← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 227

Sashe 35

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan haka ta yi iya bugawarta babu wanda ya iya jiyota, ga shi babu iska a ɗakin, dan ko view babu, in dai ka haura 30 mins a ɗakin to fa sai dai wani ba kai ba, su kansu da iskan Oxygen suke amfani idan suka shigo, in zasu fita su kasehsa, ita kuma bata san in da yake bama bare har ta kunna ta shaki numfashi. Zama ta yi a jikin kofar tana kuka hawaye sharɓe-sharɓe, dan karfin iskar da suka sake wa kansu bai gama tafiya ba, tana ɗan shaƙar numfashi kafin ya gama tafiya ta gane ALLAH da girma yake.

-------------------------🔥

AZURE BARRACK.

Washegari, yau takama ranar talata kenan. Yau su Arya basu da class sai practical, dan haka ba uniform za su yi using ba. Tin karfe bakwai suka shirya.

Kamar kullum kun sani dressing ɗinsu iri ɗaya ne, white mini sket suka sanya zuwa ƙasan hips wajen saman gwiwa kenan, daga sama kuma blue top ce, sun tara gashin kansu sun ɗaure kashi biyu da blue rebon, sun gyara na gaban goshin nan nasu ya yi matuƙar kyau, sai tashin kamshin product na STARS LADIES LUSH suke yi, kafafunsu sanye da gladiator sandals masu shegen kyau wanda ya ƙara masu kyau matuƙa, sun ɗaura igiyar sandals ɗin har wajen gwiwa.

Note, su Arya fa ba musulmai bane kuma ba kiristoci bane! Basu da addini, GAT bai yarda da kowani addini ba, dan haka su a haka suke rayuwansu, kome zasu yi lafiya lou ne, ku daina kallon rayuwansu kamar mu musulmai, ko cikakkun musulmai na ketare ma ya aka kare da su bare kuma waÉ—an da bama su da addinin!.

A parlo suka isko daddynsu ya kamala shirinsa tsab yana jiransu. Angelina ta sanya ƙatuwar bluetooth a kunne tana jin sauti tana ɗan kaɗa kai, while ita ma V sautin soyayya da kalamai masu shegen daɗi a waƙa take ji, amma ita karamar bluetooth ta sanya.

Breakfast suka yi cike da kaunar juna, daddy ya kama hannun V yana faɗin su je ya kaisu school. A shagwaɓe ta ce. "Daddy idan mun dawo daga school zan zo office ɗinka"....... Da sauri Arya ta amsa da. "Babu in da zaki je". Ta faɗa tana harararta. Angelina ce ta sake cewa. "Sai son yawo, babu in da zaki je".

Mamaki ne ya kama GAT ganin cewa basu taɓa hana junansu zuwa office ɗinsa ba, ai suna zuwa time to time, to meyasa yau suke hana juna?. Angelina da Arya sun san cewa V zata je ganin Leo ne, shiyasa suka yi saurin dakatar da ita ba tare da sun dalilinsu na yin hakan ba, gara ma Arya ace basa shi ne,bita Angelie kuma fa?! Ita dai Manassa ko a jikinta.

Kallon V daddy ya yi, suna nufar wajen mota ya ce. "Kin gaji da zaman gida ne?". Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e. "Okey sai kin zo". Ya faÉ—a yana shafa kanta........ A cikin zuciyarta Arya ta kuduri aniyar ba zata barta ta je ba, a cewarta ba zata barsu su yi soyayya ba dan kada su ja masu raini wajen maza!.

Suna fitowa waje wasu jiga-jigan sojoji su huɗu da gudu suka nufosu, a gaban GAT suka tsaya tare da sara mashi, sun wani kame tamkar basa numfashi. Kai kawai ya jinjina masu, cikin zafin nama suka ɓalle masu door na motor, ciki ya shiga rike da hannu V, ya ɗaurata a saman laps ɗinsa, a front seat ya zauna, su Arya suka shiga gidan baya, da alama GAT ya fi kaunar V fiye da sauran yaran nasa.

Wani katon soja madaka karti ne ya shiga driving seat. Ba tare da ɓata lokacin ba ya ja motar da gudun gaske suka nufi gate. Suna fitowa wasu comboi na motocin sojoji su uku, da wasu jip suka take masu baya, suka sanya motar GAT a tsakiya, take jiniya ta tashi tamkar zasu tafi filin yaki ne. Kai tsaye school nasu Arya suka nufa, sai hira suke yi wa daddyn nasu, watau idan da shi ne suna sakewa su yi hira sosai, idan ba da shi ba zaku ɗauka kurame ne.

Har cikin school suka kaisu, cike da kauna suka yi sallama, dik sai da suka leƙo gabar motar suka bashi sumbata kafin su wuce, tsayawa ya yi yana kallonsu har suka shiga cikin class nasu su ukun, ita kuma Manassa ta wuce nasu sashen, sannan ne ya umarci a juya kan mota. Dik wanda yake tare da GAT a boys ɗin nan nasa sun san yana tsananin kaunar ƴaƴansa tamkar ransa!.

Office ya wuce daga nan, dan yau suna da zaman meeting a kan tsaro, sati ya zagayo!.

---------------------🔥

Jiki dik tsamin training daren jiya, haka suka tashi, suka yi wanka, yau dikkansu cikin sportwears suka shirya, sun ga Leo ya sanya ne sai suma dikka suka sanya.

Vash da Zaysh ne suka fara ficewa, shi kuma Noor bed na Leo ya nufa, a kusa da shi ya zauna tare da cewa. "Good morning bro"........ Bai amsa ba sai ya miƙe zaune yana binsa da wani irin kallo mai kama da na tuhuma. Da sauri Noor ya bi jikinsa da kallo kafin ya sake kallo Leo, shi dai bai ga wani abin tuhuma a jikinsa ba.

"Bro lafiya?". Ya faÉ—a a É—an rikice, dan wlh idanun Leo rikita shi suke yi, ga su kalar sanyi zubin sleeping eyes, amma sai shegen kirita mutane....... Ganin babu alamar zai yi magana ne yasa Noor É—an turo baki kaÉ—an kafin ya ce. "Ka iya gindayar da mutum kasa ya fara zargin kansa"........ A yanzu shakuwa ce sosai ta shiga tsakaninsu a cikin wata É—aya da ta wucen nan, sun zama tamkar Æ´an uwan gaske.

"What kind of dream did you have last night?". In a cool way ya faɗa. Da sauri Noor ya sanya hannu yana rufe fuska, sai kuma murmushi ya kubce mashi. Wani irin kallo mai kama da harara Leo ya jefa mashi wanda yasa ya haɗiye murmushi, sai kuma ya ɗan shagwaɓe fuska. "Kai bro, I don't know her, but she's so pretty and cute".

Shiru Leo ya yi yana kara kare mashi kallo, yaro ya fara girma har da mafarkin mace, wai kyakkyawa ce, Noor ma ɗan duniya ne wasa-wasa. Jiya bayan sun dawo daga training na dare sai barci ya ɗauke sauran da wuri, shi kuma Leo sai da ya yi nafilfili sannan ya kwanta, bayan ya idar da sallar ne zai wuce sai ya ga Noor na mafarki, gabaɗaya sai numfashi yake yi sama-sama tamkar mai push-up ko wani abin mai wahala, har da haɗa zufa, ga bananarsa a miƙe zat. Kamar zai taɓa shi sai kuma ya ce kada ya katse mashi jin daɗi, shi ma da yake ɗan duniya ne wai kada ya katse mashi jin daɗi, shi ne ya kyalesa.

"Sai yanzu zaka ji kunyata?". Leo ya faɗa tare da yunkurawa zai sauƙo ƙasan bed ɗin, da sauri Noor ya biyo shi suka sauƙo..... "Bafa kunya na ji ba, amma bro fatan baka ga komai ba?"....... Girgiza kai Leo ya yi alamar yeah bai ga komai ba, daga nan bai sake yin magana ba.

Kashe wayansa ya yi tare da ajiye wa, sannan ya ɗauki ɗan littafinsa, ya fara ƙoƙarin shinfiɗa gadonsa. Da sauri Noor ya taya shi suka shimfiɗa, ya ajiye wayansa a ƙasan pillow sannan suka nufi waje, dan lokacin sallah ta kawo kai, har an fara tada kabbara.

Kai tsaye masallaci suka nufa, suna tafe kamar wasu kurame....... Bayan sallah sun haɗu a hall da suka saba tsayawa. A nan Captain ya zo ya samesu. Kamar kullum sai da yasa suka rera taken GIDAN SOJA kafin ya ce su nufi wajen da zasu yi weapon combat training. Ai Noor na jin haka ya matsa kusa da Leo, a ɗan shagwaɓe ya ce. "Bro ni ba zan iya rike bindigar nan in yi harbi ba, akwai wahala".

Kallo mai kama da harara Leo ya dalla mashi kafin can ƙasa ya ce. "But in the dream, you said you were strong enough to even harm a woman, right? Isn't that what you claimed yesterday?"....... Da sauri ya ce. "Kai bro mafarki ne fa ba zahiri ba, ku ma ni ban yi komai ba"........... Hannaye Leo ya zura a aljihu bai sake yi mashi magana ba, dan jiya Noor ya goge mashi hadda a mafarkin nan, wai har da sambatu.

A tsakiyar hall da zasu gabatar da weapon combat training É—in suka tsaya, koya musu amfani da bindiga da harbi cikin hanzari da tinani za'ayi. Dan Captain yasan basu gama iya sauya harsashi a kasa da minti É—aya ba, kunga kuwa in basu iya ba akwai matsala, in suna tsaka da yaki bullet ya kare waye zai sauya masu? Musamman ace abokan gaba na harbo masu harsasai! Kunga ai dole su kware sosai.

Nan aka kawo wasu ƙananan bindigu waɗan da ba kai tsaye na gaske bane, dan bullet ɗinsu ma yana cikin cover saboda tsaro. Nan Captain ya umarcesu da kowa ya ɗauki ɗai-ɗai. Bayan sun ɗauka ya kirga daga ɗaya zuwa uku ya ce kowa ya cire bullet dake cikin bindigar a second 30!

Cikin zafin nama suka fara, Noor jikinsa har kerma yake yi wajen buÉ—e magazine É—in bindigarsa, inda ake sakawa bullet É—in kenan, ya ciro bullet É—in ya ajiye a gefe, shi ne na biyun gama bayan Leo.
Chapter 35 · 0% Book details