← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 227

Sashe 106

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana miƙewa a saman bed ɗin cikin zafin nama ya damki gashin kanta, janta baya ya yi tamkar zai kwantar da ita, hakan yasa ta ɗaga kai sama, sai ya sanya ɗayan hannun nasa ya damko wuyanta, ya shaƙeta da karfi tare da sake tambayarta a ina ta san waɗan nan abubuwa ba tare da ya saki wuyanta ba, yarinya na ƙoƙarin sume mashi. Ai gagara iya magana ta yi, saboda tashin hankali.

"Who told you all this?!". In a harsh way ya faÉ—a still bai saki wuyanta ba. Har yanzu ta gagara yin magana, kuma karya take yi, ba iya videon can bane kawai, da yake ya razanata ne yasa ta fahimci abin ba mai kyau bane shiyasa taki faÉ—a mashi ainahin yadda komai ya faru, yanzu ma daga labari yana neman kaita lahira ina ga kuma ya ji cewa koya mata ake yi? Ai tana ganin yau mutuwa zata yi ta bi mammy É—inta.

Ganin yadda ta razana ta gagara yin magana ne yasa ya saki wuyan nata, ransa a matuƙar ɓace ya ɗauko school bag ɗinta, zuge zip ɗin ya yi, gabaɗaya ya zazzage abin dake ciki a tsakiyar room ɗin. Ai tana ganin haka ta watsa da gudu zata yi waje, dan tasan tin da ya ɗauko jakarta shikenan ya gama ganin komai, asirinta ya tonu, kasheta kawai zai yi ta sani.

Sai da kuwa tana zuwa wajen door ta samu kofar a rufe, ta yi matuƙar mamakin ganin hakan, saboda a lokacin da ya shigo ai bata ga ya rufe kofa ba, to ta ya aka yi kofar ta rufu? Ta manta da cewa gidansa ne, kuma ta manta da cewa gabaɗaya doors na gidan automated doors ne wanda da app ɗinsu na wayarsa ma kawai zai iya rufe door ɗin ba sai ya kunna computer ba ko ya je wajen control na jikin door ɗin ba, tin da yai mata tambayar farko bata amsa ba ya rufe dikka kofofin gidan, har da kofar ɗakin Madam ya rufe dan ma kada ta ce zata zo ta shiga tsakaninsu, saboda ya sha alwashin yi mata mugun duka in har bata bashi amsa ba.

Hankalinta idan ya yi dubu yau ya tashi, hannu tasa ta toshe bakinta tana faman girgiza kai irin shikenan ta gama yawo yau. Shi kuwa wasu books guda biyar ciff ya zaro daga cikin littafanta da ya gama watsawa, gabaÉ—aya jikin covers na littafan babu kyan gani, daga lesbian book, sai sex and romance. Wanda aka rubuta how to have a nice sweet sex ya zaro daga cikin biyar É—in.

BuÉ—e cover ya yi, ai yana sauke kallonsa a kan page na farko bai san time É—in da ya É—ago ya kalleta ba. Wani irin razanannen ihu ta zunduma haÉ—e da cewa yau ta shiga uku. A ransa ya ce daga ke har Madam yau sai na lahira ya fi ku jin daÉ—i, domin kuwa ita ce malamarki ta farko a gidan nan kafin school! Shi kansa school É—in naku ba barinsa zan yi ba!.

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya furta a lokacin da ya fara karanta rubutun da yake farkon shafin, bayan wani hoto da mace and namiji suke kwance sirara akwai dogon note a wajen na bayani dallah-dallah yadda mace zata gamsar da namiji, irin jima'in da namiji ya fiso, yadda zasu yi dan su ji daÉ—i da sauransu.

Tin da yake a rayuwansa, yau yana da shekaru 33 zuwa 34 a duniya bai taɓa sanin dikka wannan karatun ba, ya dai san abin da musulunci ya koyar, amma wannan kafurin tsiraran karatu bai taɓa ji ba, shi kansa sai da kwakwalwarsa ta wani irin bugawa ya ɗan ɗauke wuta, karatun tafi karfinsa wlh, dan a tsiraranta aka yi ta.

Ya ilahi, wani irin tsumar da jikinsa take yi ne yasa ya yi jifa da takardun, cikin zafin nama ya nufeta yana faɗin ta faɗa mashi daga ina ta samu waɗan nan takardun dikka? Waye ya koya masu wanan mummunar aiki? Ta taɓa yi ko bata taɓa yi ba?".

Da gudu ta watsa ta nufi wajen curtains tana ihu tana faɗin. "Daddy please for give me, ba zan sake ba"....... Yana zuwa ya sa hannu zai damkota ta gudu ya damki curtain na view. Ai tsabar takaici fisgo curtain ɗin ya yi ya ɓaɓakosa daga jikinsa bango ya yi jifa da shi.

Da gudu ta shiga toilet tana bashi hakuri, ta rufo kofa har da sanya key, har yanzu kuka yaki zuwa mata saboda tsananin firgita. Ai yana zuwa dukan takaici É—aya ya yi wa toilet door É—in, take kofar ta ruguje. Tamkar mahaukacin zaki ya zama yau.

Ciki ya shiga, da gashin kanta ya damkota, ya jata har zuwa tsakiyar room ɗin. A fusace ya damki wayar tv na ɗakin, da karfi ya fisgo shi ya tsinka. Ja da baya ta fara yi zube a ƙasa tana girgiza mashi kai.

Ai yana zuwa yasa kafansa ɗaya ya take kafafunta dikka biyu. Baya ji baya gani ya fara zaneta tamkar wanda aka saukewa wahayin duka. Tin tana ihu da karfi har ta fara yi a hankali alamar ta jigata, tin da yake bai taɓa dukan mace ba, sai yau a kanta ya fara, basa dukar halitta mai rauni, amma yau ta kuresa ne, dole ya daketa.

Sai da ya ga ta daina motsi, wayar tvn gabaÉ—aya ya tsisstsinke a jikinta, ya farfasa mata jiki sosai har da jini, ga shi irin dukan haukar nan ya yi mata, bai san in da yake duka ba, zuciya ta É—ebesa kawai dukan yake yi, har a kirji sai da ya daketa, wuya da baya dik, hannunta da tasa ta kare fuskarta dik ya fasa mata.

Ko da ta daina motsi ba wai ya hakura bane, jefa ya yi da ragowar wayar hannunsa, ya tsugguna a gabanta, yana wani irin huci ya fara faɗin. "Faɗa mun kin taɓa aikata ɗaya daga cikin abin da kika kirga? Waye kuma ya baki littafan nan? Waye yake koya maku dikka wannan lalata? Da wani classmates ɗin naku kuke fita yawo? Ina kuma kuke zuwa?".

Sai dai ina, bata motsi, hannu yasa ya ɗan jijjigata, nan ya fahimci suma ta yi, wani irin takaici ne ya kara turnuƙe shi. Cikin zafa ya miƙe ya nufi door, wayarsa ya fitar ya buɗe kofar, yana fita ya sake rufe kofofin gidan, kai tsaye ƙasa ya sauƙo.

Motarsa ya É—auka ya nufi gidansu. Yana zuwa bai gamasa parking da kyau ba ya fito cikin zafa. Dik wanda ya gansa yau hanya yake bashi a miliyan. Elevator ya nufa kai tsaye ya nufi cikin gidansu.

Elevator na tsayawa ya fita, babu ko sallama ya faÉ—o cikin main parlo É—insu. Nan ya isko Abba, Ammie, Faryan, Hareeln sai Rimsha dake kwance jikin Abba ta tada kai da cinyansa tana danna waya. Dikkansu babu wanda bai razana da ganinsa ba, musamman Harleen da ya riga kowa É—ago ido a kansa.

Cikin hanzari Rimsha ta miƙe zata gudu sama dan in baku manta ba bata zama a in da yake. Ai wani irin damka ya yi wa gashin kanta. Yana wuci ya kwashe kafafunta ta faɗi ƙasa.

Kusan a tare su Abba dik suka miƙe, saboda sun san Aryan baya dukan mata, dik tsanar Rimsha da ya yi sai dai tsawa da kora ne yake shiga tsakaninsu ban da batun duka, ko su Faryan dake maza baya dukansu bare mace.

Tana faɗuwa ƙasa yasa kafa ya fara tattaketa. Ihu ta fara yi tana faɗin. "Uncle ka yi hakuri". Baiwar ALLAH dik da bata san laifin da ta yi ba, tana bashi hakuri.

Dik cikin parlon babu wanda ya yi gigin nufarsa bare ya dakatar da shi, sai Abba ne ya yi ta mazan cewa. "Aryan lafiyarka kuwa yau? Ko ka fara shaye-shaye ne?".

Ai ina bai kula kowa ba, kai tsaye ya nufi wajen robar wayar da ta haɗa da switch da ya yi connecting light. Ɓanɓako robar ya yi, da karfi ya fincikosa, ya sanya karfi ya zaro wayar dake ciki, ya tsinkota ya nufo Rimsha. Ai tana ganin ya nufota ta kurma ihu tare da miƙewa, ta watsa da gudu ta yi sama.

Ai da gudun gaske ya bi bayanta, room ɗinta ta shiga har da sanya key. Aikuwa yana zuwa duka ɗaya ya yi wa kofar ya rugujeta. Da gudu ta ruga zata nufi toilet, taku ɗaya ya yi ya damki gashin kanta. Janta ƙasa ya yi, ya take kafafunta yadda ya yiwa Seraphina, tsakaninsa da ALLAH ya fara zuba mata wannan wayar wutan, yadda yake dukanta ma ya ninka na Seraphina sau biyu.

Ba komai yasa ya yi hakan ba kuma face ita Rimsha ai musulma ce, me bata sani ba? Bata san lesbian haramun bane? Bugu da kari ta fi Seraphina shekaru, yakamata ace idan Seraph tana yi ta tsawatar mata ne ma ba ace tare suka san komai ba! Seraph ba musulma bace, amma idan baku manta ba na ce maku Dr Hushaima banbancinta da musulmai rashin sallanta ne kawai, so haka ita ma Seraph, ta iya addu'a, ta iya karanta wasu surorin na Alqur'ani mai girma dik da bata san ma'anarsu ba, kuma tana tsananin kaunar Annabi Muhammad, musamman da mammynta ta faÉ—a mata cewa Muhammad sunan kakanta ne, ta kara son sunan sosai, kullum tana cewa tana son ganin fiyayyen halitta, saboda mammy ta ce mata sai mutanen kirki masu daraja ne suke ganinsa.

Dan haka Rimsha ta fi Seraphina sanin komai, bai kamata ace ita ta yi wannan abin ba, musamman ita da ta samu tarbiyar uwa watau Ammie, gidan Abba ai gidan tarbiya ce, amma ace ta aikata haka, ai dole ta daku sosai.

Baya ji baya gani dukanta kawai yake yi, unexpected daga bayansa ya ji an rikesa, yau dik rashin imanin Harleen da tsanar da yake yi wa Rimsha sai da ya tausaya mata ya tinkari yayan nasa zai karɓeta, dan shi da yake namiji ma ba iya jure dukan Aryan zai yi ba, suna yara sau ɗaya ya taɓa dukansa har suma ya yi.
Chapter 106 · 0% Book details