN NAKU!.

------------------------🔥

Yau takama Monday, dubbannin sojoji ne suke shawagi a ko'ina, tamkar za'ayi yaƙin duniya ta uku, sai kai komo suke yi, kowanne ka ɗaga ido ka kalla ba zaka sake sha'awar kallonsa ba, dan sai hantar cikinka ta kaɗa, idanunsu jajir kamar wuta, sai wasu muzurai suke yi, ga jiga-jigan makamai rirrike a hannayensu.

A gefe guda kuma ga matasan sojojin da aka É—auka cikin satin nan dan horarwa, kowani matashi yana shirye cikin kayansa masu balain kyau, dik sabbin matasan da suka zo suna tsaitsai ne a cikin tsakiyar assembly hall É—insu, kowani matashi ka É—aga idanu ka kallah zaka gansa cike da tsantsar muradinsa na son wanna aiki game da kwarin gwiwa, dayawansu suna tsaye ne da abokansu, wasu zaka gansu group uku, wasu su huÉ—u a wajen, wasu ma su biyu, sai hira suke yi, kuma dikkansu suna sanye da p-cap na sojoji a kansu, kowa jinsa yake yi a sama yau, suna jin tamkar sun zama sojoji, dan dik wanda yake wajen burinsa kenan.

TO ALLAH yasa kuna da rabon haye atisaye ku zama sojojin da kuke fata, kuma ALLAH yasa aikin ya zame maku alkhairi har ku yi alfahari da shi!.

Lokaci guda dikkan sojojin hankalinsu ya tattare izuwa kan hanyar shigowa hall É—in sakamakon karar sautin tsaro da suka ji yana tashi alamar an dinfaro hall É—in. Kan ka ce me kuma sun jera line by line tamkar assembly a primary school, sai dai tsayuwarsu cikin jarumta da karfafa kai ne.

Wani kyakkyawan matashi fari tas da ba zai wuci 33 years haka bane ya shigo cikin hall ɗin, sanye yake cikin kakinsa, kana ganinsa kaga jarumi dakakken namiji, fuskansa babu annuri babu alamar wasa, kai tsaye kan stage dake hall ɗin ya nufa cikin takun dake nuna lallai jininsa a tafashe yake. Yana hawa ya furta attention babu wasa yana kara haɗe rai. Da karfi suka buga kafa ɗaya a ƙasa game da sara mashi, wannan ma yana daga cikin dokokin GIDAN SOJA da suka karanta kafin su zo nan.

CAPTAIN ONBISH CO shi ne sunan dake a gaban uniform É—insa.

Captain kallonsu ya fara yi one by one yana karawa kamar yana karantar wani abin a tattare da su kuma kamar yana karantar yanayinsu. A daidai wannan lokacin commander ya shigo, shi ma cikin jarumta da nuna kwarin jiki, amma shi zai iya kai 43 to 45 years haka. A saman stage ɗin shi ma ya zo ya tsaya yana kallon yadda matasan sojojin nan suke a tsaitsaye cikin ƙamewa, ya ji daɗi har cikin ransa, dan tin daga kan yanayin tsayuwarsu ya fahimci suna da zumman cinwa abin da suka sa a gaba. Hall ɗin nan gabaɗaya kewaye yake jiga-jigan sojoji jaruman gaske.

Captain ne ya É—aga hannu ya sarawa Commander cikin girmamawa da kwarewa a aiki. Sara mashi Commander ma ya yi kafin ya juya ya fuskanci matasan nan, a take suma suka É—aga hannu suka sara mashi, jinjina masu kai ya yi kafin cikin kakkaifar harshe ya ce. "Attention!". Kafa É—aya suka sake bugawa a kasa da karfi tare da kara kamewa kam!.

"1, 2, 3 start". Commander ya sake faÉ—a cikin É—aga muryar!.

Yana cewa start suka buÉ—i baki game da É—aga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA da suke yi a kowacce safiya kamar haka...... "We march through fire, through storm and rain, With steel in heart, we bear the pain. For land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, Through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, Our oath is strong, we'll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one,
Through darkest nights, til battle's won.
With fearless hearts, our banners wave,
We are the strong, we are the brave!".

Bakinsu a haÉ—e suka rera wanna zazzafar taken nasu, dan yana rubuce cikin document É—insu, kafin su zo sai da suka haddace taken da dik wani dokan soja.

Suna kai karshe suka daddage suka buga kafa ɗaya tare da sarawa manyan nasu. Watau tun da suka fara rera wannan take dik wani soja dake AZURE sai da ya miƙe ya kame a in da yake, wannan take nasu yana sanya sojojin su ji tamkar a filin daga suke, yana balain kara masu kwarin gwiwa, motsa zuƙata da gangan jikinsu da tsumasu yake, ga shi assembly hall ɗin akwai las speaker a ciki da in suna taken dik wanda yake cikin GIDAN SOJA sai ya ji, hakan zai sanya su mimmiƙe su tsaya cak game da sanya hannu a goshi alamar girmamawa ga GIDAN SOJA GIDAN WUTA!!!!. Idan aka kamaka ana rera taken baka miƙe ka ƙame saboda girmamawa ga taken ba ma sai ka sha horo sosai! Haddace taken wajibi ne a gareka!.

Bayan sun kammala suna sauke ajiyar zuciya a hankali hankali ne Commander ya ce "Ina yi maku barka da zuwa AZURE BARRACK, Ina fatan zaku mai da hankali a kan aiki yadda yakamata?".

Dik cikinsu babu wanda ya yi magana, tamkar saƙaguna haka suka ƙame, doka ce baka isa manya suna magana ka yi magana ba tare da an baka izini ba.
Kallon Captain Commander ya yi ba tare da ya yi magana ba. Da sauri Captain ya matsa gaba tare da fara magana cikin tsantsar jarumta. "Nasan kun san dokokin GIDAN SOJA, amma zan sake tinasar daku kafin mu bada umarnin zuwa mataki na gaba". Ya É—an dakata yana kallonsu. Still ba wanda ya motsa a cikinsu.
Chapter 5 · 0% Book details